Yadda Fadar Vatican ke sirranta zaɓen sabon Fafaroma

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan lallai shi ne zaɓe mafi sirri a duniya.

Yayin da aka killace manya-manyan limaman ɗariƙar Katolika a zauren ibada na Sistine ranar laraba don zaɓo mutumin da zai gaji Fafaroma Francis, kowannensu sai ya rantse da Baibul Mai Tsarki cewa zai sirranta duk abin da ya faru a nan har tsawon ransa.

Haka ma duk wani mutum da ke cikin Fadar Vatican a yayin zaman Majalisar manyan limaman (conclave) kama daga likitoci guda biyu da ke nan domin duk wani batun lafiya na gaggawa har zuwa ga jami'an kula da abincin masu zaɓen. Duk sai sun yi rantsuwar "kiyaye cikakken sirri kuma har abada".

Don ma a daɗa tabbatarwa, sai an share sarai - zauren ibadar da kuma masaukan baƙi guda biyu saboda a gano ko wasu sun maƙala 'yan ƙananan lasifikokin naɗar sauti.

"Akwai na'urorin rikita layukan sadarwa don tabbatar da cewa ba a yi amfani da wayoyin hannu da hanyoyin sadarwar intanet wajen aika saƙo ba," a cewar John Allen, editan jaridar intanet ta Crux.

"Fadar Vatican na ɗaukar batun keɓe manyan limaman Katolikan da matuƙar muhimmancin gaske."

Kullewa gaba ɗaya

Mashahurin kullen da ake faɗa ba kawai ana yi ba ne domin sirranta hanyar zaɓen ita kanta: hana "wasu miyagu" yin yunƙurin kutsen intanet don samun bayanai ko kuma kawo hargitsi.

Matakan kuma na ƙoƙarin tabbatar da ganin limaman cocin sanye da jajayen tufafi sun keɓance kansu gaba ɗaya daga wannan duniyar mai dauɗa da kuma tasirinta yayin da suka shirya kaɗa ƙuri'a.

Mabiyan Katolika za su faɗa muku cewa zaɓe ne da Ubangiji ke yi wa ilhama, babu siyasa a ciki. Amma Vatican ba ta barin wata kafa.

Da zarar an shiga majalisar zaɓen fafaroman, wajibi ne kowa ya ajiye duk na'urorinsa ciki har da wayoyin salula da tabulet da agogon kwamfuta-huta. Fadar Vatican na da 'yan sandanta na kanta da ke tilasta aiki da doka.

"Azancin hakan shi ne a tsare amana kuma a tantance," a cewar John Allen.

"Babu talbijin babu jarida ko rediyo a masaukin baƙin -- babu komai," in ji Monsignor Paolo de Nicolo, wanda ya shafe tsawon shekara 30 yana jagorantar harkokin gidan Fafaroma.

"Ko taga ba a yarda a buɗe ba, saboda ɗakuna da yawa suna tagogin dake shigo da iskar duniyar waje."

Duk wanda ke aiki a cikin Fadar Vatican mai dogayen ganuwa domin zaɓen sabon fafaroma, sai an tantance sosai da gaske. Duk da haka, an hana su yin magana da masu zaɓen.

"Manyan limaman Katolikan kwata-kwata ba sa cewa uffan," in ji Ines San Martin ta Cibiyar Addu'o'in Pontifical Mission Societies da ke Amurka.

"Akwai dai oba-oba kawai don wasu taƙamaiman al'amura kamar, 'muna buƙatar likita a nan,' da kuma 'Tubarkalla, an zaɓi sabon Fafaroma, ko wani zai sanar da masu buga ƙararrawa a cikin Majami'a.'"

To, me zai faru idan wani ya karya doka?

"Akwai rantsuwa, kuma duk wanda bai kiyaye rantsuwar ba zai iya fuskantar kasadar kora," Monsignor De Nicolo ya ce, hakan na nufin a raba shi da cocin. "Ba wanda ya isa ya yi haka."

Farautar manyan limaman Katolika

Wani batu ne daban idan ana shirye-shiryen shiga majalisar zaɓen.

A ƙa'idance, an haramta wa manyan limaman yin furuci ko a wannan lokacin ma. Da zarar an binne Fafaroma Francis, jaridun Italiya da masu ziyara da dama sukan koma masu farautar manyan limaman Katolika, a ƙoƙarinsu na fahimtar wane ne mai yiwuwa zai zama sabon Fafaroma.

Suna cika gidajen abincin da 'yan yawon shaƙatawa ke cika da rumfunan askirin a zagayen Vatican, da shirin yin hasashe a kan duk wani abu da suka gani da kuma yiwuwar wani ƙawance.

'Yan jarida kan tsare masu kawo abinci da zance a kan abin da mai yiwuwa suka yi tsegumin ji.

Ƙarin wani babban wuri da ake hango manyan limaman shi ne bayan majami'ar St Peter ita kanta. Duk safiya, ana samun 'yan jarida da kyamarori suna dube-dube.

Manyan limamai kusan 250 ne yanzu a birnin, waɗanda aka kira su daga faɗin duniya, ko da yake waɗanda suka kai shekara 80 ko fiye ba su cancanci zaɓe ba.

Yayin da suka nufi Vatican don tarukan ibadarsu na kullum da kuma tattauna batun zaɓen, akan zagaye kowannensu ana yi masa ruwan tambayoyi game da halin da ake ciki.

Ba su cika magana ba face dai "buƙatar a samu haɗin kai" ko kuma tabbacin cewa zaman majalisar zaɓen ba zai daɗe ba.

Can waje uwa-duniya

"Gaba ɗaya hikimar hakan ita ce zaɓen ya kasance sha'anin addini tsantsa ba na siyasa ba," kamar yadda Ines San Martin ya bayyana. "Muna cewa Ruhi Mai Tsarki ya yi mana jagora kan magana da zaɓenmu."

Sai dai Fafaroma na shugabantar wata gawurtacciyar cibiya mai ɗumbin arziƙi da gagarumin ikon ya kamata, sannan ga kwarjininsa a duniya kan kowanne al'amari. Kama daga warware rikice-rikice da kuma sha'anin alaƙar jinsin namiji da mace.

Don haka mutumin da aka zaɓa – tsinkayensa da abubuwan da yake bai wa fifiko – na da tasiri ba kawai a cikin Fadar Batikan ba.

A lokaci guda, wani littafi mai ɗaukar hankali da ke fito da wasu limamai waɗanda mai yiwuwa 'yan takara ne yana ta karaɗe gari, inda yake kwarzanta wasu masu ra'ayin riƙau kamar Babban Limamin Katolika Robert Sarah na Guinea saboda yadda yake yin alla-wadai da "shaiɗancin zamani" na zubar da ciki, da kuma "aƙidar auren jinsi".

"Akwai rukunin wasu mutane a gari da ke ƙoƙarin kambama batutuwan da suke da muradi a kai," in ji John Allen. "Manyan limaman na sane da irin wannan abu, suna karanta jaridu. Amma za su yi duk abin da za su iya don tokare hakan."

"Shin akwai ƙoƙarin kamun ƙafa? E, kamar dai a kowanne zaɓe," Ines San Martin ta ce. "Sai dai ba ya amon da nake jin ya kamata a ce yana yi."

Ta ce a wani ɓangare saboda Fafaroma Francis ya naɗa sabbin manyan limamai da yawa a cikinsu har da wasu daga sabbin wurare.

"Kashi hamsin zuwa sittin ɗinsu ba su ma san juna ba.

Rufe bakunan duk wasu masu surutu

Zuwa safiyar Laraba, duk masu zaɓen suna shiga cikin Fadar Batikan – an raba su da wayoyinsu na salula, an katse su daga sha'anin sauran al'ummar duniya.

Daga sannan kuma kamar yadda John Allen ya yi imani hangen mutum shi ne gaba da siyasa, mai sassaucin ra'ayi ne ko mai ra'ayin riƙau ko "mai kwakwazo ne ko mai yin guna-guni game da batutuwan da al'umma ke muhawara ne".