Yadda mutuwar sojojin Rasha ke ƙaruwa a yaƙin Ukraine

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Olga Ivshina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian
- Lokacin karatu: Minti 4
A cikin kimanin wata goma da suka gabata, Rasha ta takfa asara sosai a yaƙinta da Ukraine, asarar da ke ƙaruwa sama da abin da mutane suke tunani, kamar yadda binciken BBC ya gano.
Yanzu da aka ƙara ƙaimi wajen tabbatar da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Amurka ke jagoranta, an samu ƙarin kusan kashi 40 na mutuwar sojoji da aka fitar idan aka kwatanta da na bara.
Jimilla, BBC ta tabbatar da kashe kusan mutum 160,000 da aka kashe a yaƙin Ukraine.
BBC ta daɗe tana bibiya tare da ƙididdige irin mutuwa da asarar da Rasha ke yi tare da amfani da alƙaluman Mediazona mai zaman kanta da wasu ƴan sa-kai tun daga watan Fabrailun 2022.
Mun daddale sunayen waɗanda suka rasu ta hanyar amfani da rahotanni da jaridu da kafofin sadarwa da tarukan jaje.
Amma ana tunanin adadin waɗanda suka rasu ɗin sun haura haka, sannan masana harkokin soji da muka zanta da su sun bayyana mana cewa alƙalumanmu ba su wuce kashi 45 zuwa kashi 65 na asalin alƙaluman.
Wannan ya sa ake hasashen asalin sojojin Rasha da suka mutu a tsakanin 243,000 zuwa 352,000.
A farkon 2025, labaran mutuwa sun ragu sosai a watan Janairu, idan aka kwatanta da watannin baya. Sai adadin ya fara ƙaruwa a watan Fabrailu lokacin da Trump da Putin suka yi magana a karon farko kan kawo ƙarshen yaƙin.
Watan da lamarin ya fi ƙamari shi ne watan Agusta, inda shugabannin biyu suka sake haɗuwa a Alaska, lamarin da ya ɗaga darajar Putin a harkar diflomasiyya bayan daɗewa yana lamɓo.
Zai yi wahalar gaske a iya tantance irin asarar da Rasha ta yi ta hanyar amfani da hanya ɗaya kacal, amma Kremlin na ganin faɗaɗa bakin iyakarta a matsayin wata hanyar neman cikar burinta wajen shiga yarjejeniyar da Amurka.

Mukashev ya kasance ɗan gwagwarmaya wanda bai taɓa goyon bayan tsare-tsaren Putin ba.
Ya shiga zanga-zanga da dama a kan adawa da ƴansanda da goyon bayan ƙungiyoyin auren jinsi da na neman a fito a Alexei Navalny.
Ya daɗe yana fitowa yana sukar yaƙin Rasha a Ukraine a kafofin sadarwa. A shekarar 2024 ne aka kama shi, sannan aka tsare shi a Moscow, inda aka tuhume shi da safarar miyagun ƙwayoyi.
Yana tsare ne sai aka tallata masa kwantiragin shiga aikin soja domin sauƙin hukuncinsa, kamar ƴanuwa da abokansa suka bayyana.
A wata doka da aka yi a 2024, an tsara ba waɗanda ake tuhuma damar samun sauƙi idan suka shiga soja.
Mukashev sai ya ƙi amincewa da tayin, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari.

Asalin hoton, Murat Mukashev
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yake zaune a gidan yari ne a watan Nuwamban 2024 ya canja shawara. Abokansa sun ce alƙawarin da Trump ya yi na kawo ƙarshen yaƙin ne ya ƙarfafa masa gwiwa, inda ya yi sauri ya amince kafin a shiga yarjejeniyar tsagaita wuta.
"Ya yi tunanin hakan zai fi masa sauƙi wajen samun ƴanci maimakon zaman shekara 10 a ɗaure."
A ranar 11 ga Yunin 2025 ne Mukashev ya mutu a fagen daga a yankin Kharkiv na arewa maso gabashin Ukraine.
Bayan shi, yawancin ƴan Rasha da suka rasu a fagen daga a 2025 ba su da wata alaƙa da aikin soja kafin a ƙaddamar da yaƙin na Ukraine, kamar yadda alƙaluman da BBC ta tattara suka nuna.
Yawanci ƴan sa-kai ne da suka shiga kwantiragin, inda yanzu haka suka fi yawa a cikin kuratan sojojin Rasha.
A bara, kashi 15 na sojojin Rasha da suka mutu ƴan sa-kai ne, amma a shekarar 2025, duk mutum ɗaya da ya rasu a cikin uku, ɗan sa-kai ne.
Hukumomi a matakin farko a ƙasar ne suka neman mutanen da za su shiga aikin soja, inda suke tallata aikin a jami'o'i da kwalejoji, da kuma neman waɗanda bashi ya musu yawa.
Zuwa watan Oktoba, aƙalla mutum 336,000 ne suka amince da shiga aikin a bana kamar yadda mataimakin shugaban hukumar tsaro ta ƙasar Dmitry Medvedev ya nuna, wanda ya nuna sama da kimanin 30,000 a duk wata.
Sakatare-jana na Nato, Mark Rutte ya ce ana kashe aƙalla sojojin Rasha 25,000 a duk wata. Idan alƙaluman nan sun tabbata, ke nan Rasha na ɗaukar sojoji sama da waɗanda ake kashe mata.
Wasu daga cikin ƴan sa-kan sun yi kuskuren fahimtar yarjejeniyar, inda suke tunanin komawa gida su ci gaba da rayuwarsu da kuɗaɗen da suka samo.
Sabon sojan sa-kai na iya samun roubles miliyan 10, kimanin dala 128,000 kimanin fam 95,000 a shekara.

Asalin hoton, ANDREY BORODULIN/AFP via Getty Images
A cewar Nato, jimillar waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata a yaƙin daga ɓangaren Rasha sun kai miliyan 1.1.
Wannan alƙaluman sun kusa daidai da lissafin BBC, duk da cewa alƙalumanmu ba su haɗa da waɗanda suka mutu a hargitsin ƴan aware da aka yi a gabashin Ukraine ba, inda ake hasashen aƙalla mutum 21,000 zuwa 23,000 ne suka mutu.
Sai dai ita ma Ukraine ta yi asarar sojoji da sauran asara a yaƙin.
A watan Fabrailun da ya gabata, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce waɗanda suka mutu a fagen daga sun kai 46,000, sannan aƙalla 380,000 suka jikkata.
Sannan kuma akwai dubbai da suka ɓace, ko kuma aka kama su suke tsare, in ji shi.
A tamu ƙididdigar, muna tunanin sojojin Ukraine da aka kashe sun kai 140,000.











