Ƙarin miliyoyin 'yan Najeriya za su auka cikin talauci nan da 2027 - Rahoto

Asalin hoton, Reuters
Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya yi hasashen cewa za a samu ƙarin miliyoyin ƴan Najeriya da za su auka cikin talauci nan da shekarar 2027, inda bankin ya ce talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin 100.
An gabatar da rahoton ne yayin taron bazara na asusun IMF da Bankin Duniya da ake gudanarwa a birnin Washington D.C. na Amurka.
Rahoton ya bayyana cewa dogaro da Najeriya ke yi kan man fetur, da raunin tattalin arziƙi, da kuma matsalolin shugabanci ne manyan dalilan da za su haifar da ƙarin talauci a ƙasar.
"Talauci a ƙasashen da ke da albarkatu amma kuma suke fama da rauni, ciki har da manyan ƙasashe kamar Najeriya da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, ana sa ran zai ƙaru da kashi 3.6 cikin 100 tsakanin shekarar 2022 da 2027," in ji rahoton.
Duk da cewa sashen da ba na fetur ba a Najeriya ya samu ɗan bunƙasa a rubu'i na ƙarshe na shekarar 2024, Bankin Duniya ya yi gargaɗi cewa wannan ci gaban ba zai yi tasiri sosai wajen rage talauci ba saboda har yanzu ana fama da matsalolin kasafin kuɗi da gazawar hukumomi.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa yankin ƙasashen Kudu da Hamadan Sahara shi ne yankin da ke da mafi yawan talakawa a duniya, inda a nan ne kashi 80 cikin ɗari na mutane miliyan 695 da ke fama da matsanancin talauci suke zaune a shekarar 2024.
A cikin wannan yanki, ƙasashe huɗu kaɗai ciki har da Najeriya suke da rabin waɗanda ke cikin wannan matsin rayuwa, wato sama da mutum miliyan 560.
A gefe guda kuma, Kudancin Asiya na da kashi 8 cikin ɗari na talakawan duniya, Gabashin Asiya da Tekun Pasifik na da kashi 2 cikin 100, inda Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka na da kashi 5 cikin 100, yayin da Latin Amurka da yankin Caribbean kuma ke da kashi 3 cikin 100.
Bankin Duniya ya danganta ƙarin talauci a Najeriya ga faɗuwar farashin man fetur da rauni wurin tafiyar da ayyukan gwamnati.
A lokaci guda, ƙasashen Afirka da ba su da arzikin albarkatun ƙasa da yawa na samun gagarumin ci gaba a tattalin arziƙinsu da kuma saurin raguwa a talauci, sakamakon hauhawar farashin amfanin gona da kuma ingantattun manufofin kasafin kuɗi.
Domin daƙile wannan hauhawar talauci a Najeriya, Bankin Duniya ya buƙaci a gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙarfafa ci gaban tattalin arziƙi na kowa da kowa da kuma kyautata sarrafa kuɗaɗen gwamnati.
Bankin Duniya ya kuma ja hankalin gwamnati ta mayar da hankali kan tunkarar cike giɓi a kasafin kuɗi da kuma haɗa kai da ƴan ƙasa domin cimma ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa da kuma rage talauci na dogon lokaci.
Hanyoyi uku da Najeriya za ta iya kauce wa matsalar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani malami a sashen tattalin arziƙi na kwalajin Shehu Shagari da ke Sokoto, kuma mai sharhi kan tattalin arziƙi, Dr Kabiru Jabo, ya shaida wa BBC cewa wannan hasashe na Bankin Duniya zai iya tabbatuwa idan har gwamnatin Najeriya bata lura da ingantawa da kuma raba hannu zuwa ga sauran masana'antu da sauran tattalin arziƙi ba.
"Idan gwamnati ta mayar da hankalinta kan abubuwa, kamar inganta harkar noma, da inganta kiwo da inganta horar haƙo zinari da inganta sashen masana'antu da kuma samar da wutar lankarti saboda duk waɗannan abubuwan sun ƙaranta a Najeriya, tabbas za a samu chanjin da zai sauya wannan hasashe na Bankin Duniya." in ji Dr Kabiru.
Ya kuma ce idan har aka ci gaba da mayar da ƙarfi ga harka da man fetur kaɗai, toh tabbas wannan hasashe na Bankin duniya zai iya zama gaskiya
Hakazalika, wani Babban malami a sashen nazarin harkar kuɗi da bankuna na kwalejin fasaha ta jahar Kano, Lawan Habib Yahaya ya ce abubuwan da gwamnati ya kamata ta fi lura da su a wannan yanayi shi ne:
"Mayar da hankali ga masana'antu da ke amfani da kayan noma wanda za su sama wa mutane aikin yi." in ji Babban malamin.
Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta nami hanyar da za ta bi ta magance matsalar tsaro da ta saka harkar noma ta girgiza a ƙasar ta yadda za a samu manoma su koma suyi noma, mutane su samu abinci.
Bankin duniya shi ma ya shawarci gwamnatin ƙasar ta mayar da hankali kan tunkarar cike giɓi a kasafin kuɗi da kuma haɗa kai da ƴan ƙasa ta hanyar domin cimma ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa da kuma rage talauci na dogon lokaci.











