Yadda Rasha ke fitar da fetur da satar bayanai ta jiragen ruwa na bogi

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Alexey Kalmykov
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian Business reporter
- Lokacin karatu: Minti 7
Fadar gwamnatin Rasha ta ce ƙasar tana da kariya daga takunkumin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya na haramta biyu daga cikin manyan kamfanonin man fetur ɗin ta. To amma Rashar na amfani da wasu jiragen dakon mai da za a iya cewa kusan na ɓoye ne wajen safarar man nata da aka sanya wa takunkumi ga masu saya da araha a faɗin duniya.
Bayan irin waɗannan 'yan kasuwa masu neman araha akwai kuma shugabannin Iran da janar-janar na Venezuela, kai hatta ma miyagun 'yan kasuwa na Turai, waɗanda su riba ce a gabansu kawai, ba ruwansu da wata magana ta illa ga muhalli ko ma maganar lafiyar matuƙa waɗannan jiragen ruwa da ke haramtaccen aikin dakon man na Rasha, matuƙan da za a iya watsi da su tsawon watanni ko ma shekaru a cikin jirgin ruwa a teku idan ta kwaɓe.
Tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine a 2022, haramtaccen aikin irin waɗannan jiragen ruwa na Rasha ya ƙaru, kuma gwamnatin Putin ita ce babbar mai cin moriyar wannan harka.
Gwamnatin tana amfani da wannan hanya ta satar hanyar sayar da man ƙasar domin samun kuɗin gudanar da yaƙinta da Ukraine, kamar yadda Trump ya ce, da kuma gudanar da ayyukan leƙen asiri da yi wa ƙasashen Nato zagon-ƙasa a Turai, da kuma wayoyi da bututai na cikin teku da ƙasashen ke amfani da su.

Asalin hoton, AFP
Rasha na cikin manyan ƙasashe uku da suka fi fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje a duniya - tare da Amurka da Saudiyya.
A 2024 Rasha ta samar da kusan kashi 10 cikin ɗari na man fetur a duniya, kamar yadda Amurka ta bayyana.
Kafin yaƙin Ukraine kusan dukkanin man fetur na Rasha, jiragen ruwan ƙasashen Yamma ne, galibi na Girka ke safararsa.
To amma yanzu kusan jiragen ruwa huɗu cikin biyar da ke dakon man na Rasha, ba su da wata inshora ta wani fitaccen kamfani na duniya, inda ake nuni da cewa kusan kashi 80 cikin ɗari na man na Rasha da take fitarwa, abin da ya saba wa takunkumin yammacin duniya.
''Rasha ta tara jiragen ruwa masu dakon mai na ɓad-da-bami, inda take amfani da su wajen kauce wa takunkumin da aka sanya mata, in ji Benjamin Hilgenstock, masani a Kyiv (Kyiv School of Economics Institute).

Asalin hoton, Getty Images
Kusan duk jirgin ruwa ɗaya cikin biyar na dakon mai da ke teku, na daga cikin waɗannan jiragen ruwan dakon mai na ɓad-da-bami, inda suke satar fitar da mai na ƙasashen da aka sanya wa takunkumi.
Daga cikinsu, kashi 50 cikin ɗari na dakon man fetur da kayan Rasha, kashi 20 na dakon na Iran, kuma kashi 10 na dakon na Venezuela.
To amma kuma sauran kashi 20 cikin ɗari na jiragen dakon takamaimai babu ƙasar da suke dakon nata man, suna iya yi wa kowa.
Kuma manyan waɗanda suke dakon man Rasha da Iran da Venezuela, kusan suna safara ne zuwa India da China.
Ƙananan ƙasashen da ke sayen man na Rasha sun haɗa da Turkiyya da Singapore da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Asalin hoton, Corbis via Getty Images
Domin ɓatar da sawu waɗannan jiragen ruwa suna amfani da wasu hanyoyi kamar:
- kwashe mai daga wannan jirgin su zuba a wani a can cikin teku inda ba a sanya ido, ko yankin ba ya ƙarƙashin wata ƙasa, kuma a lokacin da ake fama da yanayi maras kyau domin kada a gane daga ina jirgin ya fito.
- Kashe ko lalata na'urar da ke aikawa da bayanai a kan jirgin - kamar inda yake da gudun da yake yi da sunansa da tutar da yake ɗauke da ita da sauran bayanai - wani lokacin ma har su bayar da bayanan bogi.
- Suna ɓoye bayanan mallakar jirgin da sauya lambar rijistarsa sau da dama a cikin wata ɗaya.
- Sukan ɓad-da sawu ta hanyar bayar da lambobin rijista na tsohon jirgin da aka keɓe domin lalatawa ko fawarsa- wanda lokacin amfani da shi ya ƙare.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Oktoba na 2025, wani jirgin ruwa na dakon mai, mai ɗauke da tutar ƙasar Benin da aka yi zargin ana iya amfani da shi wajen kai hare-hare na jiragen sama marasa matuƙa, wanda hakan ya tilasta rufe filayen jiragen sama a Denmark, inda aka tsare jirgin a gaɓar tekun Faransa, saboda masu tuƙin jirgin ruwan sun ƙi bayar da haɗin kai, tare da kuma da tabbatar da jirgin ruwan na wace ƙasa ne.
Akwai kuma zargin Rasha ta yi kutse na jiragen sama marasa matuƙa a kan ƙawayen Nato - Sweden da Norway da Jamus.
Haka kuma a watan Nuwamban 2025, ala tilas aka rufe filin jirgin sama na Brussels na ɗan wani lokaci saboda an ga ƙananan jiragen sama marasa matuƙa a kusa da filin da wasu wurare, ciki har da sansanonin soji a Belgium.
Rasha dai ta musanta kai hari kan ƙawayen Ukraine.
A sanadiyyar binciken da aka yi a kan jirgin ruwan na Boracay, ƙasashen Nato sun zartar da matakai na tabbatar da tsaro a kansu, da suka haɗa da yuwuwar kutsawa cikin duk wani jirgi da ake zargin barazana ce da kama jirgin ruwan, in ji Babban Sakataren Nato, Mark Rutte.
To sai dai wata matsala dangane da tsare irin waɗannan jiragen ruwa da ba a san su ba, ita ce, ba za ka iya kama jirgin ruwan da ke tafiya a can cikin teku ba sai dai wanda ya raɓi ruwan ƙasarka - wato mil 12 daga gaɓar ƙasarka ko kuma ya shigo tashar ƙasarka.
Haka kuma 'yan siyasar Rasha sun nemi da ƙasar ta ɗauki duk wata barazana a kan jirgin ruwan da ke dakon man fetur ɗin ta a matsayin hari a kan ƙasar kanta.
Wannan ne ya sa a lokacin da Estonia ta yi yunƙurin tsare wani jirgin dakon mai maras tuta a tsakanin Estonia da Finland a watan Mayu na 2025, Rasha ta aika jiragen sama na yaƙi suka kewaye jirgin ruwan.

Asalin hoton, Reuters
Manyan kamfanonin jiragen ruwa galibi suna rabuwa da jirgin ruwa na dakon mai idan ya yi shekara 15.
Bayan shekara 25, kuma ana wargaza su ko fawarsu saboda sun tsufa. To amma su jiragen ruwa na ɓad-da-bami, ba a karɓarsu a yi fawarsu.
Saboda irin matsaloloin waɗannan tsofaffin jiragen ruwa ne, a watan Disamba na 2024, hukumomin Rasha suka rasa yadda za su yi da wasu irin waɗannan jiragen ruwa biyu masu shekara 50 da suka gamu da matsala ta guguwar teku inda suka zubar da tan 5,000 na man da suke ɗauke da shi a Zirin Kerth.
Wani babban masanin kimiyya na Rasha, Viktor Danilov-Danilyan, ya bayyana wannan zubar da mai a matsayin bala'in muhalli mafi muni na ƙasar na ƙarni na 21.
Kamfanonin da ake fakewa da su wajen gudanar da ayyukan bayan fage irin su Dubai, waɗanda wasu Rasha ce ke bayar da kuɗaɗen gudanar da su a cewar Financial Times, suna sayen tsofaffin jiragen ruwan da a ƙa'ida aka lokacin amfani da su ya ƙare, wanda hakan ke rikita kasuwar tare da hana yin wasu sababbi da kamfanoni ke yi.
An amfani da harkar saye da sayar da jiragen ruwan cikin gaggawa ta waɗanda ke yi a ɓoye - ba a san su waye ba a zahiri ko kuma sababbin kamfanoni, domin ɓoye bayanai.
Sannan kuma irin waɗannan jiragen ruwa na dako da ake wannan harka da su, ba sa samun kulawar da ta dace, suna tsiyayar da mai a teku.
Bugu da ƙari suna da haɗarin yin karo da wasu jiragen a hanyar da ba ta da faɗi, saboda na'urar nuna musu hanya da ta lalace ko aka kashe don kada a gano su, saboda rashin aikinta.
Duk da haka harka ce da masu ita ke samun maƙudan kuɗade, wadda kuma idan aka samu haɗari ko matsala, kamar tsiyayar mai, babu ruwansu duniya ce ke ɗanɗana kuɗarta tun da ba su da inshora.
Ko da kuwa an janye wa Rasha da sauran wasu ƙasashe takunkumin da aka sanya musu, wannan harka da amfani da jiragen ruwan na dakon mai na ɓoye za ta ci gaba a wasu hanyoyin na safara ta teku.










