Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila

Mutanen Isra'ila da dama na barci a lokacin da aka fara.

Asabar ita ce ranar da Yahudawa ke ɗauka da muhimmanci a addininsu, ma'ana iyalai suna shirin zama tare, abokai kuma suna taruwa don kasancewa tare da juna.

Amma tun daga wayewar gari, luguden rokoki ya yi nuni da fara harin da ba a taɓa yin irin sa ba, idan aka lura da girma da kuma tsarinsa.

Shekaru da dama Isra'ila ta yi ta karfafa shingen da ke tsakaninta da karamin yankin Falasdinu na Gaza. A cikin sa'o'i, an fallasa rashin ingancin shingen.

BBC ta yi nazarin bidiyo da 'yan bindiga da fararen hula da ke ƙasa suka dauka domin gano yadda aka yi kungiyar Hamas ta iya tsara wani gagarumin harin da ba a taɓa ganin irin sa daga Gaza ba.

Rokoki suka sanar da farawar harin

Da misalin karfe 06:30 agogon ƙasar ne rokoki suka fara tashi.

Ƙungiyar masu fafutukar Islama - wadda ke iko da Gaza kuma aka sanya ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci a Burtaniya da sauran ɓangarorin duniya - na amfani da wannan dabara a kai-a kai.

Yawancin rokokin da ake harbawa ba kasafai suke iya ƙetara na'urar kariya na makamai masu linzami na Iron Dome da Isra'ila ke da ita ba - amma an harba dubbai cikin ƙanƙanin lokaci don raba hankalin na'urar.

Yanayin harin ya nuna cewa an kwashe watanni da dama ana tsara shi. Hamas ta ce ta harba rokoki 5,000 a zagayen farko (Isra'ila ta ce rabin adadin ne aka harba).

An fara jin ƙarar jiniyar da ke sanar da hari daga sama har zuwa Tel Aviv mai tazarar kilomita 60 daga Gaza da kuma yammacin birnin Ƙudus kuma an ga hayaƙi yana tashi a saman garuruwan da aka kai wa hari.

Yayin da ake ci gaba da harba makaman roka, mayaka na taruwa inda suke shirin ƙetara shingen Gaza.

Duk da cewa Isra'ila ta janye sojojinta da 'yan kasarata mazauna yankin Gaza a shekara ta 2005, har yanzu tana iko da sararin samaniyarta da kan iyaka da kuma bakin teku.

Kazalika ta na gudanar da aikin sintirin sojoji akai-akai a kewayen yankin- wanda katangar kankare ce a wasu wurare da kuma shinge a wasu wuraren - akwai kuma kyamarori da na'urorin tsaro don hana kutse.

Amma a cikin sa'o'i, an ketara shingenfiye da sau ɗaya.

Ta yaya mayakan Hamas suka sami wucewa?

Wasu mayakan Hamas sun yi kokarin ketare shingen gaba daya, ciki har da yunkurin yin saukar lema ta samata (hotunan da ba a tantance ba sun nuna akalla bakwai suna shawagi a saman Isra'ila) da kuma amfani da jiragen ruwa.

Dakarun tsaron Isra'ila sun ce sun dakile yunkurin Hamas guda biyu na tsallakawa cikin Isra'ila ta hanyar amfani da jiragen ruwa a gabar teku.

Amma abin da ya banbanta wannan harin shi ne tsara hare-hare da dama da dama, da kuma kai hari kai tsaye kan shingen tsaro.

Da misalin karfe 05:50 agogon ƙasar, wani shafin Telegram da ke da alaƙa da reshen Hamas da ke dauke da makamai ya sanya hotunan farko daga ƙasa, waɗanda aka ɗauka a Kerem Shalom - mafi kudancin mashigar Gaza.

Sun nuna mayakan sun mamaye wani shingen tsaro da gawarwakin sojojin Isra'ila guda biyu a ƙasa.

Wani hoton kuma ya nuna aƙalla babura biyar kowanne ɗauke da ‘yan bindiga biyu da ke rike da bindigogi, suna wucewa ta inda aka yanka wayar shingen.

A wani yanki da babu isahsen tsaro, an ga wata katapila tana ruguza wani shingen da aka yi da wayoyi.

Mutane da dama ne da ake ganin ba sa dauke da makami suka taru a wajen, wasu kuma suka wucewa ta ɓangaren da aka ruguza.

A Erez - yanki mafi nisa daga arewacin mashigar Gaza, mai tazarar kilomita 43.4 daga Kerem Shalom - Hamas ta sake mmaye wata mashigar.

An buga bidiyo a daya daga cikin tashoshin farfaganda na kungiyar. Hakan ya nuna fashewar wani shingen kankare, wanda ya yi nuni da fara kai harin, sannan kuma ana iya ganin wani mayaki yana kiran gungun mayaka zuwa wurin da fashewar ta auku.

Wasu mutane takwas sanye da rigar tare harsashi da bindigogi sun arce zuwa wani shingen binciken ababen hawa inda suka buɗewa sojojin Isra'ila wuta.

Daga baya a cikin bidiyon, an ga gawarwakin sojojin Isra'ila a kwance a ƙasa yayin da mayaƙan ke bi ɗaki zuwa ɗaki suna kewaye wurin, cikin tsari da horarwa.

Gaza na da mashigai bakwai a hukumance - shida Isra'ila ce ke iko da su, ɗaya kuma da ke zuwa Masar na ƙarƙashin kulan Cairo.

Amma a cikin 'yan sa'o'i ƙadan, Hamas ta sami hanyoyin shiga cikin yankin Isra'ila da ɓangarori daban-daban na shingen.

Hare-haren sun yi nisa cikin yankin Isra'ila

Mayaƙan Hamas sun kwararo daga ɓangariri daban-daban na Gaza. Yanzu dai mun san daga mahukuntan Isra'ila cewa sun kai hari a wurare daban-daban har guda 27 a cikin Isra'ila, bisa ga dukkan alamu suna ƙarƙashin umarnin su buɗe wuta kan sojojin Isra'ila.

Gari mafi nisa da Hamas ta kutsa kai shi ne garin Ofakim, wanda ke da tazarar kilomita 22.5 daga gabashin Gaza. Taswirar da ke ƙasa tana nuna wurare daban-daban da suka isa.

A Sderot, an ga mayaƙan da ke tsaye a bayan wata motar ɗaukar kaya da ake tuƙawa a cikin garin, wanda ke da nisan kilomita 3 zuwa gabashin Gaza.

Kimanin mayaka 12 ne dauke da makamai aka ga suna shawagi a kan titunan Ashkelon, wadda ke arewacin mashigar Erez da aka kai wa hari.

An sake maimaita irin wannan yanayi a kudancin Isra'ila kuma sojoji sun gaya wa fararen hula su ɓoye a cikin gida.

A wani bikin kade-kade da ke kusa da Re'im, 'yan bindiga sun bude wuta kan gungun matasa da suka taru a hamada.

Wani ganau ya shaida wa BBC yadda 'yan bindigan ke zagayawa da wata motar ɗaukar kaya da ke shaƙe da makamai kuma suka shafe sa'o'i uku suna bincike a yankin don neman 'yan Isra'ilan da za su kai wa hari.

An kama sojoji da fararen hula

Yanzu mun san cewa an kwashe mutanen da aka yi garkuwa da su daga bikin da sauran wurare kuma an mayar da su cikin Gaza. Isra'ila ta ce an sace mutane 100 - sojoji da fararen hula.

Hotunan da aka ɗauka a garin Be'ri da BBC ta tabbatar sun nuna wasu fararen hula huɗu da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su.

Akwai bidiyon da ke ta yawo a intanet na wasu Isra'ilawa, wasu daga cikinsu da ke da munanan raunuka, ana terere da su a kan titunan Gaza.

An ɗauki wasu ayyukan ta’addancin da ba a tantance ba kuma muninsu ba zai bari a iya bugawa ba, wadanda suka hada da wani direban mota da aka ciro daga motarsa ​​aka yanke masa makogwaro, da kuma yadda aka wulaƙanta gawarwakin wasu fararen hula da na sojoji.

Baya ga hare-haren da aka kai kan al'ummomin Isra'ila, Hamas ta kuma kai hari kan wuraren soji guda biyu: wani sansani a Zikim da kuma wani a Re'im.

Hotunan da aka ɗauka daga kusa da Re'im sun nuna abin da ya biyo baya, inda aka ga ƙonannun motoci da dama a warwatse a kan hanyar zuwa sansanin. Ba a dai san adadin mutanen da aka kashe yayin fadan ba.

Kafofin sada zumunta na Hamas sun sha yada hotunan sojojin Isra'ila da suka mutu, amma BBC ba su tabbatar da sahihancin waɗannan hotunan ba.

A cikin 'yan sa'o'i kaɗan da fara harba makaman roka, ɗaruruwan 'yan Isra'ila sun mutu - kuma hakan ya faru ta hanyar da babu wanda ya yi tunanin zai yiwu.

Agaji ya fara isa yankin kudancin da ke fama da rikici a cikin 'yan sa'o'i kaɗan, amma Hamas, ta kasance tana a cikakken iko kan wasu yankunan da ke wajen Gaza na wani lokaci.

Saurin da aka yi amfani da shi wurin kai harin na bazata ya baiwa Isra'ila mamaki. Za a kwashe shekaru da dama ana takaddama kan yadda aka yi aka gudanar da wannan harin.

Da tsakar safiya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa: "Mun tsunduma cikin yaki."