Mutanen da ke cin ɓeraye da ƙasusuwa da ƙasa don su rayu saboda yunwa

Fari da fatara da talauci da yaki da cutuka - akwai dai tarin abubuwa wadanda za su iya matukar kawo sauyi kan abubuwan da muke ci.

Idan abu ya yi kamari aka samu kai a matsanancin hali, mutane na iya komawa cin abubuwan da haka kawai ba za su ci ba.

Irin wadannan abubuwa da mutanen da suka samu kansu a mawuyacin hali kan ci a hali na tsananin yunwa sun hada da wasu ganyayyaki ko 'ya'yan itace, ko kasa ko beraye da sauran kwari ko kasusuwan dabbobi ko fatu da dai sauransu duk domin mutum ya rayu.

Tsananin yunwa da rashin abinci da rashin abinci mai gina jiki ko tamowa matsaloli ne da ake fama da su a sassan duniya da dama, kuma abin ya yi tsanani:

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai kusan mutum miliyan 828 da ke kwana da yunwa a kullum kuma miliyan 345 na fuskantar barazanar tsananin rashin abinci.

Kafin Ranar Abinci ta Duniya wato 16 ga watan Oktoba, BBC ta ji ta bakin wasu mutum hudu daga sassan duniya daban-daban, wadanda suka taba samun kansu a cikin yanayi na tsananin yunwa, inda ta tambaye su yadda suka rayu.

'Bera ne kawai naman da muke iya samu'

"Tun ina karama nake cin bera, kuma ban taba samun wata matsala ta rashin lafiya ba.

Da beraye na rika ciyar da 'yata 'yar shekara biyu. Mun saba da cinsu,'' in ji Rani daga kudancin Indiya.

Matar mai shekara 49 tana zaune ne a kusa da Chennai, kuma 'yar daya daga cikin kabilun da suka fi fuskantar wariya ne a kasar ta Indiya - ta bar makaranta tun daga aji biyar.

A al'adar nan ta 'yan-bora da 'yan mowa ta Indiya, al'ummarta sun yi fama da wariya da nuna bambanci tsawon shekaru.

Rani tana aiki ne da wata kungiyar agaji wadda ba ta gwamnati ba , wadda ke ceto mutane a garinsu, Irula, mutanen da suka samu kansu a aiki irin na bauta.

"Kodayaushe a wajen gari da kauye muke rayuwa. Iyayenmu da kakanninmu sun gaya mana cewa a wani lokacin ba su da komai da za a ci - ko da rogo ko dankali.

A wancan lokacin da ake cikin tsanani, bera ne yawanci abin cinmu," in ji Rani a hirarta da BBC.

"Tun ina 'yar karama na koyi kama su."

Dabarun rayuwar da Rani ta koya tun tana 'yar yarinya a yanzu suna taimaka mata kan yadda iyalanta za su ci su rayu. Suna cin bera akalla sau biyu a mako.

Mutanen garin Irula suna cin nau'in beraye da ake kamawa a daji, ba irin na gida ba.

"Muna fede bera mu gasa shi, mu ci. Wani lokaci kuma mu yayyanka naman mu dafa shi mu ci da miyar wake da tsamiya," in ji Rani.

Haka kuma mutanen Irula kan haka ramin beraye su debo gyada ko wake ko wasu nau'ukan abinci su ci.

Ta kara da cewa, "Sau daya kawai nake iya sayen naman kaza ko kifi a wata. Amma beraye kusan a kodayaushe suna nan, kuma kyauta.''

'Na sha ruwa maras kyau kuma na ga mutane na cin mushe'

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Somaliya na fuskantar mummunar yunwa, da kuma tsananin fari da kasar ba ta taba fuskanta ba a shekara 40, inda tuni har matsalar ta raba miliyoyin mutane da muhallinsu.

Sharifo Hassan Ali mai shekara arba'in wadda take da 'ya'ya bakwai tana daga cikin mutanen da farin ya raba da muhallansu.

A dole ta bar kauyunsu inda ta yi tafiyar sama da kilomita 200, kusan da kafa, zuwa wani sansani na wucin-gadi a wajen babban birnin kasar, Mogadishu. Ta yi wannan tafiya ne tsawon kwana biyar.

Ta ce, ''a yayin wannan tafiya sau daya muke cin abinci a rana. Idan ma ba mu da abinci sosai sai mu ba yaran, mu mu hakura da yunwa." A kan hanyarsu ta zuwa babban birnin ta ga wasu abubuwa da suka tayar mata da hankali.

"Ruwan kogi ya kafe gaba daya. Tsawon shekaru ruwa kadan ne a kogin, saboda haka ba mu da wani zabi illa mu sha burkutaccen ruwa,'' in ji ta.

" Na ga daruruwan matattun dabbobi a kan hanyata zuwa Mogadishu. Mutane har mushen dabbobin suke ci da kirginsu."

Sharifo tana da shanu 25 da awakai 25 a da. Amma yanzu duka sun mutu a wannan fari.

"Ba ruwan sama kuma ba abin da ke gonata," ta ce.

A yanzu tana samun kasa da dala biyu a rana a aikin da take yi na wankin kayan mutane, sai dai wannan kudin bai ishe su cin abinci ba.

"Da kyar kudin za su saya mana 'yar jakar shinkafa mai nauyin kilogram daya, da kayan cefane, kuma ba zai ishi kowa ba. Wannan farin ya yi mana illa sosai."

Tana samun dan tallafi daga kungiyoyin agaji amma ta ce ba ya isarsu. Ta kara da cewa, "Ba mu da komai."

'Mun dogara ne a kan fata da kasusuwa'

Tsawon shekara biyu da ta gabata, Lindinalva Maria da Silva Nascimento, wata kaka mai shekara 63, wadda ma'aikaciya ce da ta yi ritaya, daga birnin Sao Paulo, ta ce suna rayuwa ne ta hanyar cin kashi da ganda ko kirgin da mahauta suka zubar.

'Yar fanshon tana kasafin dala 4 ne a kullum ta ciyar da kanta da mijinta da dansu daya da kuma jikoki biyu. Ba za ta iya sayen nama ba.

Saboda haka ne take zuwa wajen mahauta daban-daban ta sayi kazi da suka mutu da ganda ko kirgi.

Ko da wannan din ma tana saya ne a kusan dala 0.70 ( santi 70) kan duk kilo daya.

Ta ce, "Ina dafa 'yan kasusuwan da nake saya ne masu dan nama-nama a jikinsu. Sai na hada da wake domin a samu dandano."

Ta ce tana soya fatar kajin ne ba tare da mai ba , saboda haka duk wannan man da take samu ta haka sai ta tattara shi ta adana, idan ta tashi yin girki sai ta yi amfani da shi.

"Ba na ma tunanin sayen kayan marmari ko kayan lambu ko wani kayan zaki. A da firjina cike yake da nama da kayan lambu da tumatur da kabeji da albasa, komai na nan jibge,'' ta ce.

"Amma a yau ba komai a ciki, wannan albasar daya kawai nake da." Lindinalva ta rasa aikinta a lokacin annobar korona kuma danta ma ba shi da aiki.

"Na dogara ne ga taimakon abincin da nake samu daga mutanen da na sani da kuma tallafin da ake bayarwa a Cocin Katolika ta wurinmu. Yadda nake rayuwa ke nan," ta ce.

Sama da mutum miliyan 33 na fama da yunwa yanzu a Brazilin kamar yadda wani rahoto na baya-bayan nan na wata kungiya ( Brazilian Network for Food Security ) mai fafutukar tabbatar da wadatar abinci a kasar ta fitaRahoton wanda aka fitar a watan Yuni ya kuma gano cewa sama da rabin yawan mutanen na fama da rashin wadatar abinci.

"Yawanci mahauta na cewa ba su da kashi," in ji Lindinalva.

Ta ce dole ne ta takaita abin da take ci domin ta adana wanda za ta yi amfani da shi don gaba.

"Na kuma dogara ne da imanin da na yi cewa al'amura za su gyaru nan gaba."

'Ni da 'ya'yana muna rayuwa ne a kan wani dan itace da ke sa zawayi'

"Ba ruwan sama saboda haka ba amfanin gona. Ba mu da wani abu da za mu sayar. Ba mu da wani kudi. Ba zan iya cin shinkafa ba."

Abin da Fefiniaina wata uwa mai shekara 25, da 'ya'ya biyu wadda take a kasar Madagascar ta ce ke nan.

Rashin wadataccen ruwan sama na tsawon shekara biyu ya lalata amfanin gona ya kuma ramar da dabbobi.

Wannan na tura sama da mutum miliyan daya ga tsananin yunwa a in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Fefiniaina tana zaune ne a garin Amboasary, daya daga cikin garuruwan da rashin ruwan sama ya fi yi wa illa.

Ita da mijinta suna sana'ar sayar da ruwa ne.

"Idan na samu kudi, ina sayen shinkafa ko rogo. Idan kuma ba ni da komai sai dai mu ci irin 'ya'yan itacen nan da galibi ba a cinsu ko kuma mu kwana haka ba mu ci komai ba,'' kamar yadda ta gaya wa BBC ta hanyar wani tafinta na kungiyar Unicef.

"Yawancin mutanen da ke nan suna cin wannan dan itace ne, wanda kusan dandanonsa kamar na tsamiya ne."

"Tun wata hudu da ya gabata muke cin wannan dan itace, yanzu duka 'ya'yana biyu gudawa suke."

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta bayar da rahoto a bara cewa a kudancin Madagascar, ''Mutane na cin farar kasa, wato laka da ruwan tsamiya da wasu ganyayyaki da saiwoyi don su rayu kawai.''

'Ya'yan itacen za su kare iyalan Fefiniaina, su rayu to amma ba za su ba su abubuwan gina jikin da suke bukata ba.

Danta mai shekara hudu na daga cikin da dama da ake yi wa maganin tamowa.

"Idan muka samu ruwan sama ko da kadan ne z mu iya samun dan amfanin gona. Za mu iya cin dankali da rogo da 'ya'yan itace,'' in ji Fefiniaina.

"Ba sai mun rinka cin wancan dan itacen ba."

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce duniya ba ta taba shiga yunwa ba kamar yanzu.

Ta dora alhakin, "wannan gagarumar matsalar yunwa" a kan abubuwa hudu: rikici da sauyin yanayi da illar annobar korona ga tattalin arziki da kuma tashin farashin abubuwa.

Rahoton hukumar na 2022 ya nuna cewa kudin da take kashewa wajen tafiyar da harkokinta yanzu ya kai dala miliyan 73.6 a wata sama da na shekara 2019. Hakan na nufin ya karu da kashi 44 cikin dari.

Idan da a baya ne da za a kashe wannan karin kudin gudanarwar ne ta hanyar ciyar da mutane miliyan hudu a wata.

To amma kuma hukumar ta ce kudi kawai ba zai kawo karshen wannan matsala ba: sai dai idan akwai kuduri daga shugabanni na kawo karshen rikice-rikice, da kuma kudurin shawo kan matsalar dumamar yanayi.

Rahoton ya ce idan ba haka ba to abubuwan da ke kara ta'azzara wannan matsala ta yunwa za su ci gaba.