Brentford na da ƙwarin-gwiwar riƙe Toney, Man City na fafatawa da Liverpool kan Sane

Brentford na da ƙwarin-gwiwar ɗan wasan Ingila mai shekara 27, Ivan Toney, da ake alakanta da tafiya Arsenal da Chelsea, zai sanya hannu a sabon kwantiragi da ƙungiyar.(Talksport)

Amma Toney, wanda kwantiragin da yake kai zai kare a 2025, na son barin ƙungiyar, kuma zai nemi a sauya yarjejeniyar duk wani sabon kwantiragin da zai cimma da Brentford. (90 Min)

Manchester City za ta fafata da Liverpool wajen sake saye ɗan wasan gaba a Bayern Munich da Jamus Leroy Sane, mai shekara 27. (Bild, via Sun)

Sir Jim Ratcliffe, wanda ke gab da saye kashi 25 cikin 100 na Manchester United, na fatan gaje matsayin Sir Alex Ferguson da zaran an kammala ciniki. (Telegraph - subscription required)

Crystal Palace da Fulham na son ɗauko aron ɗan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 27. (90min)

Wakilin ɗan wasan tsakiya a Barcelona, Ilkay Gundogan ya yi watsi da raɗe-raɗin da ke alakanta ɗan wasan mai shkara 33 da yunkurin tafiya kungiyar Galatasaray ta Turkiyya. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Arsenal ta buɗe kofar tafiya ga ɗan wasan Poland Jakub Kiwior a matsayin aro, yayinda matashin mai shekara 23 ke nuna zaƙuwar ɗanɗana wata ƙungiyar. (90min)

Chelsea na iya dawo da ɗan wasanta na tsakiya Andrey Santos daga inda yake zaman aro wato Nottingham Forest saboda kin sa matashin mai shekara 18 a wasanni. (Standard)

Ɗan wasan gefe a Newcastle United Anthony Gordon, mai shekara 22, ba shi da niyyar komawa Scotland duk da rashin haskawa a tawagar Ingila da ke neman gurbi a gasa Euro 2024. (Athletic - subscription required)

Southgate ya ce Gordon, wanda ya taimaka wa Ingila lashe kofin Turai na ajin kasa da shekara 21, na gab da shiga rukunnin manya. (Standard)

Manchester City ta amince da cinikin fam miliyan 1.2 kan ɗan wasan Leeds United mai shekara 15 Finley Gorman. (Football Insider)

Ɗan wasan Tottenham Son Heung-min, mai shekara 31, ya nuna damuwa kan raunin da ya samu a lokacin bugawa kasar sa Koriya ta Kudu. (Standard)