Waɗanne kaya ne Najeriya ta haramta wa Amurka shiga da su ƙasar?

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, State House NG, White House

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu da shugaban Amurka Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 4

Ofishin kula da harkokin kasuwanci na Amurka ya bayyana damuwa kan matakin wasu ƙasashen Afirka na ƙaƙaba shingen kasuwani da Amurka, bayan jerin matakan da ƙasar ta Amurka ta ɗauka a ɓangareen kasuwanci da ƙasashen duniya.

Amurkar ta kira waɗannan matakan da ƙasashen suka ɗauka a matsayin 'rashin adalci'.

Ofishin kula da kasuwancin ya ambato matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na haramta wa ƴan kasuwar Amurka shigar da kaya guda 25 zuwa cikin ƙasar, inda ya ce lamarin zai haifar wa wasu kamfanonin Amurka tafka hasara.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

"Waɗannan manufofi sun kawo cikas ga harkokin kasuwanci wanda ya haifarda asarar kuɗaɗen shiga ga kamfanonin Amurka da ke son faɗaɗa harkokinsu a Najeriya," in ji sanarwar wadda ofishin kasuwancin na Amurka ya wallafa a shafin X.

Wannan bayani na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauki matakin lafta haraji kan kayan da ake shiga da ƙasar daga ƙasashen duniya.

Wannan lamarin ya shafi ƙasashe 70 na duniya, wani abu da ya haddasa ɓarkewar rikicin kasuwanci tsakanin Amurkar da ƙasashe da dama, musamman manyan ƙasashen da take hulɗar kasuwanci da su, kamar China da kuma ƙasashen Tarayyar Turai.

Tuni China ta ƙara harajin da take karɓa kan kayan Amurka da ake shiga da su ƙasar zuwa 84 cikin ɗari, bayan da Trump ɗin ya ƙara haraji kan kayan ƙasar China zuwa kashi 104 cikin ɗari.

Su ma ƙasashen Tarayyar Turai sun lafta harajin kashi 25 cikin ɗari kan kayan da Amurka da ake shiga da su yankin.

Kayan da Najeriya ta haramta shiga da su ƙasarta

Sanarwar da Amurkar ta fitar ta ce abubuwan da Najeriya ta haramta shiga da su cikin ƙasar tata sun haɗa da kayan gona da magunguna da ababen sha, waɗanda suka haɗa da nama da tsuntsaye da kuma kayan sha masu alaƙa da maye.

A shekarar 2025 ne gwamnatin Najeriya ta fito da wani shiri inda ta umarci babban bankin ƙasar da ya daina bayar da canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a kan wasu kayayyaki guda 25 da ake shiga da su daga waje.

Gwamnatin ta ce ta ɓullo da shirin ne domin bunƙasa kamfanonin cikin gida. Kayan da gwamnatin ta ɗauki wannan mataki a kansu su ne:

  • Tsuntsaye masu rai ko waɗanda aka yanka, har da yankakkun kaji
  • Naman alade da naman shanu
  • Ƙwan tsuntsaye
  • Man girki
  • Sukari
  • Cocoa Butter
  • Taliyar Spaghetti ko taliyar yara
  • Tumatur ɗanye ko na gwangwani
  • Abubuwan sha na kwali waɗanda aka haɗa da ƴaƴan itace
  • Niƙaƙƙen tumatur na cin abinci (Ketchup)
  • Ruwan kwalba, mai zaƙi ko maras zaƙi da kayan sha na gwangwani
  • Simintin da aka sarrafa
  • Wasu magunguna
  • Magungunan da suka lalace
  • Takin zamani (NPK 15-15-15)
  • Sabulu da garin sabulu na wanki
  • Maganin sauro (Igiyar leko)
  • Tayoyin ababen hawa da aka yi amfani da su
  • Takardar haɗa kwali ko takardar goge bahaya
  • Kafet da darduma
  • Takalma da Jakkuna da akwati
  • Kwalaben da suka zarce girman 150mls
  • Na'urar sanyaya ɗaki da aka taɓa amfani da su
  • Motocin hawa da suka zarce shekara 12 da ƙerawa
  • Alƙalamin rubutu

Baya ga Najeriya, Angola, wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi sayen kaji daga Amurka, a baya-bayan nan ta bayyana cewa za ta taƙaita yadda ake shigar da naman alade da kaji zuwa cikin ƙasar daga watan Yulin wannan shekara.

Ofishin kula da harkar kasuwanci na Amurkan ya koka kan hakan inda ya ce lamarin zai shafi masu kiwon kaji a ƙasar.

Haka nan ma bayanin ya ambato sharuɗɗan da Algeria ta gindaya kan shigar da kayan kiwon lafiya cikin ƙasarta da kuma matakin Kenya na lafta harajin kashi 50% a kan masrar da ake shiga da ita ƙasar daga Amurka.

Yadda harajin Donald Trump zai shafi ƙasashen Afirka

Amurka ta lafta wa kusan rabin ƙasashen Afirka harajin kashi 10 cikin ɗari, sai dai wasu, kamar Najeriya da Afirka ta Kudu za su fuskanci harajin da ya fi haka, inda aka lafta wa Najeriya harajhin kashi 14%, Afirka ta kudu kuma kashi 30%.

Duk da dai cewa a yanzu shugaban na Amurka ya dakatar da aiwatar da tsarin sannan ya ce za a rage.

Ƙasar Afirka da Amurka ta fi lafta wa kayanta haraji ita ce Lesotho, mai kashi 50%, sai kuma Madagascar mai kashi 47%.

Yayin da Najeriya ta fitar da kayan da kuɗinsu ya kai dala biliyan 3.5 zuwa Amurka a 2022, wanda mafi yawa ɗanyen man fetur ne, wannan kashi 5% ne kacal na kayan da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Saboda haka nan tasirin harajin da Amurka ta lafta kan kayan kowace ƙasa ya danganta ne ga yawan kayan da take fitarwa zuwa Amurkar.