Shugabannin ƙasashe bakwai da suka taɓa tuntuɓe suka faɗi a bainar jama'a

    • Marubuci, Abdou Aziz Diédhiou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 5

Abin da ke tsakanin shugabanni da tuntsirewa su faɗi ƙasa warwas kamar tauna harshe ne da haƙora ke yi ba tare da sani ba.

To haka lamarin yake tsakanin shugabanni da faɗuwa yayin da jama'a ke kallon su kamar wasu halittu na musamman.

Shugabanni mutane ne kamar kowa, haifar su aka yi suka girma kuma suna faɗi tashi kamar kowanne mutum.

An ɗauki hotunan shugabanni da dama yayin da suka yi tuntuɓe ko suka faɗi ƙasa.

BBC ta kawo muku irin wannan faɗuwa da yadda ta zama tarihi.

1- Bola Tinubu na Najeriya - 2026

Shugaba Tinubu na Najeriya ne shugaban ƙasa na baya-bayan nan da ya faɗi a bainar jama'a.

Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga yadda Shugaba Tinubu ya faɗi yayin da ake yi masa tarbar ban girma a wata ziyarar aiki da ya je ƙasar Turkiyya a makon da ya gabata.

An ga yadda shugaban ƙasar mai shekara 73 ya yi tuntuɓe sannan ya faɗi a ƙasa, inda aka ga mutane sun yi gaggawar kai masa ɗauki, kafin a yi saurin ɗauke gurin, daga baya kuma aka ga shugaban na tafiya jere da takwararansa an Turkiyya.

Ba wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ya faɗi a bainar jama'a ba.

Ko a watan Yunin 2024 ma ya faɗi, inda daga baya ya mayar da faɗuwar raha da cewa mutane sun ɗauka rawa ya yi.

Ɗaya daga cikin masu taimaka masa lokacin ya bayyana faɗuwar da ''kauce wa matattakala''.

2- Robert Mugabe na Zimbabwe - 2015

A shekarar 2015 ne Robert Mugabe, mai shekara 90 a lokacin ya yi wata faɗuwa da ba za a manta ba.

Yayin da yake sauka daga dandamalin da ya gabatar da jawabi, Mista Mugabe ya yi tuntuɓe a matattakala, lamarin da ya sa ya faɗi a kan gwiwoyinsa a gaban ɗaruruwan mutane.

Bidiyo da hotunan faɗuwar sun bazu a shafukan sada zumunta, duk kuwa da yunƙurin da jami'an tsaronsa suka yi a lokacin na saka ƴanjarida goge hotunan da suka ɗauka a lokacin.

A wannan shekarar kuma Mugabe ya sake faɗuwa a wani taro da ya halarta a Indiya.

3- Joe Biden na Amurka - 2021

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya shiga jerin shugabannin ƙasashen duniya da suka faɗi a bainar jama'a.

Ƴan adawarsa a lokacin sun ɗauki wannan faɗuwa da muhimmanci inda suka riƙa sukarsa da ita.

4- Gerald Ford na Amurka -1975

Shugaban Amurka na 38 ya yi faɗuwar da ta shiga tarihi, a lokacin da yake sauka daga jirgi.

A lokacin wata ziyara a ƙasar Austria a 1975, Shugaba Gerald Ford ya goce wa matattakalar jirgi, lamarin da ya sa ya gangaro ƙasa ya faɗi a gaban kyamarori.

Daga baya jami'an tsaronsa sun taimaka masa ya miƙe.

5- Donald Trump na Amurka -2025

A watan Yunin 2025, Donald Trump ya yi tuntuɓe yayin da yake shirin shiga jirginsa a sansanin sojin sama na Andrew da ke Jihar Maryland.

Duk da cewa bai faɗi ƙasa ba, lamarin ya ɗauki hankali, inda aka riƙa muhawara a kai tare da kwatanta faɗuwarsa da ta Biden, wanda a lokacin faɗuwarsa Trump ya riƙa tsokanarsa da 'Joe mai zamiya'

6- Salva Kiir na South Sudan -2022

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya shiga cikin wannan lissafi, duk da cewa tuntuɓen da ya yi bai kammala kai shi ƙasa ba.

A 2022 wani bidiyo ya nuna yadda shugaban na Sudan ta Kudu ya goce wa matattakala a lokacin wani biki a gaban jami'an gwamnatinsa da sojoji.

7- Paul Deschanel na France-1920

A shekarar 1920, Paul Deschanel, wanda shi ne shugaban tsohuwar Jamhuriyar Faransa ya faɗo daga jirgin ƙasa.

Bayanai sun ce faɗuwar ta taimaka masa kafa tarihi, inda ya ajiye muƙaminsa wata bakwai bayan zaɓensa.

A lokacin ajiye aikinsa ya bayyana dalilai na rashin lafiya.

Wannan lamari na nuna rashin lafiya da kuzarin wasu shugabannin sakamakon yawan shekaru.