Lookman ne ɗan Afrika tilo a jerin 'yan takarar Ballon d'Or

h

Asalin hoton, PA Media

Lokacin karatu: Minti 2

'Yan wasa uku ne 'yan Afrika suke takarar lashe kyautar Ballon d'Or, ta mata da maza ta 2024, yayin da ɗan wasan Najeriya Ademola Lookman yake cikin jerin maza 30 masu takara.

Dan wasan Atlantan na cikin jerin sunayen 'yan wasan shida da suka fito daga Ingila da Spain bayan tawagogin biyu sun buga wasan ƙarshe na Euro 2024 a Jamus.

Cikinsu akwai Lamine Yamal - ɗan wasan gefen Barcelona da ya cika shekara 17 a watan Yuli - wanda yake da tsatson Morocco da Equatorial guinea.

Akwai kuma 'yan wasan Manchester City da Arsenal da suka yi na ɗaya da na biyu a gasar Premier, amma karon farko tun 2003 babu Cristiano Ronaldo haka zalika Lionel Messi cikin jerin sunayen.

Nahiyar Afrika ta samu wakilcin Barbra Banda daga Zambia da Tabitha Chawinga daga Malawi a jerin sunayen mata.

d

Asalin hoton, Getty Images

Wasannin ƙarshe biyu da Lookman ya buga

Ya ɗauki Lookman dogon lokaci kafin ya hau layi, amma ko shakka babu shekarar 2024 ita ce wacce ta fi kowacce a wurinsa.

Dan wasan mai shekara 26 ya ci kwallo uku kuma yana cikin fitattun 'yan wasan Najeriya da suka kai Super Eagles wasan ƙarshe na kofin Nahiyar Afrika na 2023 a farkon wannan shekarar, sai dai sun yi rashin ansara da ci 2-1 a hannun masu masaukin baƙi Ivory Coast.

Ya kuma ci kwallo 11 wanda hakan ya taimaka wa ƙungiyarsa ta Atlanta ta kammala Serie A a matsayi na huɗu, kuma ta samu tikitin gasar Uefa Champions Lig.

Amma lokacin da ya fi dadi a rayuwarsa shi ne a watan Mayu a wasan ƙarshe na Europa da ya ci kwallo uku a wasansu da Bayern Leverkusen 3-0 suka lashe kofin. Hakan ya kawo ƙarshen wasannin da ƙungiyar ta Jamus ta yi ba tare da rashin nasara.

Ga jerin mutanen da aka fitar don takarar kyautar.

s

Asalin hoton, BBC Sport

  • Jude Bellingham (Real Madrid)
  • Phil Foden (Man City)
  • Ruben Dias (Man City)
  • Federico Valverde (Real Madrid)
  • Emiliano Martinez (Aston VIlla)
  • Erling Haaland (Man City)
  • Nicolas Williams (Athletic Bilbao)
  • Granit Xhaka (Bayer Leverkusen)
  • Artem Dovbik (Roma)
  • Toni Kroos (Real Madrid)
  • Vinicius Jr (Real Madrid)
  • Martin Odegaard (Arsenal)
  • Dani Olmo (Barcelona)
  • Florian Wirtz (Bayer Leverkusen)
  • Mats Hummels (Roma)
  • Rodri (Man City)
  • Declan Rice (Arsenal)
  • Harry Kane (Bayern Munich)
  • Cole Palmer (Chelsea)
  • Vitinha (PSG)
  • Dani Carvajal (Real Madrid)
  • William Saliba (Arsenal)
  • Lamine Yamal (Barcelona)
  • Bukayo Saka (Arsenal)
  • Hakan Calhanoglu (Inter)
  • Antonio Rudiger (Real Madrid)
  • Kylian Mbappe (Real Madrid)
  • Lautaro Martinez (Inter)
  • Ademola Lookman (Atalanta)
  • Alejandro Grimaldo (Bayer Leverkusen)