Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na haihu a cikin mota ba tare da taimako ba'
Wannan ne yadda lauya Julia Assis ta bayyana wa abokanta haihuwar 'yarta ta biyu, wadda ta faru a São Paulo a farkon watan Disamba.
"Mata za su so haihuwa cikin gaggawa, amma babu wadda za ta so ta haihu ita kaɗai, a kan hanya, a cikin mota, ba tare da taimakon likita ba," in ji ta.
Haihuwata ta farko ta hanyar tiyata ce, amma sun shaida min cewa wannan haihuwar tawa ta biyu za ta zo cikin sauƙi saboda jikina ya riga ya saba. In ji ta.
Lokacin da na shiga ɗakin haihuwa bayan na haihu a mota, sai mutane suka tafa min.
Doula ya ce "haihuwa ce irin wadda ba a taɓa samun irin ta ba.” Amma na ji tsoro sosai, na gigice, kuma na shiga cikin damuwa a kan 'yata da mahaifiyata, wadanda suke gefena.
Duk da cewa ba a asibiti na haihu ba, an yi rajistar jaririyar Julia kamar an haife ta ne a asibiti.
Ma'aikatar Lafiya ta bayyana cewa haihuwa a asibiti ita ce mafi aminci da kuma lafiya inda bayanai suka nuna cewa ita ce zaɓin kusan kashi 98% na mata.
“Lokacin da na fara jin alamun naƙuda a safiyar ranar Lahadi, ciwon ya riƙa ƙaruwa har zuwa ranar Litinin, ranar Talata ma haka, ciwon ya kasance tamkar ciwon mara a lokacin jinin al`ada.”
“A ranar Laraba da Alhamis, zafin bai ragu ba ko kadan, har na kasa jurewa, wajen karfe 4 na safe, zafin ya sake ƙaruwa sosai har na kasa kwanciya, sai na je ban-ɗaki, a nan sai na ji alamun kamar ruwa ya kusa fashewa, sai na shiga bahon wanka ko zafin da nake ji zai ragu.”
“Kashe-gari sai na je asibiti, wajen likita saboda ya duba ni, da ya duba sai ya ce ruwan haihuwa ya kusan fashewa amma akwai sauran lokaci, ya ce na koma gida, bayan na koma, sai ciwon naƙudar ya ƙaru sosai, ya riƙa taso min duk bayan minti goma zuwa ashirin.
Lokacin haihuwa, ana iya samun jaririn ya zo a juye, a lokacin da buɗewar bakin mahaifa ya kai fadin 'sentimita' huɗu, wannan lokacin zai yi kai wa tsawon kwanaki, daga nan kuma sai lokacin haihuwar inda jariri zai fito, in ji likita Ricardo Porto Tedesco.
Abin da ake nufi a nan shi ne, tsawon naƙuda ya danganta ga yanayin ko wace mace.
Likita Ricardo Tedesco ya ce naƙuda na iya farawa a lokacin da ƙofar mahaifa ta buɗe zuwa santimita biyar ko fiye da haka, ko kuma lokacin da ciwon naƙuda ke tashi sau uku a cikin minti goma.
A lamarin Julia, tsoron yin tiyatan ya sa lamarinta ya sha banban.
“Tunda na farka ina son zuwa asitibi da wuri, tun a lokacin ma da na fara jin alamun zafin naƙuda, amma aka ce min na jira har lokacin haihuwar ta yi idan ba haka ba kuma idan na je, tiyata za su iya mun.” In ji ta
“Da karfe 1:37pm, na ji kamar ruwa haihuwa zai fashe kuma dama an yanke shawarar malamin jinya ne zai zo har gida ya duba ni kafin lokacin haihuwar ya yi, amma hakan bai yiwu ba saboda wajen da zai zo akwai nisa daga gida na.”
“Da karfe biyu na rana, ina cikin bahon wanka yanda likita ya ce min na yi, ni kadai duk da dai mijina da mahaifiyata suna nan, zafin naƙudar sai ƙaruwa yake yi tare da alamun ruwan haihuwan ya kusa fashewa.”
“Toh, karfe biyu da rabi na kasa jure wa zafin, kawai sai na fara ihu ina kuka har malamin jinyar ya jiyo ta waya, shi ne ya ce ayi maza a kai ni asibiti.
“A hanyar zuwa asibiti, a cikin mota, sai na fara jin alamun jaririn na cuso kai har ya yi alamun fitowa, sai na fada wa mahaifiyata, shi ne a firgice ta saka hannu don ta taro jaririn, muna shiga ɓangaren haihuwa da motar, kawai sai jaririn ya fito”
“Da aka bude motar, da kaina na sauka, har na taka na zauna a kan gujerar da ake tura marasa lafiya, tare ta jaririyata a hannuna, mahaifiyata kuma duk fuskar tana cike da tsoro da gigicewa.
A cikin asibiti, sa'o'i kadan bayan haihuwar, likitocin sun gano cewa Julia na fama da zubar jini, wanda sai da aka yi mata ƙarin jini leda biyu, amma ta warke cikin mako guda.
Haɗurra
A cewar masana, haihuwa musamman irin wadda mata ke yi a hanya kafin isa asibiti suna da hadurra kamar haka:
- Za a iya samun rashin kyakkyawar kula da sabon jariri ko yiwuwar rikicewa a bangaren uwa;
- Za a iya samun haɗarin rauni - jaririn na iya faɗi ƙasa ko kuma da wuya ya iya samun tallafi a lokacin da ya fito daga ciki.
Game da haihuwar inda ba taimakon likita ko masani, za a kuma iya samun hadarin wahala ga jaririn idan naƙudar ta yi tsawo a cewar Ricardo Tedesco.
"A cikin waɗannan wani yanayi kuma inda ake buƙatar iskar da ake karawa zuwa mahaifa, za iya wahala a samu.
“Za a kuma iya samun matsalar da za ta haifar da zubar jini mai yawa.”
Mene ne ya kamata a yi idan haihuwa ta zo babu ƙwararren da zai taimaka?
Abu mafi mahimmanci shi ne tabbatar da cewa jariri yana cikin dumi, a cewar likita Ana Cris Duarte.
"Ya na da kyau a sami tawul don nannade jariri. Sannan kuma za a iya ɗora jaririn a jikin mahaifiyarsa, fata da fata, a rufe jiki da kyau, sannan ku je asibiti, neman taimako, wannan shi ne babban abu, "in ji shi.
"Ba sai an yanke cibiyar jaririn ba, ba sai an cire mahaifa ba, na ga wasu mutane ma suna ɗaure cibiyar jariri da igiyar takalmi, ba sai an yi ko daya daga wadannan ba" in ji Likitan
Ya na da matuƙar mahimmanci a nemi taimakon gaggawa don tabbatar da cewa uwa da yaro suna lafiya.
“Kusan kashi 5% na jarirai suna bukatar taimako wajen numfashi a lokacin haihuwa, Har ila yau, zubar jini bayan haihuwa na iya faruwa.