Yadda yaƙin Gaza ke ci gaba da rarraba kan Isra'ilawa

Hotuna biyu: Benjamin Netanyahu a sama, da kuma na 'yan'uwan Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza suna zanga-zanga a birnin Tel Aviv
    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan Harkokin Ƙasashen Waje
  • Lokacin karatu: Minti 5

Benjamin Netanyahu, firaministan Isra'ila mafi daɗewa a kan mulki, bai sauya buƙatun da ya bayyana ba tun daga farkon yaƙin Gaza.

Ya sha faɗa wa Isra'ilawa da duniya baki ɗaya saƙo ɗaya tun daga ranar da mayaƙan Hamas suka auka ƙasarsa tare da kai hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

"Za mu yi yaƙi domin kare ƙasarmu. Ba za mu ja da baya ba. Za mu yi yaƙi ta ƙasa, da sama, da ruwa. Sai mun lalata abokan gbarmu, kuma sai mun yi nasara.

"Wannan zai zama nasara ce ta adalci a kan zalinci, ta haske a kan duhu, ta rayuwa kan mutuwa. Za mu jajirce a wannan yaƙin, kanmu haɗe sama da koyaushe, cike da tabbacin samun adalci a yunƙurinmu."

Hoton Netanyahu tare da Winston Churchill a bayansa

Asalin hoton, Walter Stonema n via Getty / ABIR SULTAN /AFP via Getty

Bayanan hoto, Netanyahu ya sha nanata cewa burinsa shi ne tarwatsa ƙungiyar Hamas gaba ɗaya a Gaza

Hamas ta yi wa Isra'ila lahani mafi girma a rana ɗaya ta harin ranar 7 ga watan Oktoba. Har yanzu lamarin muhimmi ne a zukatan Isra'ilawa da ke tasiri a duk wani tunani da suke yi game da yaƙin.

Isra'ilawa kaɗan ne suke da tunanin cewa abin da gwamnatinsu ke aikatawa a Gaza ba daidai ba ne, abin da ke nuna kalaman Netanyahu ba su kauce hanya ba.

Kan Isra'ilawa a rabe yake kamar yadda yake tsawon shekaru, amma yanzu da Netanyahu ke jan ragamar ƙasar yana ƙara raba kan su.

Abin da Isra'ilawa ke tunani game da bala'in da ake ciki a Gaza

Yayin da ake ci gaba da yin zanga-zangar Allah wadai da shiirn Netanyahu a birnin Tel Aviv na Isra'ila, wasu mutane na tsaye riƙe da kwalayen da aka rubuta sunan yaron Falasɗinawa da aka kashe a Gaza.

Zanga-zangar neman kawo ƙarshen yaƙin na ƙara yawa - wasu ma sai sun je sansanin sojoji, inda suke son matuƙa jiragen saman soji su gan su ido da ido yayin da suke shirin kai hari a Gaza ko kuma suke dawowa.

Amma har yanzu su ne 'yan ƙalilan a ƙasar.

Timina Peretz, ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar, ta ce sun fara ne bayan Isra'ila ta karya alƙawarin yarjejeniyar da aka ƙulla a watan Maris.

"Mun lura da yawan yaran da aka kashe a makon farko. Na ƙi yarda na yi shuru lokacin da hakan ke faruwa, kisan ƙare-dangi da kuma jefa su cikin yunwa...

Wasu Falasɗinawa da aka raba da gidajensu ne suke karɓar abinci a wurin ba da agaji a Birnin Gaza

Asalin hoton, MOHAMMED SABER/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Ƙuri'un jin ra'ayoyin jama'a da yawa sun nun mafi yawan Yahudawan Isra'ila ba su damu da abin da ke faruwa a Gaza ba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Mukan samu goyon baya a tituna, kamar wasu suna cewa 'mun gode muku'. Akwai kuma mutane da yawa da ke tsine mana saboda hotunan da muke riƙe da su."

Na tambaye ta ko ana kiran su da maciya amanar ƙasa. "Tabbas, da yawansu suna yin hakan. Sukan ce idan muna da irin wannan tunanin gara mu koma Gaza da zama.

"Sun kasa gane cewa sukar masu mulki ɗaya ne daga cikin shika-shikan dimokuradiyya."

Ƙuri'un ra'ayin jama'a da aka tattara tun bayan da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza a watan Maris bayan karya yarjejeniyar tsagaita wuta, sun nuna cewa mafi yawan Yahudawa ba su damu da abin da ke faruwa a Gaza ba.

Wani bincke da ak fitar a kwana uku na ƙarshen watan Yuli daga cibiyar Israeli Democracy Institute ya ce kashi 78 na Yahudawan Isra'ila, waɗanda su ne 4 cikin 5 na jama'ar ƙasar, na ganin "Isra'ila na bakin ƙoƙarinta wajen guje wa haddasa bala'i a kan Falasɗinawa".

Da aka tambaye su ko "suna jin damuwa ko a'a game da rahotonnin yunwa tsakanin mazauna Gaza?"

Kashi 79 na Yahudawan na Isra'ila sun ce ba su jin komai. A gefe guda kuma, kashi 86 na Larabawan Isra'ila, waɗanda 'yan ƙalilan ne, na cewa sun damu sosai ko kuma sun ɗan damu.

Netanyahu ya taɓa cewa: "Mutanen da kawai suke cikin yunwa su ne mutanenmu da Hamas ke garkuwa da su"

Asalin hoton, REUTERS/Ronen Zvulun/Pool

Bayanan hoto, Netanyahu ya taɓa cewa: "Mutanen da kawai suke cikin yunwa su ne mutanenmu da Hamas ke garkuwa da su"

Ms Peretz ta ɗora wa kafofin yaɗa labaran Isra'ila alhakin ƙin nuna wahala da kashe-kashen da ke faruwa a Gaza.

Ta ce alhakinta ne ta dinga fito da abin da ba a saba ji ba a matsayinta na 'yarjarida a gidan talabijin ɗin ƙasar.

Masu zanga-zangar neman a sako mutanen da ke hannun Hamas

Asalin hoton, REUTERS/Ammar Awad

"Nan take na ce yaƙin kuma yana kashe Falasɗinawa da yawa a Gaza, wanda ba wata magana ce mai girma ba. Sai aka hayayyaƙo min."

Hotunan Isra'ilawa da ke tsare

Isra'ilawa kusan 20 ne har yanzu ke tsare a hannun ƙungiyar Hamas a Gaza.

Hotunansu da Hamas ɗin ta fitar a kwanan nan sun tayar wa 'yan'uwa da sauran 'yan ƙasa hankali.

Tun daga lokacin kuma suka koma abin tattaunawa a kodayushe.

Hoton sojin Isra'ila Evyatar David a ƙanjame, wanda Hamas ke garkuwa da shi a Gaza

Asalin hoton, The Hostages Families Forum Headquarters

Bayanan hoto, Hamas ta fitar da bidiyon Evyatar David, abin da ya jawo mummuna martani daga Isra'ilawa da kuma shugaannin ƙasashen Turai

Na haɗu da wani matashi mai suna Aaron, wanda jami'in sojin Isra'ila ne kuma ya yi yaƙi a Gaza.

Yana ganin abin da Isra'ila ke yi a Gaza daidai ne.

"Ka zo Gaza ka ga wani ramin ƙarƙashin ƙasa," in ji shi. "Ka ga yadda ake rasa iskar shaƙa a tsananin zafi yayin da muke yaƙar 'yanta'adda da ke ɓuya a bayan mata da ƙananan yara...

"Abu ne mai sauƙi mutum ya zauna a ɗaki mai sanyi kuma ya dinga yanke wa mutane hukunci."

Rashin goyon baya tun kafin harin 7 ga Oktoba

Kafin a kai harin ranar 7 ga watan Oktoba, dubban Isra'ilawa ke zanga-zangar Allah wadai da shirn sauye-sauye.

"Wannan gwamnatin ce mafi baƙin jini tun kafin fara yaƙin nan," in ji marubuciya Ms Scheindlin.

"Jim kaɗan bayan fara yaƙin, ba kamar yadda kake gani a wasu ƙasashe ba, babu wanda ya goya wa gwamnati baya."

Firaministan Isra'ila Benjmain Netanyahu

Asalin hoton, ABIR SULTAN/Pool via REUTERS

Su kuwa masu tsattsauran ra'ayi da suka taimaka wa Netanyahu kafa gwamnati sun riƙe wuta cewa ba za a kawo ƙarshen yaƙin ba har sai an gama a Hamas baki ɗaya.

A gefe guda kuma wasu na cewa ya ƙi yarda a kawo ƙarshen yaƙin ne saboda ya tsira daga gurfana a gaban kotu.

A matsayinsa na ɗan ƙasa, zai fuskanci masu bincike game da yadda Hamas ta iya kai hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Ga kuma shari'ar da yake fuskanta ta zargin cin hanci da rashawa, wadda za ta iya kaiwa ga yanke masa hukuncin zaman gidan yari.

Abokan siyasarsa kamar ministan kuɗi Bezalel Smotrich, da ministan tsaron cikin gida Itamar Ben-Gvir sun sha yin barazanar cewa za su kifar da gwamnatin idan ya ƙulla kowace irin yarjejeniya da Hamas.