'Ban ga amfanin ci gaba da zama da nono a jikina ba'

Asalin hoton, Lisca
- Marubuci, Abdou Aziz Diédhiou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- Marubuci, Alassane Dia
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A farkon watan Oktoba ne Fatima Guéunoune ta yi wata tattaunawa da kafafen yaɗa labarai.
Ta shiga wani gangamin yaƙi da cutar sankarar mama da ake kira "Pink October", domin wayar da kan jama'a game da cutar. Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci a gareta, da kuma ga waɗanda ke fama da cutar, wadda ke yin illa ga mata da dama.
A bana, gangamin wayar da kan jama'a kan cutar sankarar mama na Pink October yana da muhimmanci na musamman ga Fatma Guénoune, wadda likita ce mai shekaru sama da sittin da ta shafe shekaru da dama tana fafutukar yaƙi da cutar sankarar mama a Senegal.

Asalin hoton, Lisca
Sai dai watanni kaɗan da suka gabata, bayan wani gwajin lafiya da ta yi, ita kanta ta gano tana ɗauke da cutar.
"Na gano ƙarin ne ta hanyar duba kaina da na yi wa kaina, inda na shafa nonona," in ji Dakta Fatma.
"Da na laluba nonona sai na ji wani dunƙule da ba kamar yadda na saba ba. Nan take na fara zargin wata matsala ce, daga baya kuma aka tabbatar min cutar daji ce."
Tana bayar da labarin cikin natsuwa ba tare da nuna wata alamar fargaba ko damuwa ba.
"Ni likita ce, kuma na saba duba marasa lafiya tare da gano irin waɗannan abubuwa. Da na ji wannan dunƙulen a nonona, na fahimci cewa sankara ce," in ji ta, domin ita ma ƙwararriya kan cututtukan da suka shafi mahaifa da al'aurar mata, wadda ta shafe shekaru masu yawa tana yaƙi da cutar sankarar mama.
Tsawon shekaru tana sadaukar da lokacinta da ƙarfinta wajen wayar da kai, da gudanar da gwaje-gwajen gano cutar kyauta, tare da tallafa wa mata marasa galihu da ke fama da sankarar mama. Amma yanzu ita ma dole ta yi fama da cutar a matsayin mara lafiya.
Ƙalubale ne da ta sha ganin wasu mata suna fuskanta, kuma ta ce ta karɓe shi da zuciya ɗaya a matsayinta ƙaddara.
"Na gode wa Allah, domin na ga tasirin cutar sankara a rayuwata da kuma cikin iyalina. Na kasance tare da wasu daga cikin 'yan uwana har zuwa lokacin da suka rasu sakamakon cutar," in ji ta.
Duk da gano cutar a wannan mataki na rayuwarta, Fatma ta ce hakan bai girgiza ta ba ko kaɗan.
"A koyaushe nakan ce Dakta Fatma Guénoune ce ta gano cutar Fatma Guénoune. Haka nake son marasa lafiya su kalli halin da suke ciki," in ji ta.
Matar, wadda ta shafe sama da shekara goma tana jagorantar ƙungiyar yaƙi da cutar sankara a Senegal (LISCA), ta ce gano cutar ya ƙara mata imani.
Bayan gano cutar ta yanke shawara mai tsauri

Asalin hoton, Lisca
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai daga bisani ta yanke shawarar cire nonuwanta gaba ɗaya.
Ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda cutar sankarar mama tana yawan faruwa a cikin danginsu.
"Ban ga amfanin ci gaba da zama da nonon da cuta za ta iya sake bayyana a cikinsa ba. Haka kuma ba na son na ci gaba da rayuwa cikin fargabar sake kamuwa da cutar. Saboda haka ne na zaɓi a cire nonuwana gaba ɗaya," in ji ta.
Fatma Guénoune ta ce yanke wannan shawara bai yi mata wuya ba.
Ta ce: "A shekaruna yanzu, ba na ganin kasancewa ta a matsayin mace sia ian da nono ba. Don haka ba ni da wata damuwa idan mutane suka gan ni ba tare da nono ba."
Tun bayan aikin, tana samun magani da take amfani da shi, kuma ana sa ran za ta ci gaba da jinyar na wasu shekaru.
Da aka tambaye ta yadda iyalanta da na kusa da ita suka ji labarin, musamman kasancewar sun saba ganinta a matsayin wadda ke taimaka wa masu fama da sankara, sai ta ce da farko ba su yarda cewa ita ma ta kamu da cutar ba.
"Da yawa daga cikinsu sun kasa yarda cewa ni ma ina fama da sankarar mama," in ji ta.
"Ina da wani ƙani da ya yi zaton wasa nake yi. Shi ne wanda ya fi kowa kuka lokacin da ya gan ni da bandeji bayan tiyatar, domin tun farko bai yarda cewa da gaske ina da cutar ba," in ji ta.
Ta bayyana cewa ta ci gaba da rayuwarta har bayan da gwaje-gwaje suka tabbatar tana ɗauke da cutar. Wannan ne ma ya sa wasu mutane suka riƙa shakkar ko da gaske tana fama da rashin lafiyar.
Ta ce: "Misali, wata 'yar uwata ta tambaye ni dalilin da ya sa ban yi kuka ba. Sai na ce mata, idan ni na yi kuka, wa zai kwantar muku da hankali? Ai ni ce na saba ƙarfafa muku gwiwa. Ba ku ne za ku ƙarfafa min gwiwa ba. Don haka dole na tsaya da ƙafafuna domin kaina da kuma dominku."
Mutum zai yi tunanin cewa kamuwa da cutar da ya shafe shekaru yana yaƙi da ita zai sauya yadda yake kallon abubuwa. Amma ga Fatma Guénoune, hakan bai canja komai ba.
Yadda ta yi yaƙi da cutar sankarar mama

Asalin hoton, Lisca
"Ban canza ra'ayina ba. Hasali ma, a kullum ina tsayawa tare da mata masu buƙata, musamman marasa lafiya da kuma waɗanda rashin hali ya hana su samun magani," in ji Dakta Fatma.
Wannan ƙuduri ne da ta runguma tun tana likita, wanda ya sa ta mayar da yaƙi da cutar sankara wani muhimmin ɓangare na rayuwarta. Haka kuma ne ya kai ta ga shiga ƙungiyar LISCA, wadda take jagoranta tun fiye da shekara goma da suka gabata.
A cikin ƙungiyar, ita da takwarorinta suna ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da tallafa wa mata masu fama da cutar sankara, domin taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen da cutar ke haifarwa.
Ƙungiyar ta ce: "Mun yi imanin cewa idan muka haɗa kai, za mu iya shawo kan ƙalubale tare da ba da ƙwarin gwiwa ga waɗanda suka fi buƙatar hakan. Kowace gudummawa, ko ƙarama ko babba, da kowane irin taimako ko yunƙuri, na ƙara ƙarfafa gwiwar masu fama da cutar sankara da kuma tsarin tallafin da ke tare da su."
Ta ƙara da cewa: "Cutar sankara cuta ce mai tsanani, amma fatan samun waraka shi ne abin da ke ƙarfafa mu. Mun san cewa kowane ci gaba da ake samu, kowace nasara, da kowane binciken da ake gudanarwa, suna taimakawa wajen gina makoma mai kyau. Muna kuma da yaƙinin cewa tare da goyon bayan kowa, bege na iya zama hanya zuwa ga samun waraka."
Yin gwaje-gwaje na taimakawa

Asalin hoton, Lisca
A cewar ƙungiyar LISCA, ana samun sabbin masu fama da cutar sankarar mama kusan 2,220 a kowace shekara a Senegal, yayin da sama da mutum 1,300 ke rasuwa sakamakon cutar.
Mata marasa galihu da ke zuwa LISCA na neman shawara da tallafi domin fuskantar cutar, wadda kuɗin jinyarta ke kaiwa kusan CFA franc miliyan 5.3 ga mai fama da sankarar mama.
Idan bincike ya tabbatar da cewa mara lafiya ya cancanci tallafin ƙungiyar, LISCA na taimaka masa da kuɗaɗen jinyar (chemotherapy), gwaje-gwajen likitoci, hotunan bincike (scan), tiyata, da gwajin radiotherapy, kulawar bayan jinya, da kuma tallafin lafiyar ƙwaƙwalwa.
Yayin da take ci gaba da fuskantar ƙalubalen da cutar sankarar mama ke haifarwa, LISCA na ƙara zage damtse wajen wayar da kai da kuma ƙarfafa gano cutar tun da wuri, wanda har yanzu ake ɗauka a matsayin hanya mafi inganci ta ceton rayuka da rage nauyin da cutar ke ɗorawa kan iyalai.
A Senegal, tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na masu sankarar mama ne ake gano cutar a lokacin da ta riga ta yi tsanani, lamarin da ke rage yiwuwar samun waraka.































