Forest ta doke Wolves za ta hadu da Man Utd a Kofin Carabao

Asalin hoton, Getty Images
A daya karawar da aka yi a gasar ta cin Kocin na EFL ko Carabao a ranar ta Laraba, Nottingham Forest ta doke Wolverhampton Wanderers 4-3 a bugun fanareti.
Tun da farko sun tashi a wasan kunnen doki, wato 1-1, daga nan sai aka tafi bugun fanareti, inda Forest ta samu galabar da ta sa za ta kara da Manchester United a wasan kusa da na karshe mai karawa biyu, gida da waje.
Za su yi wasannin ne a makonnin da za su fara daga 23 da 30 ga watan nan na Janairu.
A karawar ta Laraba, Forest ce ta fara cin kwallo inda tsoffin 'yan wasan Wolves Morgan Gibbs-White da Willy Boly, suka yi wa-ta-gangano, da bugun kusurwa, da Gibbs-White ya aika wa Boly, wanda shi kuma bai yi wata-wata ba ya shekata a raga, minti 18 da wasa.
Wolves ta farke kwallon bayan an koma daga hutun rabin lokaci a minti na 64 ta hannun Raul Jimenez.
Nottingham Forest ta kai wasan na kusa da karshe a wannan gasar ta cin kofin EFL karon farko a shekara 31, inda za ta kara da Manchester United, wadda ta doke ta a wasan karshe na 1992.






