Manchester United na zawarcin Kane, Mainoo na son ya bar Old Trafford

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda zai iya barin Bayern Munich a bazara mai zuwa.(Star), external

Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce Kane, wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din, 'za su karbe shi da hannu biyu'' idan ya dawo , amma ba ya tsammanin dan wasan zai bar kungiyarsa ta Jamus a yanzu.(Sky Sports), external

Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, ya soma shirin barin Manchester United a watan Janairu domin neman wata kungiyar kwallon kafa .Ya samu wata kungiya da ta nemi a ba ta shi aro sai dai Man U ta yi watsi da tayin a bazara . (Mirror), external

Bayern Munich na tunanin sabunta kwantiragin dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 23, bayan an alakanta shi da komawa Liverpool.(Liverpool Echo), external

Arsenal ta tuntubi dan wasan Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, amma Juventus, wacce ta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi masa a lokacin bazara, ta kimanta shi kan Yuro miliyan 80 zuwa 100 . (Tutto Juve via Goal, external)

Chelsea na sha'awar dan wasan bayan Faransa Ismael Doukoure, mai shekara 22, wanda a halin yanzu yana kungiyar Strasbourg mallakar BlueCo, a dai dai lokacin da wasu kungiyoyin firimiya da dama ke zawarcinsa.(TBR Football), external

Aston Villa na son dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 ya cigaba da taka mata leda na din din, Man U ce ta bada aron dan wasan ga Aston Villa. (National World)