Daga Bakin Mai Ita tare da Sallau na Daɗin Kowa

Daga Bakin Mai Ita tare da Sallau na Daɗin Kowa

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya tattauna da Umar M.S. Jigirya - wanda aka fi sani Sallau Kowa Naka a fim ɗin Daɗin Kowa.

Tsohon ɗan wasan kwaikwayo ne da ya fara drama 1992 a cikin birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Ya shafe lokaci mai tsawo yana shiryawa da ba da umarni kafin daga baya ya fara fitowa a finafinai.

Ya shaida wa BBC cewa finafinan da ya ɗauki nauyi da waɗanda ya fito da waɗanda ya fito a ciki sun kai 1,000.