Abin da ya haddasa tashin farashin man zaitun a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Sifaniya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa samar da man zaitun a duniya, inda take samar da kashi 70 na man zaitun da ake amfani da shi a nahiyar Turai, sannan kuma ta samar da kashi 45 na man zaitun ɗin da duniya ke amfani da shi.
Ƙarancin samun ruwan sama a wannan lardi da sauran lardunan da ake noma zaitun ɗin a faɗin ƙasar ya taimaka matuƙa wajen rage yawan man zaitun ɗin ake samarwa a faɗin ƙasar, lamarin da ya haddasa tashin farashinsa.
A Sifaniya, farashin man zaitun ya ƙaru da kashi 70 a wannan shekarar kaɗai, bayan ƙaruwarsa a shekarar 2022.
A yanzu ana sayar da kwalbar man zaitun kusan dala 9.88 a shagunan kasuwanni

Francisco José García de Zúñiga na zagaya ɗaya daga cikin gonakinsa na bishiyar zaitun. A yanzu lokacin kakar man zaitun ne yayin da 'ya'yan suka nuna.
Ana amfani da inji wajen kaɗo 'ya'yan, yayin da ake jin ƙarar kaɗo 'ya'yan daga wuri mai nisa.
"Wannan kakar ba ta yi mana kyau ba, in dai za mu faɗi gaskiya ," in ji shi. "Mun samu matsalar fari a tsawon shekara biyu a jere, 2022 da 2023, shekarun nan biyu damina ba ta yi mana kyau ba."
Mista García de Zúñiga na da gona a Jaén, da ke zama cibiyar gonakin bishiyoyin zaitun a lardin kudanci ƙasar.
"Matuƙar aka samu raguwarsa a Sifaniya to dole hakan ya shafi duniya," in ji Mista García de Zúñiga.
"Idan abin da ake kai wa kasuwannin duniya ya yi kaɗan saboda raguwarsa a Sifaniya, bayan kuma buƙatarsa ba ta ragu a duniya ba, to dole farashinsa ya tashi, wannan ita ce ƙa'idar kasuwa"..

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamfanin Nuestra Señora del Pilar, inda ɗaruruwan manoman zaitun a yankin Jaén ke sarrafa man, shi ne babban kamfani da ke irin wannan aiki a duniya .
To sai dai a kakar da ta wuce kamfanin ya sarrafa kilo miliyan 24 na man, alƙaluma mafi ƙaranci da ya taɓa sarrafawa a tarihi.
A wannan shekara, kamfanin ya ƙiyasta cewa zai sarrafa kilo 30 zuwa 35, wanda shi ma dai bai kai yadda ya saba sarrafawa a baya ba.
Shugaban kamfanin, Cristóbal Gallego Martínez, ya ce ƙaruwar farashin man fetur, da takin zamani cikin shekaru biyu da suka wuce ya taimaka wajen tashin farashin man zaitun a ƙasar.
Sai dai ya ƙara da cewa ƙarancin ruwan sama shi ne babban abin da ya haddasa matsalar a wannan shekara.
"Muna fuskantar matsalar sauyin yanayi, inda muke samun fari a wasu lokuta, sannan mu samu mamakon ruwa sama a wasu lokuta kafin kuma mu sake fuskantar karancin ruwan a lokacin da kaka ta fuskanto,'' in ji shi.
"A yanzu haka muna cikin fari, rabonmu da ruwan sama tun lokaci mai tsawo."
Mista Gallego Martínez ya ce matsalar fari da ambaliya na neman zama wata babbar barazana ga manoman ƙasar , ya kuma ce akwai buƙatar gwamnatocin ƙasar a matakai daban-daban su ɗauki matakan magancewa ta hanyar zuba jari a noman rani.
Tashin farashin man zaitun a Sifaniya ya shafi ilarihin nahiyar Turai.
To amma a wasu ƙasashen farashin bai ƙaru sosai ba, domin kuwa a baya-bayan nan an ga yadda 'yan Sifaniya ke tsallakawa zuwa Portugal domin sayen man zaitun saboda araharsa a can.
Farashin man zaitun a Birtaniya da Ireland bai kai yadda yake a Sifaniya ba a watannin baya-bayan nan, duk kuwa da cewa daga Sifaniya suke shigo da shi.
Dalili kuwa shi ne waɗannan ƙasashe sun sayo man da a yanzu ke shagunnansu a watannin da suka gabata, lokacin da farashin bai tashi ba.
A Sifaniya, inda ake tsananin buƙatarsa, ana samun ƙaruwar buƙatarsa.
Ana sayar da kashi 65 na man zaitun ɗin Sifaniya a ƙasashen ƙetare, duk kuwa da cewa a wannan shekara adadin ya ragu matuƙa.
Haka kuma an samu raguwar sayar da shi a cikin ƙasar da kashi 10, kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna.
''Man zaitun shi ne abu mafi kyau da ɗan'adam zai ci domin kare kansa, ko magance cutar ciwon zuciya'', in ji Fernando López-Segura na asibitin Reina Sofía.
"Man da muke shawartar mutane su sha ba shi da yawa, amma yana ɗauke da amfani mai yawan gaske,'' in ji shi.
To sai dai a yanzu matsalar samun ƙarancin ruwan sama ya sa muna ƙayyade yawan man zaitun da mutane za su riƙa amfani da shi.










