Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jijjiga: Cutar da ta daɗe tana yi wa mata kisan mummuƙe
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
"Har yanzu matata tana fama da shanyewar hannu da rashin magana," wannan ne abin da wani mai suna Murtala Said Sulaiman ya bayyana wa BBC a lokacin da yake bayyana halin da matarsa take ciki tun bayan fama da cutar jijjiga da ta yi.
Wannan labari ne na wata mata mai suna Ummukulsum mazauniyar unguwar Durumin Iya a jihar Kano wadda ta haifa ƴaƴa biyar, amma ta tsinci kanta a lalurar jijjiga a haihuwarta ta ƙarshe, kuma har yanzu bayan kusan shekara bakwai take cigaba da fama.
Wannan labari ne da ke bakin mutane da dama, kasancewar jijjiga ta daɗe tana ci wa mutane, musamman mata tuwo a ƙwarya, musamman a garuruwan masu ƙaramin ƙarfi.
Cutar jijjiga lalura ce da mata ke fuskanta a lokacin haihuwa, inda suke jijjiga da yunƙurin tauna harshe da sauran alamomi.
A wani rahoto da ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta fitar a watan Oktoban shekarar 2024 game da hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar mai suna, "National Guidelines for the Management of Pre-Eclampsia/Eclampsia in Nigeria," ta ce mutuwa lokacin haihuwa na cikin manyan matsalolin da ɓangaren kiwon lafiya ke fuskanta a ƙasar.
Rahoton ya ƙara da cewa cutar na cikin abubuwa biyar da suke jawo mutuwar mata wajen haihuwa,
Rahoton ya ce cutar ce ke sanadiyar kashi 17 cikin 100 na mutuwar mata wajen haihuwa, inda rahoton ya ce za a iya kiyaye aukuwar mutuwar ta hanyar amfani da ƙa'idojin da suka dace.
'Yadda na faɗa cikin jijjiga'
A Unguwar Durumin Iya da ke ƙwaryar Kano, Ummkulsum Ibrahim da ka ganta, za ka sha ƙalau take, sai ka yi mata magana ne za ka gane sai a hankali domin har yanzu tana fama da jinya a sanadiyar samun kanta da ta yi a yanayi na jijjiga a lokacin wata haihuwa da ta yi kimanin shekara takwas da suka gabata.
Mijinta Malam Murtala ya shaida wa BBC cewa duk da cewa ya san lalurar jijjiga, na matarsa ta zo da wani irin salo.
"Watarana na dawo gida, sai ta ce min tana son abu mai ɗan yaji. Sai aka kawo mata. Bayan na fita na dawo sai na tarar da ita a kwance a cikin wani hali. Sai muka lallaɓa a hankali muka tafi da ita asibiti. Ko da muka ƙarasa asibiti ba ta san inda take ba. Sai numfashi take yi sama-sama."
Ya ce a haka ta yi kusan kwana biyu tana naƙudar, har ta shiga jijjiga, "amma yanayin jijjigar da ta yi, sai ya zama hannunta ya ɗan shanye, sannan tana zubar da miyau ta bakinta, kuma ba ta iya magana, sai aka ce mana ya shafi ƙwaƙwalwarta, har aka tura mu asibitin ƙwaƙwalwa na Dawanau."
Murtala, wanda ya kasance yana taya matarsa aikace-aikacen gida, tare da taimakon ƴanuwanta, ya ce yanzu yaransa sun fara girma, inda suka fara taya ta aikace-aikace.
"Ita ma ta fara samun sauƙi, tana iya yin wasu aikace-aikacen. Amma dai har yanzu ba ta warware ba, domin wani lokacin ko ta yi niyyar yin magana, sa ta kasa. Wasu lokutan sai dai ta rubuta abin da take so. Amma har yanzu hannun da bakin ba su saki ba, amma tana jin komai," in ji shi.
Ya ce yanzu sun bar wa Allah komai, "muna addu'a, sannan idan ta ɗan ji wani yanayi, sai mu leƙa asibiti. Yanzu kusan shekara takwas ke nan muna fama," in ji shi, wanda ya ƙara da cewa sun haifa yara biyar, amma yanzu uku ke raye.
A game da zuwa awon ciki, wanda masana suka ce shi ne babban musabbain jawo cutar, Murtala ya ce tana zuwa awo sosai, "kasancewar da ta ɗauki cikin, ta yi fama da laulayi sosai. Domin takan yi amai sosai. Don haka muna zuwa asibiti sosai," in ji shi, inda ya ƙara da cewa sun yi amannar cewa lalura ce, ba aljanu ba.
A jihar Kaduna, wata mai suna Zainab ma'aikaciyar jinya ce, wanda hakan ya nuna sanin muhimmancin awo da ta yi, ta bayyana cewa ta taɓa tsintar kanta a mafarin cutar da ake kira pre-eclampsia, amma likitoci cikin ikon Allah likitoci suka samun nasarar daƙile faɗawarta.
A cewarta, "A lokacin bayan na shiga naƙuda, dukkan abubuwan da ya kamata a duba irin protein harbawar jini wato BP suna daidai, amma ranar da zan haihu, har mahaifa ta buɗe ta kai sentimita 3, sai BP ɗina ya hau zuwa 180, sai aka gwada min fitsari da sauri, shi ma aka ga protein ga ƙafafuna suna kumbura."
Ta ce nan da nan ta fara fita hayyacinta, "Sai aka min allurar hana jijjigar, sannan aka min ƙarin ruwa, aka kuma saka min robar fitsari. Haka aka ci gaba da lura da ni har na haihu."
Abin da ke jawo cutar
Cutar ta jijjiga tana da alamun da mai haihuwa za ta fara nunawa, wanda ake kira pre-eclampsia, kamar hauhawar bugawar jini, kafin mace ta fara jijjigar.
A duniya, aƙalla mata 700,000 ne suka rasuwa a sakamakon jijjiga a shekara, kuma sama da abin da ke cikin ko kuma jarirai 500,000 suke mutuwa, wanda yake daidai da rasa aƙalla rasuwa 1600 a kullum, kamar yadda rahoton ma'aikatar lafiya ya nuna.
Domin jin abin da ke jawo jijjigar, BBC ta tuntuɓi Dokta Jamila Mu'utassim Ibrahim, wadda likitar mata ce a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Bayero da ke Kano ta ce cuta ce da mafi yawancin bincike ya nuna ba a san me yake kawo ta ba, "amma akwai abubuwan da suke da dangantaka da ita kamar hawan jini da masu ciki, sanna akwai mabiyiya, wato abin da ake kira uwa da take fitowa bayan an haifi yaro. Ana tunanin matsalar da ke jawo cutar tana tattare da ita mabiyiyar."
Sai dai duk da yadda cutar ke cin mata, har yanzu ba a gano takaimaimen abin da ke jawo ta ba. "Kamar cutar maleriya an san cizon sauro ke jawo ta, amma ita wannan cutar akwai dai abubuwan da ake lura da su, idan kana da su, akwai yiwuwar za ka tsinci kanka a wannan cutar, amma takaimame abin da ke jawo ta, ba a sani ba," in ji Dokta Jamila.
Dr Jamila ta lissafa wasu abubuwa da ta ce masu su suna cikin hatsarin kamuwa da cutar a lokacin haihuwa:
- Mata masu ƙananan shekaru da suka samu cikin farko da waɗanda shekarunsu suka ja, suna cikin waɗanda suke cikin haɗarin kamuwa. Ƙasa da shekara 18 da sama da shekara 35.
- Masu hawan jini. Hawan jini na cikin manyan abubuwan da ke alamta samuwar jijjiga.
- Masu ɗauke da cutar sukari.
- Da ɗauke da cikin ƴan biyu ko ƴan uku ko sama da haka.
- Wadda mahaifiyarta ko ƴan uwanta ko ta taɓa yin cutar a baya.
- Cututtukan da garkuwar jikin mutum ke faɗa da garkuwar jikinsa.
Me ya kamata a yi domin kariya?
A game da hanyoyin da ya kamata a bi domin kare faɗawa cikin wannan yanayi na tsinkau-tsinkau, Dokta Jamila ta ce zuwa asibiti da sauri na da matuƙar muhimmanci.
A cewarsa, "Abu na farko shi ne cutar tana bayar da alama. Hawan jini na ckin manyan alamu. Don haka da mace ta samu ciki yana da kyau ta fara zuwa awo. Zuwa awon ne zai sa a riƙa auna yanayin jinin, da an ga jinin ya fara hawa sai a san me za a yi domin a daƙile cutar cikin sauri."
Sai dai ta ja hankalin mutane cewa ba cutar aljanu ba ce, inda ta ce, "ya kamata a nema ilimi, wannan cuta ce kuma ana warkewa. Tana kama masu juna biyu ne, kuma ana warkewa, kuma idan aka gane da wuri, za a iya kare faɗawa."