Ko halittun da za su zo nan gaba za su gane ɗan'adam ya rayu a duniyar nan tamu?

Asalin hoton, Microgen Images/Science Photo Library via Getty Images
Mu 'yan'adam muna da yawan kewar abubuwan da suka wuce.
Mun bankaɗo abubuwan da ke ƙarƙashin marasa iyaka a tsawon tarihin duniya na shekara biliyan huɗu da rabi, waɗanda suka ba mu damar fahimtar yadda wasu halittu suka rayu kafin mu zo dunyar.
Amma da a ce mu ma za mu ƙare kuma wasu halittun masu basira su taso nan da miliyoyin shekaru, ko za su san da rayuwarmu mu ma? Ko kuma wace irin rayuwa muka yi?
Damar mayar da mu duwatsu
Ba zai yiwu mu dogara da cewa masu binciken kimiyyar tarihi za su iya samun duwatsun da ke nuna alamun rayuwarmu ba, in ji Adam Frank, farfesa a fannin ilimin physics a Jami'ar Rochester da ke Amurka.
"Wani ɗan ƙalilan ɗin ɓangare ne na rayuwa a kan wannan duniya ta Earth aka taɓa narkarwa zuwa duwatsu, musamman al'ummomin da ba su daɗe ba sosai a duniya," a cewarsa.

Asalin hoton, Courtney Hale/E+ via Getty Images
Wata maƙala da Farfesa Frank ya haɗa gwiwa wajen rubutawa ta nuna cewa duk da yawaitar dabbar dinosaur a duniya tsawon shekaru miliyan 165, 'yan ƙalilan aka samu na duwatsun da ke nuna alamun rayuwarsu har zuwa yanzu.
Sbaoda haka, maƙalar ta nuna ganin cewa ɗan'adam bai wuce shekara 300,000 a raye ba zuwa yanzu, ba lallai mu samu wata damar da za a dinga tunawa da mu ba a tarihi.
Amma za mu iya barin wasu alamomi na daban.
Sauya kimiyyar sinadarai
Wani ɓangare na tsarin kimiyyar ƙasar dunya shi ne amfani da duwatsu a fannoni da dama.
Kowane launin dutse na wakilta ko kuma nuna nau'in yanayin da duniya ke ciki a lokacinsa.
A cewar Farfesa Frank, yawan ƙaruwar zafi da toroƙon tekuna saboda ayyukan da ɗan'adam ke yi za su shafi abin da ke jikin duwatsun, wanda "za a iya bincikawa nan da wasu miliyoyin shekaru daga yanzu".
"Za a tarar da bambanci a sinadarin isotopes saboda yanayin duniyar Earth ya sauya sakamakon ayyukan ɗan'adam," in ji shi.
Juya halittar mazauna duniya
Ko da a ce ba a samu ƙasusuwanmu a tsarin fossil ba, wato duwatsu, akwai yiwuwar mu sauya jujjuyawar halitta na wasu tsirrai ko kuma dabbobi da muka yi safara zuwa wurare daban-daban.
Wani bincike da aka gudanar a 2018 ya gano cewa kashi 96 cikin 100 na dabbobi masu shayarwa a duniya sun kasance mu 'yan'adam ko kuma dabbobinmu.
Sama da biyu cikin uku na makamashin halittar da tsuntsaye ke samu na zuwa ne daga dabbobinmu.
Mukan yanka kaji fiye da biliyan 75 duk shekara, a cewar alƙaluman ƙungiyar Our Wolrd in Data. Saboda haka irin wannan dubun dubatar halita da ke mutuwa a lokaci guda za su sa a sha wahalar alkinta wata alama ta halittarsu.
Babban abin da za a fi tunawa da mu
A wani littafi mai suna Discarded: How Technofossils Will Be Our Ultimate Legacy, Farfesa Zelasiewicz da abokin aikinsa na Jami'ar Leicester a Birtaniya, Farfesa Sarah Gabbott, sun yi imani cewa abubuwan da ke tattare da mu ne za su ci gaba da zama bayan mun bar duniya.
Sun kira wannan yanayi da technofossils - kamar gwangwanayen lemo da muke sha, ko wuraren ajiyar mota na ƙarƙashin ƙasa, ko ledojin zuba abubuwa.

Asalin hoton, Sarah Gabbott
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike a 2020 ya ƙiyasta cewa muna samar da gigatonne 30 na abubuwa duk shekara - wanda ke nuna kowane ɗan'adam na samar da kayayyakin da suka zarta nauyin jikinsa duk mako.
Ya kuma gano cewa yanzu muna da abubuwan da ɗan'adam ya samar a duniya fiye da abubuwa masu rai.
Mafi yawan abubuwan da 'yan'adam ke ƙerawa na samuwa ne daga kankare, wanda ba lallai masu bincike na nan gaba su iya gane shi ba.
"Ɗaya daga cikin hanyoyin da muke ƙirƙirar kankare a yanzu har da amfani da hodar fly ash...idan aka hange shi ta madubin microscope za a gan shi wani iri ne," in ji Farfesa Zelasiewicz.
"Idan suka ga abubuwan da aka haɗa da wannan hodar za su ji cewa ba shi ne suka sani ba a matsayin kankare.
Da yawna abubuwan da muke amfani da su za su daɗe ba su gushe ba tsawon lokaci.
Farfesa Gabbott ya ce Robobi "za su iya yin miliyoyin shekaru ba su ɓace ba".
Muna yawan amfani da roba sosai ta yadda nan da shekarar 2050, za a samu robobi a cikin teku da suka fi kifi yawa a cikin ruwa, kamar yadda hasashen Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna.
"Akwai duwatsun da suka shafe shekaru biliyan huɗu," Farfesa Gabbott ya bayyana.
Tuni ɗan'adam ya bar alama mai girman gaske a duniyar Earth. Sai dai babu tabbas ko wasu halittu masu basira za su gan su bayan mun tafi.
Amma ko abu ne mai amfani mu dinga tunanin abin da za mu bari tun yanzu?
Farfesa Frank na ganin hakan.
"Ina ganin ya kamata mu tsallake wannan ƙarni na rashin dattako a fannin fasaha, mu samu damar yin tunani game da tarihinmu a duniya nan da miliyoyin shekaru masu zuwa," a cewarsa.











