Illar hazo ga lafiyar mutane da yadda za ku kare kanku

Kamar sassan arewacin Najeriya a yanzu, gurɓacewar iska ta ta'azzara sosai a birnin Lahore na Pakistan a watan Nuwamba

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kamar sassan arewacin Najeriya a yanzu, gurɓacewar iska ta ta'azzara sosai a birnin Lahore na Pakistan a watan Nuwamba
    • Marubuci, Victoria Lindrea
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo da ƙura a sassan ƙasar daga ranar Litinin zuwa Laraba.

Hukumar Nigerian Meteorological Agency (NiMet) ta ce yankunan arewaci da na tsakiyar Najeriya ne za su fi fuskantar yanayin na hazo da da ƙura.

NiMet ta ce za a samu matsala wajen hangen nesa saboda hazon a tsawon kwanakin ukun.

Hukumar ta buƙaci jama'ar da ke zaune a yankunan da hazon zai fi tsanani da su ɗauki matakan kariya, musamman wadanda ke fama da wata larura da ba ta son ƙura kamar Asma, ko kuma cutukan da suka shafi numfashi.

Kazalika, NiMet ta shawarci kamfanonin jiragen sama da ke zirga-zirga a Najeriya da su tabbata sun samu cikakken rahoto game da yanayin da za a iya kasancewa da shi a iya kwanakin da aka yi hasashen hazon.

Akan ce iska na da inganci ne idan ta samu maki daga 0 zuwa 50. Amma idan ta wuce 300 to ta zama mai haɗari. An taɓa samun mafi gurɓacewa a Pakistan mai maki 1,900 a farkon watan nan.

A watan Nuwamba ma gurɓatattun yanayi sun dira a yankuna da dama na Indiya da Pakistan, yayin da hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna dunƙulallen hazo da ke yawo a saman biranen Lahore da Delhi.

Iskar birnin Lahore mai sama da mutum miliyan 14, na da ma'aunin ingantacciyar iska 400 a ranar Talata 12 ga watan Nuwamba, a cewar IQAir da ke bin diddigin ingancin iska a duniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An rufe makarantu da wuraren shaƙatawa. An rage awannin gudanar da harkoki, sannan aka taƙaita zirga-zirgar mutane.

Amma ta yaya mutane za su kare kan su daga barazanar hazo - kuma ko hakan zai yi aiki?

An daɗe da sanin cewa gurɓatacciyar iska na jawo wa mutane rashin lafiya.

An yi ƙiyasin cewa gurɓatacciyar iska ta jawo wa mutane kusan miliyan 4.2 mutuwar wuri a faɗin duniya a 2019, a cewar alƙaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Ƙananan abubuwa da ake kira particulate matter a Turance (PM) kan shiga cikin jinin mutum ta huhunsa, inda sukan ratsa jiki - abin da zai iya haifar da larura ta har abada kamar ciwon zuciya, ko bugun jini, ko kuma kansar huhu.

A ranar Talata a birnin Lahore, an samu cunkoson waɗannan abubuwan (PM) masu girman 2.5 micrometres sama da sau 50 na fiye da adadin yawan da ake buƙata, in ji IQAir.

"Yaɗuwar cutukan idanu saboda ƙwayoyin cuta sakamakon hayaƙi, da ƙura, da sinadarai na jawo barazana ga lafiyar ɗan'adam," kamar yadda gwamnatin Punjab ta bayyana a ƙarshen mako.

Hukumomi sun ce sama da mutum 40,000 sun kai kansu asibiti saboda cutar asthma, da ƙaiƙayi a maƙogwaro, da kuma tari.

Hazo na haifar da larurar hana huhun yara girma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hazo na haifar da larurar hana huhun yara girma

Ku nemi ƙarin bayani kan yanayin kuma ku zauna a gida

To me mutum zai iya yi ya taimaka wa kansa?

Kuna iya farawa da nazari game da ingancin iskar ta hanyar sauraron kafofin labarai - idan za ku iya kuma - ku duba rahoton yanayin a shafin World Air Quality Index a manjahar cibiyar.

Idan ana hazo, akan ba da shawarar mutane su zauna a gida, musamman yara, da tsofaffi, da marasa cikakkiyar lafiya.

Duk lokacin da ma'aunin ingancin iskar ya kai sama da 100 ana kallonsa a matsayin "mai haɗari ga wasu mutane", a cewar likitoci.

Yanzu haka birnin Lahore na Pakistan na fama da gurɓatacciyar iska da ba a saba gani ba

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Birnin Lahore na Pakistan na fama da gurɓatacciyar iska da ba a saba gani ba

A saka takunkumi

Idan ya zama sai an fita, akwai 'yan hanyoyi da za a iya bi masu sauƙi. Ɗaya daga ciki shi ne rufe fuska, ko kuma baki da hanci takamaimai.

Hazo na ɗauke da hayaƙi da ƙura. Yana da launin toka-toka, da kuma ƙauri-ƙauri kamar ana ƙona wani abu da ke saka mutum ya ji maƙaƙi a huhunsa.

Takunkumi kan rage yawan abubuwan da mutum ke shaƙa - ko kuma dai haka ake fata - amma kuma dole ne a lura sosai da irin takunkumin da ya kamata a saka, da ma yadda ya kamata a saka shi.

Mazauna birnin Bangkok na Thailand ma na fama da hazon

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Mazauna birnin Bangkok na Thailand ma na fama da hazon

Wani bincike da ƙwararru suka yi a 2020 lokacin annobar korona, ya gano cewa takunkuman da aka yi da yadi na ba da ƙaramar kariya ne kawai ga ƙananan ƙwayoyin abubuwa.

Takunkuman da ake kira N95 (ko FFP2) na ɗauke da mayafin kariya da yawa, wanda ke ba da kariya mai girma sosai.

Hukumar WHo ta ce FFP2 (da ƙasashen Turai suka amince da su) kan kare mutum daga shaƙar ƙwayoyin abubuwa da kashi 94 cikin 100, yayin da N95 (wanda Amurka ta amince da shi) ke kare kashi 95.

Sai dai saka kowane irin takunkumi ya fi babu.

Idan za a saka shi, a tabbatar an lura da yanayin fudkar mutum da gashin fuska. Kuma dole ne a rufe baki da hanci a lokaci guda.

Mamakon hazo bai hana mazauna birnin Lahore zirga-zirga ba

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Mamakon hazo bai hana mazauna birnin Lahore zirga-zirga ba

Taka-tsantsan wajen shaƙar nimfashi

Duk lokacin da muka buɗe tagogi da ƙofofi, hakan na bai wa abubuwan waje shigowa cikin ɗaki, cikinsu kuma har da hazo.

Saboda haka, idan ana mamakon hazo bai kamata a buɗe tagogi da ƙofofi ba sai ya zama dole.

Na'urorin tace iska za su iya taimakawa wajen rage tasirin hazon. Irin waɗannan ƙananan na'urori kan daƙile ƙura kuma ta inganta iska a cikin ɗakuna.

Na'urar da aka fi ba da shawarar a yi amfani da ita ita ce Hepa (High Efficiency Particulate Air), wadda aka fi samu a cikin jiragen sama na zamani.

Na'urar mai inganci kan "dakile kashi 99.97 cikin 100 na dattin da ke cikin iska".

Sai dai kuma girman na'urar ma yana da amfani matuƙa. Dole ne a kwatanta girman na'urar da kuma na ɗakin da ake so a tsaftace, sannan dole a dinga sauya rariyar na'urar akai-akai.

Babbar kotun yankin Punjab a Pakistan ta ɗora mafi yawan alhakin hazon kan hayaƙin da ababen hawa ke fitarwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babbar kotun yankin Punjab a Pakistan ta ɗora mafi yawan alhakin hazon kan hayaƙin da ababen hawa ke fitarwa

Ƙara yawan makarai

Mamakon hazo kenan ya lulluɓe yankin Siberia na Rasha

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mamakon hazo kenan ya lulluɓe yankin Siberia na Rasha

Daga ƙarshe, likitoci na ba da shawara ga mazauna cikin yanayin hazo da su ƙara ƙwayoyin halittar da ke ba su kariya a jikinsu, inda zai ba su damar yaƙi da tasirin hazon da suke shaƙa.

Akwai wahala wajen motsa jiki saboda yanayin da ake ciki, amma ƙwararru na ba da shawarar mutane su dinga motsawa, su ci abinci mai ƙara lafiya, kuma su sha ruwa da yawa.

Idan mutum ya ɗan ji rashin lafiya, musamman idan iska ce ta jawo - kamar atishawa, ko maƙaƙi a maƙogwaro, ko ciwon kai. A irin wannan yanayi, shan shayi mai ɗauke da 'ya'yan itatuwa kan taimaka.