Waiwaye: Hare-haren jihar Filato da fargabar dawowar Boko Haram

Filato

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

An shiga makon ne da batun wasu hare-hare da wasu mahara suka kai, inda suka kashe mutum 52 da tarwatsa wasu 2,000 a jihar Filato ta arewacin Najeriya, kamar yadda hukumar kai agajin gaggawa ta Najeriya ta tabbatar.

Babu masaniya game da dalilan kai hare-haren a ƙauyuka shida na ƙaramar hukumar Bokkos, waɗanda su ne mafi muni tun bayan rikicin da ya ɓarke a yankin a watan Disamban 2023, lokacin da aka kashe sama da mutum 100.

Harin na baya-bayan nan ya fito fili ne a cikin ƙarshen mako, lokacin da aka kai mutanen da suka jikkata asibiti, kuma tuni shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin zaƙulowa da kuma hukunta waɗanda suka kai harin.

Fargabar dawowar Boko Haram

BH

Asalin hoton, Getty Images

A makon ne kuma Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda jihar ke rasa wasu yankunanta sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram a baya-bayan nan.

Zulum ya bayyana haka ne ranar Talata a wani taro kan harkar tsaro da ya kira domin tattauna batun.

A makonnin baya ne wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar ta Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar - a hari da suka kai Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala.

Gaskiyar batun cire shugaban INEC, Mahmood Yakubu

INEC

Asalin hoton, Getty Images

Haka kuma a ranar Litinin ɗin makon ne aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya cire shugaban hukumar zaɓen ƙasar INEC, Mahmood Yakubu daga mukaminsa.

Labarin ya yi ta ƙewayawa a shafukan sada zumunta da ke faɗin ƙasar duk da cewa shugaban baya cikin ƙasar a halin yanzu, inda aka yi tattauna batun - mutane suka yi ta tofa albarkacin bakunansu.

Amma, mece ce gaskiyar labarin na tsige shugaban na INEC?

Me masu zanga-zangar Take It Back Movement ke buƙata?

TIB

Asalin hoton, @TIBmovement

A makon ne kuma wasu matasa a ƙarƙashin ƙungiyar Take It Back Movement suka gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Cikin jihohin da aka gudanar da zanga-zangar akwai jihohin Legas da Oyo da kuma Rivers.

Omoyele Sowore - wanda shi ne ɗantakarar jam'iyyar AAC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 - shi ne shugaban ƙungiyar Take it Back wanda ya jagoranci zanga-zangar.

Matasan sun fito zanga-zangar ne duk da shawarar da rundunar ƴansanda ta ba su cewa su dakatar da yunƙurinsu., wani abin da ya sa su yin arangama da ƴansanda.

Ƴanbindiga sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina

Umar Dikko Radda

Asalin hoton, Umar Dikko Radda

Haka ma a makon ne yankin ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi Mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara.

Maharan sun kuma kashe akalla mutum 6, inda suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume ta jihar.

Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita bah ar zuwa ranar Lahadi da rana.

Malam Ya'u Ciɓauna mazaunin garin Layin Garaa ne na ƙaramar hukumar Funtua, kuma ya ce ''Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴanmata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53''

Shekara ɗaya da rasuwar Saratu Daso

Daso

Asalin hoton, Daso Instagram

A ranar Laraba ta makon ne fitacciyar jarumar Kannywood marigayiya Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso take cika shekara ɗaya cur da rasuwa.

A ranar Talata, 9 ga watan Afrilun 2024, ana tsaka da shirye-shiryen ƙaramar Sallah ta rasu.

Jarumar ta yi rasuwa ce ta fuju'a, domin an kwanta da ita lafiya ƙalau, amma aka wayi gari ba tare da ita ba.

Daso jaruma ce mai taka rawa daban-daban a masana'antar fim ta Kannywood, inda ta ƙware taka rawar rigima da rashin haƙuri, da kuma rawar barkwanci a wasu lokutan.

Haramta waƙar 'Tell Your Papa' ta Eedris Abdulkareem.

Eadris

Asalin hoton, abdulkareemeedris/Instagram

Haka kuma a ƙarshen makon ne gwamnatin Najeriya ta haramta yaɗa waƙar 'Tell Your Papa' ta fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya, Eedris Abdulkareem.

A waƙar, mawaƙin ya yi kira ne ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu da ya faɗa wa mahaifinsa cewa, "mutane suna mutuwa" saboda ƙuncin rayuwa da rashin tsaro, sannan ya ƙara da cewa, "akwai yunwa" a ƙasar.

A wata wasiƙa da hukumar kula da kafofin labarai ta Najeriya wato NBC ta fitar, ta buƙaci kafofin yaɗa labarai na ƙasar da su guji saka waƙar domin a cewarta, ta saɓa da dokokin yaɗa labarai na Najeriya.

NBC ta ce lafuzzan da aka yi amfani da su a waƙar ta Tell Your Papa "ba su dace ba", sannan ta ƙara da cewa waƙar ta saɓa da tarbiyyar ƙasar.