Hotunan ɓarnar mummunar gobarar daji a Amurka

Lokacin karatu: Minti 2

Jami'ai a birnin Los Angeles sun ce mummunar gobarar daji ta lalata sama da gidaje dubu 10 da wasu gine-gine a jihar California.

Mutum 10 aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da neman wasu.

Kuma hukumomi sun ce akwai yiwuwar yawan waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Ƙiyasin ɓarnar da gobarar ta yi ya kai aƙalla dala miliyan 135.

Mutane da dama sun rasa gidajensu a mummunan bala'in da ya afku musu.

An tura jami'an tsaro na ƙasa 400 a yankin domin taimaka wa ƴansanda aiki, bayan da aka samu rahotanni sata ko kwashe kayan jama'a

Ɗan majalisa mai wakiltar Carlifornia, Brad Sherman ya ce gobarar ita ce mafi muni a tarihin Amurka.