Gane Mini Hanya: Kan Zakkar fidda-kai
Lokacin karatu: Minti 1
Yayinda ake shirye-shiryen zuwan ƙaramar sallah, ana sa ran al'ummar musulmi da suka yi azumin watan Ramadan za su fitar da zakkar fidda kai da ake fitarwa a ƙarshen azumin.
A ƙarshen kowane azumin watan na Ramadana a kan buƙaci kowane musulmi ya bayar da sadakar wani nau'in abinci ga mabuƙata da suke tare da su domin su ma su yi bukukuwan na salla cikin sauƙi.
Kan haka ne BBC ta tattauna da Malam Ibrahim Khalil wani babban malamin addinin musulunci a Najeriya, wanda ya yi masa ƙarin bayani game da zakkar ta fid da kai








