An ragargaza asibitin Al-shifa bayan samamen Isra'ila na mako biyu

Sojojin Isra'ila sun ce sun fice daga asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza bayan ragargaza asibitin a samame na mako biyu da suka yi.

Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an gano gomman gawawwaki kuma mazauna yankin sun ce an ruguza gine-gine.

Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) ta ce sojojinta sun kashe tare kuma da tsare ɗaruruwan ƴan ta'adda, kuma sun gano makamai da bayanan sirri a faɗin asibitin.

IDF ta ce ta kai samame al-Shifa ne saboda ƴan Hamas sun tattaru a can.

An gwabza kazamin faɗa a samamen na mako biyu da kuma kai hare-hare ta sama a kusa da gine-gine da yankunan da ke kewaye.

An far wa sashe-sashe na asibitin ne saboda Hamas da ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinawa na amfani da wurin a matsayin sansani, in ji IDF, inda ta zargi mayakan Hamas da faɗa cikin asibitin, saka abubuwan fashewa da kuma ƙona gine-ginen asibiti.

Wasu hotuna sun nuna yadda aka lalata wani ɓangare na yin tiyata a asibitin al-Shifa, wanda ke ɗauke da ɗakin kwantar da waɗanda cutar su ta yi tsanani, da kuma wani gini na karɓar marasa lafiya masu buƙatar gaggawa.

Gomman gawawwaki waɗansu har sun fara ruɓewa, aka gano a ciki da wajen asibitin, wanda a yanzu ya kasance ba ya aiki kwata-kwata, a cewar ma'aikatar lafiya a Gaza.

Wani likita ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sama da gawawwaki 20 ne aka gano, inda motoci suka tattake wasu daga ciki.

A ranar Lahadi, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce marasa lafiya 21 sun mutu tun bayan da aka yi al-Shifa ƙawanya. An yi ta sauyawa marasa lafiya wurin kwanciya sau da dama kuma sama da 100 ne aka kwantar a cikin wani gini ba tare da taimakon likitoci ba, in ji shi.

Wani mara lafiya mai suna Barra al-Shawish ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa abinci kaɗan kawai sojojin Isra'ila suka ba da damar a kai musu. "Babu jinya, ba magani, ba komai sai ruwan bama-bamai na sa'a 24 babu kakkautawa da kuma ragargaza a asibitin," in ji shi.

An mayar da wasu marasa lafiya zuwa asibitin al-Ahli, kamar yadda wani likita ya shaida wa Reuters.

Wata sanarwa da IDF ta fitar, ta ce dakarunta sun kammala samamen da suke yi a yankin da asibitin al-Shifa yake kuma sun janye daga wajen". Yayin samamen, mun hana a far wa fararen hula, marasa lafiya da kuma jami'an lafiya", a cewar IDF.

A ranar Lahadi da yamma, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce al-Shifa ya dawo mattara ta ƴan ta'adda kuma sama da mambobin ƙungiyoyin mayaka na Falasɗinawa 200 ne aka kashe, ciki har da manyan kwamandoji, inda wasu suka miƙa wuya.

Isra'ila ta ce an tsare wasu mutane 900 a ciki da wajen asibitin al-Shifa, inda aka gano cewa sama da 500 daga ciki sun kasance mambobin Hamas da kuma ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinawa.

Makonni biyu da suka wuce, ya ɗauki ɗaruruwan sojojin Isra'ila sa'o'i kaɗan kafin su shiga asibitin wanda ya kasance mafi girma a Zirin Gaza. Wannan ya biyo bayan samame mai cike da ce-ce-ku-ce da suka kai can a watan Nuwamba, inda aka ɗauki makonni da dama kafin tankokin yaƙi da kuma hare-hare ta sama su sauka a can.

Ga magoya bayan sojojin Isra'ila, wannan ya kasance hujja na irin nasara da suka samu a yaƙin, inda suka kaddamar da wani harin ba-zata kan abokan gaba.

A baya, wani mai magana da yawun IDF ya kwatanta samamen da cewa shi ne "ɗaya daga cikin gagarumin nasara a yaƙin kawo yanzu" saboda irin bayanan sirri da suka samu da kuma yawan waɗanda suka kashe da kuma tsarewa.

Sai dai, wasu masu sharhi sun bayyana cewa samame na biyu da aka kai asibitin al-Shifa ya ƙara nuna rauni a cikin tsare-tsaren sojojin Isra'ila a yakin. Sun kalubalanci cewa hakan ya nuna yadda Hamas da Islamic Jihad suka sake tattaruwa cikin sauki bayan da Isra'ila ta janye dakarunta daga arewacin Gaza da kuma buƙatar samar da wani tsari na bayan yaƙi na mulkar yankin.

Asibitocin Gaza sun kasance abin da aka sa gaba a yaƙin da ake yi yanzu, inda dubban Falasɗinawa ke neman mafaka daga ruwan bama-bamai da Isra'ila ke y a yankinsu da kuma yi wa asibitocin dirar mikiya da dakarun Isra'ila ke yi saboda sun ce mayakan Hamas na zaune a can.

Tun tsawon lokaci, Isra'ila ta zargi Hamas na amfani da cibiyoyin lafiya a matsayin mafaka domin kaddamar da hare-hare, abu kuma da ƙungiyar ta musanta.

A ranar Litinin, ma'aikatar lafiya a Gaza ta buƙaci taimakon ƙasashen waje domin sake komawa kula da lafiya a asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza.

Asibitin wanda ya kasance mafi girma a kudancin Gaza, ya daina aiki tun bayan da Isra'ila ta yi wa yankin dirar mikiya a watan Febrairu.

An fara yaƙin ne bayan da Hamas ta kaddamar da hari zuwa kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutum 1,200 tare kum da yin garkuwa da 253, a cewar alkaluma da Isra'ilar ta fitar.

Kusan 130 ne ake ci gaba da yin garkuwa da su, ana kuma ɗaukar cewa 34 daga ciki sun mutu.

Sama da Falasɗinawa 32,700 ne aka kashe sannan an jikkata 75,000 a Gaza tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da samamen soji, a cewar ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas. Ta ce kashi 70 na waɗanda aka kashe sun kasance mata da yara.

Yaƙin ya kuma janyo Falasɗinawa da dama na cikin barazanar fuskantar yunwa. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa Gaza na cikin bala'in faɗa wa yunwa, abin da ya janyo babbar kotun MDD bai wa Isra'ila umarnin cewa kada ta toshe hanyar kai agaji zuwa Gaza.

Sai dai zanga-zangar ƙin jinin Netanyahu ta sake fito da rarrabuwar kan siyasar Isra'ila.