Ko ƙasashe masu tasowa na iya daina dogaro kan bankunan duniya?

Hoton Hedikwatar asusunbayar da lamuni na duniya

Asalin hoton, Barry Winiker/Getty Images

Bayanan hoto, Hedikwatar asusunbayar da lamuni na duniya a birnin Washington, DC na Amurka
    • Marubuci, Mamadou Faye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar
  • Lokacin karatu: Minti 5

Fiye da shakaru, 70 asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) da bankin duniya sun yi kakagida a harkar tsara yadda tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa ke kasancewa. Manyan hukumomin biyu, an kafa su ne domin samar da daidaito ga arzikin duniya, kuma sun zamo masu tsara gyare-gyare da kawo sauyi da kuma bayar da bashi ga ƙasashen duniya a lokacin rikici

Amma ta la'akari da guguwar fafutukar neman ƴancin ƙasashe a harkar gudanar da tsare-tsarensu ba tare da katsalandan ba, ko ƙasashen nahiyar Afirika za su iya rayuwa ba tare da dogaro ga asusun bayar da lamuni na duniya kuwa?

A yanzu haka, bashin da China ke bai wa ƙasashe ya zarce wanda bankin duniya ke bayar wa, kuma ƙungiyar BRICKS ta kafa nata bankin na ci gaban ƙasashen ƙungiyar.

Samar da waɗannan zaɓi da a baya babu su, ya ƙara ruruta wutar neman ɓallewa da gudanar da tsare-tsaren tattalin arzikin su ba tare da alaƙa da manyan bakunan duniya ba.

A Afirika, ƙasashe da dama da suka haɗa da Ethiopia da Kenya, da sauran su sun karkata ga China domin neman bashin kuɗaɗen gina kayan more rayuwa irin su layin dogo da filayen wasa da dai sauran su.

A nahiyar Asia, Sri Lanka da Pakistan na tsakiyar zaɓi a tsakanin Beijing da Washington.

A Latin America kuma, Argentina da Ecuador na neman ɓallewa daga shirye-shiryen tsuke bakin aljihu, yayin da suke ci gaba da tatauwa yarjejeniyar da ke ƙasa.

Amma tunda su ma zaɓin da suke dubawar suna da irin nasu ƙa'idojin da ƙasashen ke damuwa a kai, har yanzu IMF ya fi zama wajen da ƙasashen suka dogara domin cin bashi.

Lokacin da Ghana da Pakistan da kuma Argentina suka faɗa matsalar tattalin arziki, babu wata hukuma ko banki da suka ba su tallafi domin agaza masu. Shi kuma bankin duniya ya ci gaba da zama mai matuƙar muhimmanci wajen samar da manyan abubuwan buƙatun rayuwa da suka haɗa da tituna da ruwa da makamashi da sauran ayyuka masu muhimmanci da ɓangaren ƴan kasuwa masu zaman kansu suka gaza talafawa.

Mene ne amfanin cibiyoyin kuɗi na duniya?

Asusun bayar da lamunai na duniya a birnin Washington, D.C.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Kamata ya yi gudunmuwar bankuna irin su IMF da bankin duniya ke ga ƙasashen duniya ta karkata kan samar da hanyoyin da za su iya biyan bashin da ke kansu cikin kwanciyar hankali,'' in ji Dr. Seydou Bocoum, wani masanin tattalin arziki na ƙasar Senegal.

Dr. Bocoum ya ƙara da cewa "Kuma su ne suke tsara hanyoyi da dabarun yadda ƙasashen za su bi domin kaiwa ga nasarar biyan bashin nasu, ta hanyar tantance tashin darajar kudi ko faɗuwar ta.

Taron Bretton Woods Conference, na 1944 ne ya kafa IMF da bankin duniya a matsayin kinshiƙin tsarin tattalin arzikin duniya. Ana yawan ambato su a tare, amma manufofinsu daban, duk da dai suna tallafawa juna.

Aikin IMF shi ne samar da daidaito a tsakanin kuɗaɗen ƙasashen duniya, ta hanyar tantance darajar kuɗaɗen da ƙayyade tashi da saukar farashi da kuma matsayin canjin kudi. Ya na kuma tallafawa ƙasashen da ke cikin matsin tattalin arziki da bashi da kuma shawara kan hanyoyin inganta tattalin arzkin.

Shi kuma bankin duniya ya karkata ga gudanar da ayyukan ci gaba masu dogon zango. Yana bayar da tallafin gina hanyoyi da samar da makamashi da ruwa da makarantu da bunkasa noma da gina asibitoci da yaƙi da talauci da kuma samar da bashi mai nisan zangon lokacin biya.

Ko ƙasashe masu tasowa za su iya daina dogaro kan IMF?

Abebe Selassie, Darakta mai kula da Afirika a asusun bayar da lamuni na duniya (IMF)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abebe Selassie, Darakta mai kula da Afirika a asusun bayar da lamuni na duniya (IMF)

Ana iya cewa hakan za ta yiwu, idan muka yi amfani da matsayar Dr Seydou Bocoum.

"Tabbas, ƙasashe masu tasowa na iya gudanarda harkokin su ba tare da dogaro da IMF ba. Botswana ba ta da wani shiri da take yi tare da IMF. Don haka ba wai ƙasashen suna buƙatar IMF bane, yana dai talafawa waɗanda ke cikin ƙangin tattalin arziki. Saboda haka, babu shakka kowacce ƙasa na son tallafin IMF amma fa ba lallai bane mu dogara kan shi wajen neman mafita,'' in ji Dr. Seydou Bocoum.

Yayin da wasu ƙasashen Afirika ke cikin matsin tattalin arziki kuma ake samun irin su Ghana da Zambia da kuma Ethiopia, masu dogaro kan IMF, akwai wasu irin su Angola da DRC da kuma Kenya da ke tafiyar da harkokin su lafiya lau, inda suke samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da bashin da suka ciwo daga China.

Da aka tunatar da shi cewa akwai kasa irin Najeriya mai ƙarfin arzikin mai, wadda idan aka haɗa ta da Senegal wadda bata da irin wannan arziki, Dr. Bocoum ya jaddada cewa yarjejeniyar WAEMU za ta iya taimakawa ƙasashen cikinta wajen magance matsalolin su.

Wane zaɓi ƙasashen ke da shi?

Ƴan ƙasar Senegal

Asalin hoton, Getty Images

"Ina ganin kamar irin goyon bayan da ake samu daga jama'a ne. Idan ka samu goyon bayan ƴan ƙasa, kuma daga baya ka juya masu baya, to ya zama wajibi ka samar wa kanka wasu dabaru na daban da za ka maye gurbin wancan goyon baya da a baya kake samu daga mutanen,'' in ji Jean-Claude Kouadio, wani masanin tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa ''kamar misali ne da ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), waɗanda suka zaɓi raba gari da ƙaashen duniya, da kuma nuna cewa ba su buƙatar tallafin su.

"Amma zahirin zance shi ne ƙasashen nan suna buƙatar sauran ƙasashen duniya domin gudanar da rayuwar su. Abu ne mai wahalar gaske a samu ƙasar da bata buƙatar goyon baya da tallafin wasu ƙasashe da ke tare da ita. Amma a yanzu zaɓin da suke da shi, shi ne neman hanyoyin ƙulla sabbin ƙawance da alaƙa ta taimakon juna domin janyo ci gaba a cikin ƙasashen su.'' In ji Mr. Kouadio.

Sai dai kuma, Dr. Seydou Bocoum na ganin cewa akwai wata hanyar ta daban, wadda ta mayar da hankali ga samun yanayin yalwatar tattalin arziki.

Ya ce abu mafi muhimmanci shi ne "ƙasashe masu tasowa su daina amfani da tsarin IMF, wanda ake kira Washington Consensus, wanda ya ce ƙwararu sun gano cewa ba zai yi aiki a kan ƙasashen ba.''