Lafiya Zinariya: Illar shan shisha ga lafiyar ƴan mata
Lafiya Zinariya: Illar shan shisha ga lafiyar ƴan mata
Shirin Lafiya Zinariya na wannan mako ya tattauna kan illar shan shisha ga lafiyar ƴan mata.
Hukumar yaƙi da cutuka ta Amurka ta ce tabar shisha ta samo asali ne daga ƙasashen Iran da Indiya a shekaru da dama da suka gabata.
Hukumar ta ce wani bincike da aka yi a Amurka a shekarar 2018, ya nuna cewa kusan kashi takwas cikin ɗari na ɗaliban babbar sakandare sun taɓa shan shisha a 2017.
Amurka CDC ta ce gawayin da ake amfani da shi wajen tafasa shisha na fitar da gurɓataccen iska na Carbon monoxide da na karfe da kuma wasu sinadarai da za su iya janyo cutar daji.
Sannan sinadarin tobacco da ake amfani da shi a shisha da kuma hayakin na ɗauke da abubuwa masu guba, ɗa ke janyo sankarar huhu da ta mafitsara da ta baki.