Darussan da Japan ta koya daga girgizar ƙasa

Mummunar girgizar kasar da aka yi a ranar farko ta shekarar 2024

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, Gagarumar girgizar ƙasar da aka yi ranar farko ta shekarar 2024, ta ruguza gidaje a tsakiyar Japan
    • Marubuci, Daga Rupert Wingfield-Hayes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Tsohon wakilin BBC a Tokyo

Kusan shekara 13 ke nan da samun mummunar girgizar ƙasa da bala'in tsunami waɗanda suka janyo hatsari a tashar nukiliya ta Fukushima.

Lamari ne wanda mutanen Japan ba za su taɓa manta shi ba.

Kuma a ranar Litinin sai abubuwan da suka faru a wancan lokaci, suka dawo sabbi, yayin da ƙasa ta fara girgiza aka kuma fara jin sautin ƙararrawar da ke ankarar da mutane game da zuwan girgizar ƙasa a Ishikawa.

Sai dai ankararwar ba sabon abu ba ne a Japan.

Lokacin da na koma ƙasar, da zarar na ji ginin da nake ciki ya ɗan fara rawa, sai na yi wuf na fita.

Amma bayan watanni, sai ya kasance ina barcina duk da cewa an samun motsin ƙasa.

A Japan, girgizar ƙasa wata aba ce da mutane suka saba rayuwa a cikinta.

Za ka dinga fargabar ko yaushe mafi muni za ta auku? Shin ginin da nake ciki na da ƙwari sosai?

Ga al'ummar wannan zamani duk wannan fargaba ta bayyana ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2011.

Cikin minti biyu ƙasa ta yi girgizar da ba a taɓa jin irinta ba, a iya tunanin mutum. Ta kuma ci gaba da girgizar a kai- a kai.

Duk wanda ya shaida hakan zai iya tuna a wurin da yake lokacin da girgizar ta auku da kuma irin firgicin da ya shiga.

Amma ashe mafi munin tana tafe.

Can bayan minti 40, sai tsunamin farko ta fara isa kan tudu daga cikin teku, ta ruguza katangar da aka gina a bakin tekun don bayar da kariya.

Ta mamaye garuruwa da ƙauyuka masu nisan ɗaruruwan kilomitoci daga bakin tekun arewa maso gabashin Japan.

Duk wannan, an nuna shi kai tsaye ta gidan talbijin daga kyamarar helikwafta da ke shawagi a saman birnin Sendai.

Mummunar girgizar kasa ta shekarar 2011

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mummunar girgizar ƙasar da aka samu a gabashin Japan cikin shekara ta 2011 ta lalata ɓangarori masu yawa na zirin ƙasar

Washe gari abin ya fi muni, inda aka samu hatsari a tashar nukiliya. Abin da ya fara janyo malalar sinadarai daga tashar Fukushima.

Lamarin da ya sa aka umarci dubban ɗaruruwan mutane su fice daga gidajensu, kuma hatta babban birnin ƙasar wato Tokyo bai tsira ba.

Wannan rana ta zo da mummunan tashin hankalin da ba zai misaltu ba ga kowa.

Na je ina neman wurin da zan koma a Tokyo, matata ta duba taswira don gano wurin da ke da dutse mafi ƙarfi, wanda kuma ke da nisa daga kowane irin rafi.

Sannan ta damu matuƙa kan lokacin da aka yi ginin: "Muna neman ginin da daɗewarsa bai gaza 1981 ba."

Muna shiga gidan da muka samu wanda aka gina a 1985, sai muka fara tara abinci da ruwan sha.

Muka tara abubuwan da ba za su lalace ba a tsawon shekara biyar masu zuwa, a karkashin wurin wanke hannu da ke bandaki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da an sake shiga irin fargaba da tashin hankalin da aka samu a shekarar 2011, a ranar Litinin.

Sai dai girgizar ƙasar baya-bayan nan na nuni da irin nasarar da Japan ta samu.

Ƙasar ba ta bayyana girgizar ƙasa da tsananin girmanta ba.

Tana bayyana yadda ƙasa ta girgiza ne ta ma'aunin ɗaya zuwa bakwai.

Amma a ranar Litinin a Ishikawa girgizar ta kai ma'auni na bakwai.

An samu lalacewar hanyoyi da gadoji masu yawa a wurare da dama. Sannan an samu zaftarewar ƙasa mai matuƙar yawa.

Sai dai mafiya yawan gine-gine ba su rushe ba.

A manyan biranen Toyama da Kanazawa, rayuwa ta fara komawa kusan yadda aka saba.

Na yi magana da wani abokina da ke Kashiwazaki, wanda ya shaida mini cewa. "Abun na da matukar firgitarwa."

"Shi ne mafi muni da na taba fuskanta a nan, don dole muka bar inda muke a gabar teku. Amma yanzu mun koma, kuma komai na tafiya lafiya."

Batu ne na wani aikin injiniyan da aka yi mai cike da nasara, wanda aka fara shi tun shekarar 1923, lokacin da Tokyo ta fuskanci gagarumar girgizar kasa.

Hanyoyin zirga-zirga na Japan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hukumomi sun yi gaggawa wajen gyara hanyoyin zirga-zirga, bayan girgizar kasar ta ranar Litinin

Babbar girgizar kasa ta Kanto, kamar yadda aka fi saninta, ta shafe bangarori masu yawa na birnin, inda gidajen da aka gina da bulo suka ruguje.

Hakan ne ya sa aka fara tunanin wani tsari na yin ginin da za jurewa girgizar kasa a Japan.

Kuma tun daga nan ne ake kara wa sabon gini karfi da karafa da kankare.

Su kuma gine-ginen da aka yi da katako, sai ake kara musu wasu karafa masu kauri.

Sannan a duk lokacin da kasar ta fuskanci babbar girgizar kasa, ana duba irin barnar da aka samu, sai a inganta tsarin.

Babbar nasarar da aka samu ita ce a shekarar 1981, inda daga sannan ne duk wani sabon ginin da za a yi sai an dauki wasu matakai na karfafa ginshikin ginin ta kasa ta yadda zai jurewa girgizar kasa.

Haka kuma bayan aukuwar girgizar kasa ta Kobe a shekarar 1995, an kara koyon wasu darusan.

Wani abun da ke nuna nasarar da aka samu shi ne bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 9 a shekarar 2011, wadda girgizar ta kai maki 5 a Tokyo.

Hakan daidai ya ke da girgizar da kasar da aka samu a shekarar 1923.

A shekarar 1923, girgizar ta lalata birnin, kuma mutane 140,000 sun mutu.

A shekarar 2011 dogayen gine-gine sun yi rawa, tagogi sun farfashe, sai dai babu ginin da ya rushe.

Tsunami ce ta kashe dubban mutane a sannan ba motsin kasa ba.

Akwai hotunan Ishikawa da ke nuna girgizar ta rusa tsofaffin gidagen katako.

Wani sabon gini guda daya ya tuntsura, sai dai wasu kafafen watsa labarai sun yi saurin bayyana cewa an gina shi ne a shekarar 1971.

Haka zalika akwai rahotannin mutane da dama sun mutu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata.

Sai dai da wuya wata kasa a duniya ta fuskanci irin wannan girgizar kasar ba tare da tunanin cewa lamarin zai munana ba.