Jam'iyyar da ta shafe shekara 40 kan mulki a Angola na fuskantar babban kalubale a zabe

Asalin hoton, Reuters
Ana tunanin zaɓen Angola na ranar Laraba zai kasance mafi zafi tun bayan da ƙasar ta samu ƴancin kanta a 1975.
Kasancewar Jam'iyyar MPLA ce ke mulki fiye da shekara 40, zai yi wuya ta bari shugabanci ya suɓuce mata. Amma Jam'iyyar tana fuskantar ƙalubale sakamakon ƙaruwar talauci da rashin aikin yi.
Duk da cewa Angola ƙasa ce mai arzikin mai da albarkatun ƙasa, da yawan ƴan ƙasar ba su amfana da arzikinta ba. Yayin da aka kwashe shekara 20 ana zaman lafiya bayan yaƙin da aka daɗe ana yi, jam'iyyar ba ta haifar da wani ci gaba da al'umma ke fata ba.
Jam'iyyu takwas ne ke fafatawa a zaɓen amma babbar Jam'iyyar hamayya Unita ta taɓa kasancewa ta ƴan tawaye. Tana neman yin amfani da gazawar Jam'iyya mai mulki domin samun nasara yayin da kusan masu zaɓe miliyan 15 ke shirin zaben shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki na tsawon shekara biyar.
Akasarin masu ƙalubalantar MPLA na iya karya lagon ƴan hamayya amma a wannan karon Unita ta kafa wata haɗaka da ƙunyoyi masu zaman kansu da masu fafutuka domin faɗaɗa damarta ta lashe zaɓe.
Masu zaɓe za su kaɗa ƙuri'a a akwati guda kuma shugaban jam'iyyar da ya fi yawan ƙuri'a ne zai zama shugaban ƙasa. Luanda, babban birnin ƙasar ya kasance cike da batutuwan farfaganda.
An kafa manyan alluna ɗauke da hotunan ƴan takarar shugaban ƙasa a ko ina cikin birnin inda a lokutan yaƙin zaɓe, kiɗa ke tashi duk a ƙoƙarin janyo hankalin masu kada kuri'a.
Launin ja da baƙi da ruwan tarwaɗa da ke jikin tutar MPLA ya mamaye takenta na "ƙwarin gwiwar al'umma'. Launin tutar Unita - Ja da kore su ma ana iya ganinsu a wasu sassan birnin inda wasu hotuna ke ɗauke da taken "Lokaci ya yi'.
Jiga-jigan ƴan takarar shugaban ƙasar sun haɗa da Jagoran MPLA, João Lourenço - mai shekara 68 da ke neman yin ta-zarce a karo na biyu da Adalberto Costa Júnior - mai shekara 60 da yake neman mulki a karon farko.
A babban birnin ƙasar, an jibge ƴan sanda da sojoji - matakin da ke ƙara nuna fafatawar za ta yi zafi gabanin zaɓen mai cike da tarihi.

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu masu nazari na cewa mutane sun fara hangen ganin wata jam'iyyar a kan karaga. Masaniyar tattalin arziki, Âurea Mouzinho ta shaida wa BBC cewa ra'ayin mutane shi ne ƙasar a shirye take na ganin abubuwa sun sauya,"
"Mutane sun rage fargaba, suna son sauyi. "Lokacin ƙarshe da al'amura suka kasance irin haka shi ne 1992 lokacin da shugaban ƙasa na wancan lokacin, José Eduardo Dos Santos, ya fafata da jagoran Unita, Jonas Savimbi.
Taƙaddama kan sakamakon zaɓen ta jefa ƙasar cikin yaƙin basasa. Amma an samu banbanci da yanzu. "Shekara 30 bayan nan, muna iya cewa akwai mutanen da suka fi ƙarfi a tsarin zaɓen da yin nazari da kuma sukar matakan da suke ganin ba daidai bane." in ji Cesaltina Abreu, wata mai nazari a Jami'ar Katolika ta Angola.
Amma MPLA na ci gaba da samun yaƙinin cewa za ta yi nasara. "Muna da tabbacin samun nasara. Muna aikin janyo hankalin mutane, muna tattaunawa da su kuma muna nazarin abin da suke faɗa," kamar yadda Arsénio Satyohamba, wani shugaban matasa na MPLA youth leader da ke neman takarar ɗan majalisa ya faɗa wa BBC.
Duk da samun mulki a 2017 da alƙawarin yaƙi da cin hanci a Jam'iyyar da gwamnati da kuma samar da ayyukan yi ga matasa 500,000, zangon farko na Mr Lourenço ya kasance cikin ƙalubale abin da ya rage masa farin jini. "
"A 2017, João Lourenço ya kawo wani ɓangare na MPLA, duk da Angola na fuskantar taɓarɓarewar tattalin arziki saboda dalilai da dama. Ya bijiro da wasu shirye-shirye na daidaita tattalin arziki kuma a yanzu muna ganin haka na faruwa," in ji Mista Satyohamba.
Ya ƙara da cewa "Baya ga cutar korona da wasu tarin ƙalubale, Shugaba Lourenço ya samu damar inganta tattalin arzikin ƙasarmu,".

Asalin hoton, EPA
Sai dai matsanancin yanayin da mutane ke fuskanta har da ƙaruwar yunwa da talauci, bai sa kowa yana fatan alkhairi ba.
Rashin aikin yi a Angola ya kai kusan kashi 30 cikin 100 amma a tsakanin matasa, matakin ya kai kashi 60 cikin 100, kamar yadda ƙididdiga daga hukuma ta bayyana.
"Abin da muka gani tun 2017 na nuna taɓarɓarewar halin da mutane ke ciki," in ji masaniyar tattalin arziki, Ms Mouzinho. "Mun ga tattalin arziki da ke ci gaba da muni. "Rashin ayyukan more rayuwa kamar ruwan sha da wuta da ilimi da rashin kiwon lafiya na zama a bin damuwa ga akasarin matasa a birane da ƙauyuka. Sannan su ne suka fi rinjaye.
Wata mai goyon bayan Unita, Ana de Sousa, mai shekara 22, na ganin akwai buƙatar a samu canji a ƙasar. "Ba mu da ayyukan yi, muna ƙoƙarin neman gurbi a gwamnati amma ba ma samun dama," kamar yadda ta shaida wa BBC. "Muna da yara da dama da ke buƙatar ilimi da lafiya."

Asalin hoton, Getty Images
Wani ɗalibi ɗan shekara 24 da ke karanta tarihi, Lígio Katukuluka yana son ya ga ana mutunta ra'ayoyin matasa. "Akwai buƙatar matasa, da sune suka fi yawa a Afirka, su zama masu riƙo da ra'ayoyinsu," a cewarsa.
"Ina ganin an ware al'ada da ilimi. Ina son ƙarin hannun jari domin ƙara haɓaka al'adun Afirka. "Ƙasarmu ta shafe shekara 20 cikin kwanciyar hankali amma har yanzu matsalolin da ake da su na ci gaba da ƙaruwa, in ji ɗan kasuwa Cláudio Silva, mai shkeara 34
"Unita na samun karɓuwa a wajen matasa saboda suna bayyana hanyoyin magance matsalolin ƙasar, suna ba da sabbin dabarun kawo sauyi kan abin da aka saba gani tun lokacin da aka samu ƴancin kai. "Duk da yaƙinin cewa zaɓen zai kasance kan-kan-kan, ana fargabar za a tafka magudi wani abu da ke ƙara ɗaga hankalin jama'a.
Wata ƙungiya mai suna "Ku kasa, ku tsare" ta jiyo ra'ayoyin wasu. Tana ƙarfafa wa mutanen da suka yi zaɓe gwiwar su tsaya a rumfar zaɓe har sai sun kare ƙuri'unsu. "Hukumomi sun ce mutane su koma gida da zarar sun kaɗa ƙuri'a.











