Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Hamza Umar Assudani
Filin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna da Malam Hamza Umar wanda aka fi sani da Assudani.
An haifi malamin a unguwar Kwarbai da ke cikin birnin Zariya a shekarar 1980.
Ya soma karatunsa na addini a gidansu, amma daga bisani an tura shi wurin wasu manyan malamai inda ya ci gaba da karatu.
Kazalika malamin ya shiga makarantar boko inda ya soma a makarantar firamare ta Lemu sanna ya je makarantar firamare ta Larabci, wato Provincial Arabic Primary School, wadda ya kammala a 1992.
Malam Hamza ya yi karatun sakandare a Jama'atu Arabic School da ke Zaria inda ya gama a 2000.
Daga nan ya tafi makarantar gaba da sakandare ta Munazzama da ke Kura a Jihar Kano.
Malamin ya kara da cewa daga bisani ne ya tafi kasar Sudan inda ya yi digiri kuma ya kammala a 2005.
Kazalika ya dawo Najeriya inda ya yi digiri na biyu wato Masters a Jami'ar Bayero da ke Kano a 2014.
Malamin ya ce akwai malamai da suka yi tarisi a rayuwarsa amma babu kamar Sheikh Ahmad Maqary Sa'id.