'Na ga motocin a-kori-kura a yankin Darfur cike da gawawwakin mutane'

Rikicin Sudan

Asalin hoton, ABDALLALATEIF ELTAYEB

Faɗa yana ci gaba da ƙamari a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, duk da tsagaita wutar da aka yi, inda Larabawa masu gwagwarmaya da makamai ke kai hari a kan manyan dakunan ajiyar kayayyaki, da kasuwanni da gidaje.

An kashe wani babban jami'in 'yan sanda kuma wani ma'aikacin agaji ɗan ƙasar Sudan ya shaida wa BBC cewa yana nan ɓoye a ƙarƙashin gado saboda tashin hankalin da ke faruwa.

“Ko ban-ɗaki ba na iya yunƙurawa na je,” abin da Abdallalateif Eltayab ya bayyana kenan ta wayar tarho daga birnin El Geneina.

Wutar rikici ta riga ta ruru inda ta haddasa zaman ɗar-ɗar na ƙabilanci, kamar yadda ya yi bayani.

Shekara da shekaru Darfur tana fama da tashin hankali tsakanin al'umominta daban-daban na Afirka da Larabawa.

A lokacin da waɗanda ba Larabawa ba suka ɗauki makamai suna faɗa da gwamnati cikin shekara ta 2003, suna ƙorafin cewa ana nuna musu wariya.

Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar ɗaukar mafiya yawa Larabawa 'yan bindiga, waɗanda aka zarga da ta'asa da cin zarafi da tursasawa.

Har zuwa zancen da muke yi da ku a yanzu, ƙungiyoyin 'yan Afirka da dama da ke yankin Darfur suna zaune a sansanonin 'yan gudun hijira don tsira da ransu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu Larabawa masu ɗauke makamai – da ke da alaƙa dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF, wato jami'an tsaro masu kayan sarki da ke artabu da sojoji – ga alamu suna amfani da giɓin tsaro da ake da shi.

“An fara gwabza faɗa ne kwana huɗu da suka wuce,” in ji Mista Eltayeb, wanda ya shekara 26 a matsayin ƙwararren ma'aikacin jin-ƙai, wanda ainihi daga Khartoum, babban birnin Sudan ya fito.

“Masu ɗauke da makaman suna ta kai hari kasuwanni, da manyan wuraren ajiyar kaya, da ofisoshi, da cibiyoyi da asibitoci, sannan a yanzu kuma suna kai wa gidaje hari, kawai ina zaman jiran su iso kaina ne.

Ana ta harbe-harbe a ƙofar gida kusa da inda ɗakin wanka yake.

A duk lokacin da nake son zuwa ban-ɗaki, sai na jira na kasa kunne tsawon minti biyar zuwa 10 domin tabbatar da harbe-harbe sun lafa, sannan na zagaya”.

An bayar da rahoton cewa an kwashe tsawon mako ana ta gwabza ƙazamin faɗa a Yammacin Darfur, inda a ranar Laraba aka harbe mataimakin daraktan 'yan sanda na jihar West Darfur, Birgediya Janar Abdel—Baqi Al-Hassan Mohamed.

Sudan Crisis
Bayanan hoto, Wani mayakin RSF da bindiga a gaban hedikwatar 'yan sanda ta jihar Yammacin Darfur

Wannan harbi ya auku ne washe garin ranar da fararen hula suka yi tururuwa zuwa ofishin 'yan sanda na jihar Darfur, inda suka ƙwace makamai.

“Larabawan masu ɗauke da makamai suna ta kai hari kan mutanen da rikici ya raba gidajensu,” kamar yadda Mista Eltayeb ya yi bayani.

Sun ƙone duk sansanonin mutanen da rikici ya raba da gidajensu.

"Daga nan mutanen da rikici ya raba da gidajensu sai suka tafi shalkwatar 'yan sanda kuma a yanzu sun ɗauki makamai.

Sun yi ƙoƙarin kare kansu a ranar Talata amma abin ya gagare su. “

Da Mista Eltayeb ya yi ƙoƙarin fita daga gidansa na ɗan wani lokaci domin ya yi cajin wayarsa saboda kwanansa biyar kenan ba su da wutar lantarki, nan ne ya ga abin ban tsoro a zahiri game da tashin hankalin.

“Na ga manyan motocin dakon kaya maƙare da gawawwakin mutane, sannan Larabawa ɗauke da makamai, suna riƙe da bindigogi suna banka mana harara.

Bayan nan ne, na koma gida ina ta amfani da ɗan ma'adanin lantarki ina cajin wayata, sai dai baturin yana ci gaba da rage ƙarfi zai mutu.

A ƙarshe zan kasance ba ni da sauran caji a baturin waya.”

Ya matsu ya fita waje

“Ni da abokan aikina mun yi magana game da yunƙurin tserewa, sai dai babu dama, ba wata dama ko kaɗan".

Sudan Crisis

Asalin hoton, ABDULLATEEF ELTAYEB

Bayanan hoto, Abin da ake hangowa kenan daga tagar ɗakin Abdallalateif Eltayeb a garin El Geneina

Ƙungiyar ba da agaji da ake kira War Child da ya tuntuɓa, ta shaida masa cewa tana aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya domin sauya matsugunnai ga ma'aikatansu 'yan ƙasar Sudan waɗanda ba daga yankin suka fito ba, kuma suke fuskantar babban ƙalubale a wurin.

"Muna yin duk mai yiwuwa domin tallafa wa ma'aikatanmu.

Sai dai yanzu a El Geneina, tashin hankali ya Ƙazance ta yadda dukkan wani yunƘuri da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yi don kwashe mutane, tamkar ɗaukar Dala ba gammo ne.” Dara Mcleod babban daraktan ƙungiyar War Child da ke Kanada, ya shaida wa BBC.

Wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan, Volker Perthes, shi ma ya ce tabbas ƙungiyoyi a Darfur, suna “amfani da wannan hali da ake ciki suna gudanar da nasu rikici”.

“Lamarin ya yi muni ne saboda waɗanda ya kamata su samar da tsaro ga jama'a na ƙasar, a Darfur da sauran yankuna, sun kasance su kansu suna da hannu dumu-dumu a faɗan,” ya shaida wa BBC

Lokacin da aka fara yaƙin Darfur shekara ashirin a baya, Larabawa masu gwagwarmaya da makamai, waɗanda gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir ta ba su makamai, su aka fi sani da Janjaweed.

Su ne suka gagari kowa inda suka kashe dubban ɗaruruwan mutane kuma suna ƙona ƙauyuka, suka washe su. An ce shi ne kisan -ƙare dangi na farko a cikin ƙarni na 21.

A cikin dakarun RSF, akwai tsofaffin mayaƙan ƙungiyar Janjaweed, kuma ana fargabar suna fama tsohon tabo ne a yankin don amfanin kansu.

Labarin cewa mutanen el-Bashir da ke da hannu a ta'asar da Janjaweed ta aikata sun tsere daga gidan yari da ke Khartoum, na iya sa halin da ake ciki ya ƙara ƙazanta.

A cikinsu akwai Ahmed Haroun, wani tsohon ministancikin gida da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) take nema saboda laifukan yaƙi da aka aikata a Darfur.

Ba Yammacin Darfur ne kawai lamarin ya shafa ba.

Ɗan jarida kuma mai sa ido kan al'amuran kare haƙƙin ɗan'adam, Ahmed Gaouja, ya ce mutanen da ke ɗauke da makamai suna ta musguna wa fararen hula da ke birnin Nyala a kudancin Sudan.

“Suna kwasar ganima, da tafka sata, da lalata dukiyar mutane da kashe-kashe,” ya shaida wa shirin BBC na Newsday.

Abin da Mista Eltayeb kawai yake so a yanzu shi ne a kawo ƙarshen faɗan don ya samu ya kuɓuta.

“Ina son ganin iyalaina a Khartoum.

Idan ba haka ba, zan je garin Port Sudan. Ina da dangi a can. Ko kan iyakar Chad da ke kusa da mu, zan je Chadi na jira a can har sai lokacin da faɗan ya lafa.

Sai na je Khartoum don na ga iyalina”

Sai dai idan ba a tsagaita wuta a Darfur ba, to ba a san ranar da zai iya ganin iyalan nasa ba.

Sudan Crisis