Akpabio da Tajuddeen sun zama shugabannin majalisa ta goma a Najeriya

An zaɓi Sanata Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai ta goma a Najeriya, da kuma Sanata Barau Jibrin a zaman mataimakinsa.

Yayin da aka zaɓi Onarabul Tajuddeen Abbas da Onarabul Benjamin Kalu, a matsayin shugaba da mataimakin shugaban majalisar wakilai.

Godswill Akpabio ya ci zaɓen ne da ƙuri'a 63 a kan abokin takararsa Sanata Abdul'aziz Yari wanda ya samu ƙuri'a 46.

Daidai lokacin da 'yan majalisar wakilai 353 suka kaɗa ƙuri'unsu ga Tajuddeen Abbas, wanda ya zama shugaban majalisar wakilai.

Ya kayar da tsohon mataimakin shugaban majalisar, Onarabul Idris Ahmed Wase da kuma Aminu Sani Jaji, inda kowannensu ya samu ƙuri'a uku.

Sanata Barau Jibrin ya ci zaɓe a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ba tare da hamayya ba. Haka shi ma Ben Kalu a majalisar wakilai.

Sabbin shugabannin majalisar ta goma su ne suka samu goyon bayan jam'iyya mai mulki ta Najeriya wato APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Akawun majalisar tarayya, Sani Tambuwal tuni ya rantsar da su, inda suka hau kan kujerun shugabanci kafin a ci gaba da rantsar da sauran zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

Zaɓen na yau ya kawo ƙarshen kai ruwa da rana da taƙaddamar da aka shafe watanni ana yi tun lokacin da jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu suka nuna goyon baya ga takarar Sanata Akpabio da Onarabul Tajuddeen.

Sun dai kafa hujja ne da cewa tun da Bola Ahmed Tinubu, shugaban ƙasar da mataimakinsa Kashim Shettima, duka Musulmai ne, ya fi dacewa a samu Kirista daga Kudancin Najeriya ya zama shugaban majalisar dattijai.

Shi ne mutum na uku mafi girman muƙami bisa tanadin doka a Najeriya.

A cewarsu matakin zai tabbatar da daidaito wajen raba muƙamai da inganta haɗin kan ƙasar mai al'ummomi da addinai mabambanta.

Sai dai masu sukar matakin sun ce abin da APC da Shugaba Tinubu suka yi tamkar katsalandan ne cikin harkokin Majalisar Tarayya wadda tsarin mulki ya ba ta 'yancin cin gashin kanta.

A shekara ta 2015, Majalisar Tarayyar ta zaɓi 'yan takaran da ba su da goyon bayan jam'iyya mai mulki da kuma shugaban ƙasar, lamarin da ya haifar da zaman doya da man ja a wasu lokutan, da kuma shure wasu buƙatun da ɓangaren zartarwa ke kai wa gabanta don neman amincewa.

Yadda zaɓen ya gudana

Ga alama, zaɓen ya fi zafi kuma an fi kai ruwa rana a Majalisar Dattijai, inda Sanata Akpabio ya yi nasara da ratar ƙuri'a 17 kacal.

Sanatocin sun kaɗa ƙuri'a ne ɗaya bayan ɗaya, kafin a ƙidaya kuma akawun Majalisar Tarayya ya tabbatar da mutumin da ya yi nasara.

A zauren Majalisar Wakilai, kusan ana iya cewa baki ya zo ɗaya a tsakanin 'yan majalisar inda ɗan takarar jam'iyya mai mulki Tajuddeen Abbas ya yi nasara da gagarumin rinjaye.

Sun kaɗa ƙuri'a ne ta hanyar miƙewa ɗaya bayan ɗaya, suna bayyana ɗan takarar da mutum yake marawa baya. Sai da aka kwashe tsawon sa'o'i kafin kammala zaɓen.

Yanzu dai abin zuba ido a gani shi ne yadda majalisun tarayyar za su tunkari aikin da ke gabansu na yin dokoki da bibiyar ayyukan hukumomi da ma'aikatun ɓangaren zartarwa.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun yi ta bayyana fatan cewa majalisa ta goma za ta kasance daban da wadda ta gabace ta.

An dai zargi majalisar a ƙarƙashin jagorancin Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila da kasancewa 'yar amshin shata da yarda da kusan duk wata buƙata daga ɓangaren zartarwa.

Gwamnatin a ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta yi ƙaurin suna wajen cin ɗumbin bashi, wanda masu suka ke cewa ya jefa Najeriya cikin ƙangin da za ta shafe tsawon shekaru ba ta fita ba. Ko da yake, gwamnatin ta yi ta kare matsayin da cewa lamari ne da ya zama dole saboda akwai buƙatar fitar da ƙasar daga rikicin karayar tattalin arziƙi har sau biyu da ta shiga sanadin annobar korona.