Me ya sa Turkiyya ke son shiga ƙawancen tattalin arziki na BRICS?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Selin Girit and Mahmut Hamsici
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
“Shugabanmu ya bayyana ƙarara cewa Turkiyya na son shiga duka muhimman ƙungiyoyi, ciki kuwa har da BRICS,” in ji Omer Celik, kakakin jam'iyyar Shugaba Erdogan mai mulkin Turkiyya.
Bai tabbatar da rahotonnin ko Turkiyya ta nemi shiga ƙungiyar a hukumance ba, to amma ya ce “ana kan hakan”.
Ana sa ran ƙungiyar ta BRICS (ƙasashen da tattalin arziƙinsu ke haɓaka cikin sauri, Brazil, Rasha China, Indiya da Afirka ta Kudu) za ta tattauna batun amincewa da sabbin mambobi a babban taron da za a gudanar a garin Kazan da ke yammacin Rasha tsakanin 22-24 ga watan Octoba.
Me zai faru idan Turkiyya ta shiga BRICS?
Idan aka gayyaci Turkiyya kuma ta shiga, za ta kasance ƙasar NATO ta farko da ta shiga wani ƙawancen tattalin arziki da ba na ƙasashen Yamma ba, wanda kuma Rasha ko China ke jagoranta.
“Ina tunanin hakan zai zama wata manuniya mai muhimmanci, ba wai ga Turkiyya ko BRICS ba, har ma ga NATO da ƙasashen Yamma,” in ji Kerim Has, wani ƙwararre kan alaƙar Turkiyya da Rasha.
Ya ƙara da cewa Turkiyya na buƙatar zuba jari daga ƙasashen waje, don haka dole ne ta faɗaɗa dangantakarta da sauran ƙasashen duniya, musamman yanzu da tattalin arzikinta ke fama matsaloli.
“Idan tattalin arzikin Turkiyya ya ruguje, hakan zai shafi bankunan ƙasashen Turai, saboda tattalin arzikin Turkiyya ya dogara da bankunan,” in ji shi. ''Kusan rabin kasuwancin Turkiyya tana yi ne da ƙasashen Turai''.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Tarayyar Turai ta ce ƙungiyar EU ce babbar ƙawar kasuwarcin Turkiyya, kusan kashi 31.8 na kasuwancin Turkiyya da EU take yi. A 2022 yawan kasuwancin da ke tsakanin Turkiyya da Turai ya kai euro biliyan 200.
A cewarsa hakan ne ma ya sa ƙasashen Turai suka rufe idanunsu kan yadda Turkiyya ta ƙi aiki da takunkuman da aka sanya wa Rasha bayan mamayar da ta yi wa Ukaine.
“Ƙasashen Yamma na kawar da idanunsu kan yadda Turkiyya ke ƙarfafa alaƙar kasuwancinta da Rasha da kuma ƙungiyar ƙasashen,” in ji mista Has.
“Haka kuma, idan Turkiyya wadda mamba ce a ƙungiyar tsaro ta NATO ta zama mamba a ƙungiyar BRICS, ɗaya daga cikin nauyin da zai rataya a wuyanta, shi ne rage ko sassauta kalamanta game da yadda ƙasashen Yamma ke kiran ƙungiyar da su''.
“Haka kuma wani nauyin da zai rataya a kan Turkiyya a matsayin mamba a BRICS, musamman daga ɓangaren Amurka da Birtaniya shi ne ta hana BRICS komawa mai adawa da ƙasashen Yamma''.
Wace ce ƙungiyar BRICS?
Da farko ana kiranta da BRIC, wato ƙungiyar ƙasashen da tattalin arzikinsu ke haɓaka cikin sauri. An samar da ƙungiyar a 2006 daga ƙasashen Brazil da Rasha da India da kuma China. Ƙungiyar ta koma BRICS a 2010 bayan da Afirka ta Kudu ta shiga.
An kafa ƙungiyar BRICS ne domin haɗa kan ƙasashe masu bunƙasar tattalin arziki wuri guda, domin tunkarar manyan ƙasashen Yamma da masu ƙarfin tattalin arziki.

Ƙawancen ya samu gagarumar bunƙasa a shekarun baya-bayan nan, inda yanzu ya haɗa ƙasashen Iran da Masar da Habasha da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Ƙasar Saudiyya ma ta ce tana duba yiwuwar shiga, yayin da Azerbaijan ya nemi buƙatar shiga a hukumance.
Wasu rahotonni da suka bayyana a kamfanin dillancin labarai na Bloomberg a makon da ya gabata sun nuna cewa Turkiyya ta nemi buƙatar shiga ƙungiyar tun watanni da dama da suka gabata.
Tun a a shekarar 2018 Shugaba Erdogan ya bayyana sha'awar ƙasarsa ta shiga ƙungiyar BRICS, a lokacin taron ƙungiyar na 10 a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Me ya sa Turkiyya ke son shiga BRICS?
Shugaba Erdogan - wanda ke jagorantar ƙasar fiye da shekara 20 da suka gabata, yake kuma nuna damuwa kan jan ƙafar da Turkiyya ke fuskanta na zama cikakkiyar mamba a ƙungiyar EU - na cewa ƙasarsa na buƙatar kyautata alaƙarta da duka ƙasashen Gabashi da Yammacin duniya.
“Ba sai mun zaɓa tsakanin ƙungiyar EU da ƙungiyar SCO ta haɗin kan ƙasashen yankin Asiya ba,” kamar yadda Mista Erdogan ya bayyana, yana la'akari da ƙungiyar BRICS da China da Rasha ke jagoranta.
“Mu muna son gina alaƙa da duka ƙungiyoyin domin samun nasara”.

Asalin hoton, Getty Images
A 2022, adadin kasuwancin da ke tsakanin Turkiyya da Rasha ya kai kashi 11 na duka kasuwancin da ƙasar ke yi, yayin da kasuwancinta da China ke da kashi 7.2.
Kerim ya yi amanna cewa Rasha za ta goyi bayan shigar Turkiyya cikin ƙungiyar BRICS
“Babban abin da ke gaban Rasha, shi ne yadda za ta ririta tattalin arzikinta domin ci gaba da yaƙin Ukraine, domin tabbatar da tattalin arzikinta bai ruguje ba sakamkon jerin takunkuman ƙasashen Yamma,” in ji shi.
“Don haka. dole ne Moscow ta tabbatar da kusancinta da Turkiyya. Ƙawancensu na da girma da faɗi, kama daga makamashi zuwa kasuwanci da yawon buɗe ido. Haka kuma Rashar na son ƙulla ƙawance da wata ƙasar NATO.”
Yusuf Can daga cibiyar Wilson ta Amurka ya ce ba a ganin ƙoƙarin Turkiyya na shiga BRISC da SCO da sauran ƙungiyoyi a matsayin wata damuwa ba.
“NATO za ta ribatu da hakan, kasancewar mambanta na cikin ƙawancen,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Matsalar tattalin arziki
Turkiyya na fama da matsin tattalin arziki, kuma ana kallon dogarar da ta yi da ƙasashen waje a ciwon bashi a matsayin ɗaya daga cikin dalilan ƙasar na faɗaɗa hulɗarta.
Alƙaluman Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya nuna cewa a shekarar 2023, Turkiyya ce ƙasa ta 17 mafi girman tattalin arziki a duniya.
Ra'ayoyin a;l'ummar ƙasar a baya-bayan nan sun nuna cewa matsalar tsadar rayuwa ce ta fi damun 'yan ƙasar.
Shugaba Erdogan ya riƙa matsa wa babban bankin ƙasar lamba domin ya ci gaba da karɓo bashi a kudin ruwa mai sauƙi, don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa ministan kuɗin ƙasar, Mehmet Simsek ya yi iƙirarin cewa hauhawar farshin da ake samu a ƙasar ''shi ne mafi muni'', da dama na fargabar sake samun mafi muni a nan gaba.
“Tun bayan naɗa Mista Simsek, hauhawar farashi ke ci gaba da ƙaruwa, kuma darajar kuɗin ƙasar ta ci gaba da faɗuwa, duk kuwa da ƙarin kuɗin ruwa da aka yi daga kashi 8 zuwa kashi 50...'', in ji Darka Umit na jami'ar Berlin.
Kawo yanzu dai ba za a iya cewa komai ba game da makomar tattalin arzikin Turkiyya, kamar yadda masana suka bayyana.
“Hauhawar farashi zai ragu a watanni masu zuwa saboda shirin da aka yi,” in ji Dakta Akcay.
“To sai dai raguwar hauhawar farashi, ba shi ne ke nuna cewa an kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar ba. Indai ba a ƙara wa ma'aikata albashi aka yi ba, sannan aka ɓullo da shirye-shiryen tallafa wa talakawa, to matsalar za ta ci gaba''.
Idan buƙatar Turkiyya ta shiga ƙawancen da ba na ƙasashen Yamma ta yi nasara, hakan ka iya daidaita tattalin arzikinta.
To sai dai ana ganin babbar manufar Turkiyya ta shiga BRICS ba ya rasa nasaba da siyasa da kuma manufofin Shugaba Erdogan kusan 360 na ƙasashen waje ba.











