Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG ta lashe Ligue 1 na bana na 12 jimilla
Paris St-Germain ta lashe Ligue 1 na kakar nan, bayan da wadda take ta biyun teburi Monaco ta yi rashin nasara 3-2 a gidan Lyon ranar Lahadi.
Kenan PSG ta samu damar daukar kofin babbar gasar tamaula ta Faransa ta bana da tazarar maki 13, ba wadda za ta tarar da ita, bayan da saura wasa uku a gama kakar nan.
Tun a ranar Asabar ya kamata PSG ta lashe kofin bana, amma sai ta tashi 3-3 a gida da Le Havre a karawar mako na 31.
Wannan shi ne kofin Ligue 1 da PSG ta dauka na 12 jimilla, kuma na 10 cikin kaka 11.
Mintin farko da take leda Monaco ta fara cin kwallo ta hannun Wissam Ben Yedder, daga baya Lyon ta farke ta hannun Alexandre Lacazette, sannan ta kara na biyu ta wajen Said Benrahma.
Monaco ta farke ta hannun Ben Yedder a minti na 60, amma kuma mai masaukin baki, Lyon ta kara na uku ta hannun Malick Fofana, saura minti shida a tashi karawar.
Yanzu dai kungiyar da Luis Enrique ke jan ragama za ta mayar da hankali wajen daukar Champions League na farko a tarihi.
A watan Mayu ne PSG za ta kece raini da Borussia Dortmund gida da waje a zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai ta bana.
PSG za ta rasa Kylian Mbappe da zarar an kammala kakar nan, wanda ya amince zai koma Real Madrid da taka leda.
Kafin fara kakar nan PSG ta rasa zakakuren 'yan wasanta biyu, wato Lionel Messi, wanda ya koma Amurka da Neymar, wanda yake taka leda a Saudi Arabia.