Elizabeth I: Sarauniyar Ingila da ba ta taɓa aure ba

الملكة إليزابيث الأولى

Asalin hoton, Alamy

    • Marubuci, نيل أرمسترونغ
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 7

Sarauniya Elizabeth I, wadda ƴa ce ga Sarki Henry VIII, ita ce sarauniya ɗaya tilo wadda ba ta yi aure ba, sannan ziyararta zuwa gidan sarauta na Kenilworth kimanin shekara 450 da suka gabata na ƙunshe da wasu bayanai game da soyayyarta da yadda ta ƙi amincewa da yunƙurin neman aurenta.

Da yammacin wata rana a watan Yulin shekarar 1575, Sarauniya Elizabeth I a lokacin tana da shekara 41 ta je Kenilworth a yankin Warwichshire a wata ziyara da ake gani ita ce ziyara mafi tsawo, kuma ta ƙarshe zuwa gidan a rayuwarta.

Sarauniyar ta ba Robert Dudley kyautar gidan na sarauta ne a 1563, sannan bayan shekara ɗaya ta naɗa shi sarautar Earl of Leicester. Dudley na cikin makusantan sarauniyar, sannan ana cewa ya kasance na kusa da ita tun suna ƙananan yara.

Yanayin kusancinsu ya haifar da ce-ce-ku-ce sosai a Birtaniya da ma gutsuri-tsoma a tsakanin mutane.

Elizabeth I da Robert Dudley sun kasance na kusa da juna

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Elizabeth I da Robert Dudley sun kasance na kusa da juna

Robert Dudley ya yi gyare-gyare a gidan sarautar a shirye-shiryen da yake yi karɓar baƙuntar sarauniyar. Sannan ya ƙara sababbin gine-gine, inda ya samar da wani lambu babba a ciki.

Haka kuma ya yi duk abin da zai iya yi wajen ƙawata gidan sannan ya tanadi dukkan kayan alatu, sannan ya wani babban bikin nishaɗi irin su kaɗe-kaɗe da raye-raye.

Dudley ya kashe kuɗi sosai a taron tarbar, inda aka ƙiyasta taron ya ci aƙalla fam 1,000 a kullum, kimanin dala 1,400 a kullum, kuɗin da zai kai kimanin miliyoyin daloli a yanzu.

Jeremy Ashbee, shugaban kula da kayayyaki a gidajen adana tarihi na English Heritage ya shaida wa BBC cewa, "an shirya ƙayataccen taron na 1575 ne domin neman amincewar Sarauniya Elizabeth.

Wani hoto daga fim ɗin Elizabeth na 1998

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Wani hoto daga fim ɗin Elizabeth na 1998

Shirye-shiryen Dudley sun fara tafiya ne kyau kafin abubuwa suka fara lalacewa. Asali an shirya za a yi wani salon rawa da ake kira 'masque', wanda aka tsara yi a ranar Laraba 20 ga watan Yulin.

Sai dai amma ba a samu nasarar raƙashewar ba. Shin sokewa ake yi saboda rashin yanayi mai kyau kamar yadda hukumomi suka bayyana? ko kuma dai ita sarauniyar ce ta fahimci maƙasudin shirya taron, ranta ya ɓaci ta fasa zuwa?

A taron bikin, an shirya wata dodanniya soyayya da aure mai suna Juno za ta zo ta yi magana da Sarauniya Elizabeth, inda za ta buƙace ta da ta guji bin tafarkin Diana, ta yi aurenta ta sama iyali.

Duk da cewa Dudley ya samu dama sosai wajen samun kusanci da sarauniyar, amma wannan saƙon da aka shirya isar wa ga sarauniyar ya girmama sosai. Amma dai ko ma dai mene ne, ba a yi taron ba, inda sarauniyar ta kasance a gefenta a cikin gidan sarautar na wasu ƴan kwanaki kafin ta fice a ranar 27 ga watan na Yuli.

"Ƙarfin mulki"

Ziyarar Elizabeth zuwa Kenilworth shekara 450 da suka gabata ne suka sa aka mai fasahar zane Lindsay Mendak ya sassaƙa wasu mutum-mutumi.

Asalin hoton, Lindsey Mendick/ Courtesy English Heritage/ Jim Holden

Bayanan hoto, Sassaƙen da aka yi domin tuna ziyarar Elizabeth zuwa Kenilworth shekara 450 da suka gabata
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai fasahar zane-zane Lindsey Mendick ta sassaƙa wasu mutum-mutumi domin cika shekara 450 da ziyarar Sarauniya Elizabeth zuwa gidan sarautar, waɗanda ta kira "Wicked Game" a cikin gidan sarauta.

Ta sassaƙa mutum-mutumi guda 13 domin nuna sarauniyar da waɗanda suke tare da ita amma a surar dabbobi. Ta nuna sarauniyar a tsakiya a matsayin zakanya, sai ga Dudley a matsayin barewa.

Mendick ta shaida wa BBC, "ina matuƙar girmama ta kuma ina ƙaunarta, kuma tarihinta zai taimaka mana matuƙa domin fahimtar yadda ya kamata mata su rayu a zamanin yanzu. Taron da Dudley ya shirya a Kenilworth, an shirya shi ne a matsayin gagarumin bikin nishaɗi da raƙashewa, amma a bayan fage akwai wasu manufofin shirya taron. Amma yadda Sarauniya Elizabeth, duk da girmanta da darajarta sai ta zaɓi rayuwa ba tare da aure ba, ko kuma ta haifa ƴaƴa."

Sarauniyar Elizabeth I, ƴar Sarki Henry VII, ita ce sarauniyar Ingila tilo da ba ta taɓa yin aure ba. Ta ɗare karagar sarauta ne a shekarar 1558 tana da shekara 25, inda ta gaji ƴanuwanta Edward VI da ya yi mulki 1537 zuwa 1553 da Mary I tsakanin 1516 zuwa 1558.

Masu bayar da shawara da masu riƙe da sarauta da dama sun ta matsa mata lamba cewa ta yi aure saboda darajar kujerar da take riƙewa da ma tsaron ƙasar saboda a lokacin ana kallon mulkin mace a matsayin wani abu na daban. Ana ganin ya kamata mace mai sarauta ta yi aure ne saboda ko ba don ta haifa ɗa magaji ba ma, tana buƙatar miji da zai taimaka mata wajen kula da yanayin a harkokin soji.

Duk da irin neman aurenta da aka yi, da masu zuwa da kansu da masu aike, amma Elizabeth ta ƙeƙashe ƙasa ta ce sam ba za ta yi auren ba.

"Rashin tsayayye"

Hoto daga cikin fim ɗin Elizabeth: The Golden Age (2007), wanda a ciki aka nuna jaruma Cate Blanchett da ta fito a matsayin sarauniyar da ba ta damu da komai ba sai sarauta

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Hoto daga cikin fim ɗin Elizabeth: The Golden Age (2007), wanda a ciki aka nuna jaruma Cate Blanchett da ta fito a matsayin sarauniyar da ba ta damu da komai ba sai sarauta

Elizabeth ta yi amannar cewa mace za ta yi sarauta da mulki ba tare da dole sai tana da aure ba. A shekarar 1544, ta ga yadda Catherine Parr, matar Sarki Henry VIII ta ɗare karagar mulki lokacin da sarkin ya tafi yaƙi a Faransa.

Haka kuma abubuwan da ta gani a aure sun ƙara taimakawa wajen cire mata rai. Misali mahaifinta ya sa an kama mahaifiyarta Anne Boleyn bisa zarginta cin amanar aure da haɗa baki, sannan ya amince a yanke mata hukunci ta hanyar fille mata kai a lokacin da Elizabeth take da shekara 3 a duniya.

Daga cikin sassaƙen Mandick akwai wanda ke nuna yadda ake yanke wa mahaifiyar sarauniyar hukunci, inda aka nuna Anne a tsugune tana addu'a shi kuma mai aiwatar da hukuncin yana jira.

Wasu masana kuma suna ganin wataƙila Elizabeth na tsoron mu'amalar aure, inda marubuciya Alison Weir ta rubuta a littafin mai suna 'Elizabeth the Queen' cewa akwai yiwuwar "sarauniyar tana da alamun haɗa soyayya da mu'amalar aure da mutuwa a kusa da kusa ne."

A shirin da BBC ta shirya a 2005 mai taken 'The Virgin Queen' an nuna Elizabeth a matsayin sarauniyar mai tsoron mu'amalar aure.

Amma dai an Elizabeth da zama da maza kyawawa, kuma tana mu'amala da su da ke nuna shaƙuwa sosai. Amma tana da hujjojin tsoron samun ciki da ma haihuwa.

A zamanin 1485 zuwa 1603 an sha fama da matsalolin haihuwa. Jane Seymour, matar Henry VIII ta rasu ne a lokacin haihuwa, Catherine Parr ta rasu ne bayan jinyar da ta sha fama da ita bayan haihuwa, sannan kakar Elizabeth ita ma a wajen haihuwa ta rasu.

Yadda ake kallon Elizabeth

Tun farkon mulkinta take nuna kanta a matsayin sarauniya da ba ta san namiji ba

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Tun farkon mulkinta take nuna kanta a matsayin sarauniya da ba ta san namiji ba

Bayan wasu dalilai nata, akwai kuma abubuwan da suke da alaƙa da siyasa da suka hana Elizabeth aure, waɗanda ake tunanin daga ciki akwai burinta na nesanta ƙasarta daga kutsen ƙasashen waje.

Don haka, da a ce misali ta auri Robert Dudley, ke nan ba don rasuwar matarsa a wani yanai wai wahalar fahimta ba a shekarar 1560, da an riƙa samun rigingimu da za su iya shafar gudanar da sarauta.

Sai kawai Elizabeth ta bar kowa cikin tunani, inda ta nuna kanta a matsayin sarauniyar da ta fi damuwa da buƙatun mutanenta sama da nata na kanta. Tun farkon sarautarta take nuna wa duniya cewa ita "Sarauniya ce da ba ta san ɗa namiji ba".

A shekarar 1559 da take amsa tambaya daga ƴan fadarta da suke takura mata sai ta yi aure, sai ta ce, "duniya za ta riƙa tunawa cewa an taɓa yin wata sarauniya da ta yi mulki, sannan ta rasu ba ta taɓa yin aure ba."

الملكة إليزابيث الأولى

Asalin hoton, Alamy

A fim ɗin da aka yi tarihinta, Sarauniya Elizabeth— wadda jaruma Glenda Jackson ta taka rawa, ta ce :

"tun ina shekara takwas na daina yarda da maza. Na ga lokacin Sarauniyar Catherine matar Sarki Henry VIII da aka yanke wa hukuncin ksa take ta gudu a cikin fada tana roƙon yafiyar sarkin. Amma babu namijin da ya saurare ta."

Amma tambayar ita ce: shin Elizabeth ta ba Dudley damar nuna mata soyayya? sannan shin mene ne amfanin ziyarar Kenilworth a tarihin soyayya?

Ashby ya ce: "ba na tunanin Dudley zai yi fushi don ta ƙi aurensa. A wasiyyarsa ma ya buƙaci a bar gidan sarautar a yadda yake. Ina tunanin yana matuƙar son abin da ya faru a ranar kuma yana kallonsa a matsayin rana mafi girma a rayuwarsa."

Sarauniyar ta ji haushi da Dudley ya aura Lettice Knollys a 1578, amma daga baya ta yafe masa. Lokacin da ya rasu a 1588, ta kulle kanta a cikin ɗaki na tsawon lokaci har sai da aka ɓalle ƙofar ta fito.