Tottenham na shirin dawo da Kane, Chelsea da Man city na Hamayya kan Anderson

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham na shirin yin wani gagarumin yunƙuri na maido da Harry Kane arewacin Landan daga Bayern Munich a bazara mai zuwa kuma a shirye ta ke ta biya buƙatun albashin kyaftin ɗin na Ingila (TeamTalk)
Manchester City na shirin gabatar da tayin fam miliyan 75 kan ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest Elliot Anderson a bazara mai zuwa amma akwai yiwuwar ta fuskanci hamayya daga Chelsea kan ɗan wasan na Ingila mai shekara 22. (Express)
Crystal Palace ba ta tayar da hankalinta kan makomar Adam Wharton ba, a yayin da ake ta raɗe-raɗin cewa Manchester United na zawarcin ɗan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 21. (Sky Sports)
Manchester United na sha'awar siyan ɗan wasan gaba a bazara kuma ta fara zawarcin Mateo Retegui, inda Ruben Amorim ke shirin kashe kusan fam miliyan 52 don siyan ɗan wasan gaban na Italiya mai shekara 26 daga ƙungiyar Al-Qadsiah ta gasar Saudi Pro League. (Fichajes)
Ɗan wasan gaba na ƙasar Turkiyya Kenan Yildiz na ci gaba da ƙoƙarin ganin an inganta kwantiraginsa a Juventus amma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya a tattaunawar ba, yayin da ƙungiyoyin da suka haɗa da Chelsea da Arsenal da kuma Barcelona ke sa ido sosai kan ɗan wasan mai shekara 20. (Gazzetta dello Sport)
Paris St-Germain na tattaunawa kan sabon kwantiragi da Bradley Barcola, mai shekara 23, bayan da ɗan wasan gaban na Faransa ya ja hankalin ƙungiyoyi da dama ciki har da Liverpool da Bayern Munich a bazarar da ta gabata. (L'Equipe)
Barcelona da Real Madrid na shirin fafatawa don siyan ɗan wasan baya na Bayern Munich Dayot Upamecano, mai shekara 26, a bazara mai zuwa kan cinikin kyauta duk da cewa Manchester United na zawarcin ɗan wasan na Faransa. (Footmercato)
AS Roma ta kasancekan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke rububin ɗan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee amma ana ganin Como ma na da kuɗin da za ta iya dawo da ɗan wasan na Netherlands mai shekara 24 zuwa gasar Serie A. (Gazzetta dello Sport)
Juventus ta yi watsi da tayi da dama cikin watanni shida da suka gabata kan ɗan wasan Faransa Khephren Thuram, mai shekara 24, musamman daga ƙungiyoyin Premier da suka haɗa da Arsenal da Chelsea da Liverpool. (TBR Football)
Kocin Chelsea Enzo Maresca yana da shakku kan makomarsa na dogon zango a Stamford Bridge a yayin da Juventus ke nazari kan da ɗan Italiyan mai shekara 45 a matsayin wanda zai iya kaɓar ragamar ƙungiyar ta gasar Serie A. (TeamTalk)










