'Yar Afirka ta farko da ta karaɗe nahiyar a kan babur

Ebaide ta yi amfani da intanet kuma ta dogara kan sauran matuƙa babur wajen neman inda za ta ci abinci da kuma yada zango

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Ebaide ta yi amfani da intanet kuma ta dogara kan sauran matuƙa babur wajen neman inda za ta ci abinci da kuma ya da zango
    • Marubuci, Parisa Andrea Qurban
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Udoh Ebaide Joy ta zama mace baƙar fata ta farko da ta karaɗe nahiyar Afirka ita kaɗai a kan babur.

Sai da mai shekara 32 ɗin ta shafe wata uku kafin ta kai birnin Legas a Najeriya daga Mombasa na Kenya. Tafiya ce mai nisan kilomita 9,000.

"Na so na aikata wa kaina wani abu na musamman," a Ebaide. "Saboda na san zan iya, kuma ina da son ƙalubalantar kai na, ina ƙaunar na ji ina motsi."

Ga yadda ta ba da labarinta ga shirin Africa Daily na BBC.

Abin rashin jin daɗin da ya sa ta kama hanya

 Ebaide riding her motorbike in a black track suit

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Ebaide ta shafe wata uku kafin ta kai birnin Legas a Najeriya daga Mombasa na Kenya a tafiyar mai nisan kilomita 9,000

Matar da aka haifa a Najeriya ta samu ƙarin gwiwar yin balaguron ne saboda wani lamari maras daɗi da ya faru da ita kusan shekara 10 da suka wuce.

Wani hatsarin mota ya taɓa ritsawa da ita tana 'yar shekara 23, wanda kuma ya shafi ƙashin gadon bayanta. Ta shafe watanni tana amfani da keken guragu bayan haka.

"Haka ya sa na fara tunain sai na ji daɗin rayuwata iya ƙarfina," kamar yadda ta yi bayani. "Ina ganin kuma jin daɗi a wajena shi ne yin tafiye-tafiye."

Sai da aka yi wa Ebaide tiyata kafin ta fara warkewa. Tana fitowa daga asibiti ta ci alwashin more rayuwarta.

"Ba ni son maimaita ƙaramin abu kullum," in ji ta. "Ina son abu na musamman, wani abu na ƙashin kaina."

A farkon shekarar nan ne Ebaide ta sayo babur mai ƙarfin 250CC wanda ta saka masa suna Rory, inda ta tafi Nairobi don koyon yadda ake tuƙa shi.

Karaɗe Afirka

Wuraren da Ebaide ta je a Afirka
Bayanan hoto, Wuraren da Ebaide ta je a Afirka

A ranar 8 ga watan Maris, Ebaide ta kama hanya zuwa ta Kenya, zuwa ƙasashne Uganda, Rwanda, Tanzania, Zambia, Angola, Kongo, Kamaru, da kuma Najeriya.

"Na zaune a ƙauyuka, da garuruwa, da birane don ganin wurare," kamar yadda ta ce.

"Ba kullum nake tuƙa babur ɗina ba. Duk ranar da na hau kuma sai na yi aƙalla kilomita 300."

Ta ji harsuna, ta ga al'adu, ta shaida wurare iri-iri.

Ebaide ta ce balaguro tsakanin ƙasashen Afirka ne babban abin da ta fi jin daɗi a rayuwarta

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Ebaide ta ce balaguro tsakanin ƙasashen Afirka ne babban abin da ta fi jin daɗi a rayuwarta

Ta ci ɗaya daga cikin abincin da ba za ta taɓa mantawa da shi ba a Uganda.

"Wani matsuguni ne a tsakiyar daji, kamar wurin cin abinci. Sun ji daɗin ganin mace a kan babur kuma yadda nake magana da harshen Swahili ya burge su."

Amma ta gamu da tutsun hanya a wani sashen daban.

"A birnin Kampala, titunan ba su da tsari, kuma matsattsu ne."

Takan tuna Kenya saboda abotar mutanenta, Rwanda kuma saboda duwatsu da kuma yawan shan kwana da sauya hanya da ta dinga yi a tsakiyar duwatsun.

Sau ɗaya ta taɓa yin faci yayin balaguron nata

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Sau ɗaya ta taɓa yin faci yayin balaguron nata

Matuƙiya ita kaɗai

Duk da irin bambancin hanyoyin, Ebaide ta ce ba ta taɓa samu wata matsala da babur ɗin nata ba. "Ina matuƙar son sa."

Ta ga abubuwan al'adu masu a kan hanyarta, da na ƙayatarwa har ma makwarar ruwa ta Victoria Falls da ke Kogin Zambezi ta ba ta sha'awa sosai.

Babur ɗin Ebaide bai ba ta matsala ba a duka tafiyar da ta yi

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Babur ɗin Ebaide bai ba ta matsala ba a duka tafiyar da ta yi

Ta yi ɓatan hanya a wasu lokutan tana mai cewa tafiya a cikin daji na rikitarwa da gajiyarwa.

"Tafiya kai kaɗai a kan hanyoyin nan ba tare da kana jin harshensu ba abu ne mai tsoratarwa."

"Kodayaushe a firgice nake. Sai na yi ta rage gudu idan na zo shan kwana saboda ban san abin da zan gani a gaba ba. Zan iya ganin maciji, ko wata dabba daji a kan hanya. Wannan abin tsoro ne ƙwarai."

Da farko ta ɗauki tanti amma kuma ta watsar da tunanin yin hakan a gefen titi.

"Ban taɓa kafa tanti a kan hanya ba saboda abu ne mai hadari a Afirka. A otel na yi ta zama tun daga Kampala har na zo Najeriya."

Ebaide ta ji daɗi haɗuwa da mutane masu yawa da kuma ganin wurare daban-daban

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Ebaide ta ji daɗi haɗuwa da mutane masu yawa da kuma ganin wurare daban-daban

"Akasari nakan tafi ne da tufafina, da kwamfuta, da 'yan wasu kayayyaki."

Ebaide ta kuma nemi wasu matuƙa baburan a ƙasashe da dama waɗanda suka taimaka mata - abin da ta hakan ya ƙara daɗaɗa tafiyar tata.

Ta yi amfani da manhajojin balaguro da kuma intanet wajen bin hanyoyi da kuma neman inda za ta ci abinci da yada zango.

Wurin zuwa na gaba

Tuni Ebaide ta fara tsara balaguro zuwa Morocco

Asalin hoton, Udoh Ebaide Joy

Bayanan hoto, Tuni Ebaide ta fara tsara balaguro zuwa Morocco

Ebaide ta haƙiƙance cewa ba ta haɗu wani cikas ba. "Mutane na mamakin ganin mace a kan babur ɗinta," in ji ta.

Ebaide ta dinga bayyana yadda balaguron nata ke wakana a shafukanta na sada zumunta, inda mutane da yawa da ba ma a Afirkan suke ba suka dinga yin tafiyar tare da ita.

"Lokacin da na isa Legas, ban iya tare hawayena ba. Mutane na ta murna. Na kasa ɓoye farin cikina."

Dogon balaguron ya sauya tunanin Ebaide: "Na ji daɗin da ban taɓa ji ba a rayuwata yayin wannan balaguron."

"Tafiyar ta tuna min cewa nijajirtacciya ce kuma mai naci da za ta iya shawo kan duk wani ƙalubale da rayuwa ta zo da su."

Sai dai ba ta da wani shirin hutawa.

"Balagurona na gaba shi ne daga Najeriya zuwa Morocco. Ina so na kama hanya ranar 29 ga watan Agusta."