Kasaitacciyar Jana'iza - su wane ne a gaba-gaba a binne Sarauniya Elizabeth II?

Dubun dubatar sojojin Burtaniya da na kasashen waje ne za su kasance a sahun gaba yayin jana'izar kasa da ake yi wa Sarauniya Elizabeth a taro mai cike da tarihi.

Taron ya kunshi duk rundunonin soji, da 'yan gidan sarauta, da manyan hadiman Sarauniya ne za su yi wa basarakiyar mai dogon zamani bankwanan karshe inda za a binne ta a Windsor.

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka kamata ku sani kan ainihin yadda jana'izar za ta kasance.

Sojojin Burtaniya da kasashen Commonwealth za su yi maci a birnin London da Windsor.

Za kuma su yi jerin gwano, tare da bai wa dakarun ban girma damar gudanar da tasu hidimar.

Sarauniya dai ta kasance babbar kwamandar askarawan Burtaniya kuma tana da alaka ta kukut da sojoji, don haka za su yi wa gawarta rakiya tun daga birnin London har zuwa Windor, inda a nan ne wurin karshe da za a yi binne ta.

Rukunin farko kuma gajerun zaratan sojoji za su dauki gawar tun daga Westminster Abbey zuwa zauren addu'o'i, daga Westminster Abbey kuma sai Wellington Arch, kafin a dangana da ita Windsor. Da zarar gawar ta isa Windsor, sai sashe na uku na sojojin fsdsr St George's Chapel su dora daga inda suka tsaya.

Abin da za a mai da hankali a kai shi ne kashi na biyu, wato tafiya da gawar tun daga birnin London bayan gama addu'o'i, inda 'yan sanda na musamman wato Canadian Mounted Police, za su raba kansu zuwa rukuni shida, da rakiyar makadan badujala.

Mambobin rundunar sojin Burtaniya da na kasashen Commonwealth, da 'yan sanda har da jami'an NHS za su shiga wannan biki. Ana sa ran dakarun za su bar Westminster Abbey da tsakar rana cikin mintuna 45.

Za a sa akwatin gawar Sarauniya, da aka yi wa adon ban mamaki, a tsakiya kuma za a dora kambun masarautar a kan gawar, zagaye da runduna ta musamman ta sojin ruwa da za su harba bindiga domin girmama ta.

Tun cikin 1979 aka kera igwar da ta dauko gawar kawun Yarima Philip, wato Lord Mountbatten, sannan da ita aka dau gawar mahaifin Sarauniya wato Sarki George VI, a 1952.

Sojojin Grenadier Guards ne za su take mata baya, da dakarun tsaron Sarki da wani bangare na sojojin Gentlemen at Arms, da na Yeomen na kamfanin sojin masarauta na Archers.

Manyan masu sarauta, ciki har da Sarki Charles na III da 'ya'yansa Yarima William da Yarima Harry ne, za su take wa gawar Sarauniya baya.

Sauran 'ya'yan gidan sarauta su kuma za su kasance a baya. Sarauniya Consort Camilla, Yariman Wales, da Countess ta Wessex da Duchess ta Sussex na cikin wadanda za su yi wa gawar Sarauniya rakiya a cikin mota.

Yadda cikakkiyar janazar za ta kasance

'Yan sandan dawakai na Burtaniya da dakarun kasashe kamar sojin saman New Zealand • 'Yan sandan masarauta na Canada • Makadan badujala da maharban bindiga na Gurkhas • Wakilan George Cross daga Malta, 'Yan sandan Constabulary da hukumar lafiyar Burtaniya • Da duk wata rundunar masu damara daga sassa daban-daban na duniya na cikin wadanda za su yi wannan kasaitaccen biki mai cike da tarihi da za a dade ba a ga irinsa nan kusa a fadin duniya ba.

Wakilan sojin sama na masarauta: 603 (daga birnin Edinburgh) da tawagar makadan badujalarsu, da sojin sama na Marham, da na kwalejin sojoji da ke Cranwel da sauraunsu

Wakilan sojoji: Kamfanin Artillery • Masu mukamin janar-janar • Makadan badujalar Burtaniya na Sandhurst da Colchester • Injiniyoyin Gurkha na Sarauniya • Dakarun fadar Welsh • Rundunar Duke din Lancaster • Da ta Scotland • Rundunar Wales • Rundunar Ireland • Makadan badujalar Ireland, da sauransu

Wakilan sojin ruwan Burtaniya: Tun daga kan manya da kanana da makadan badujalarsu

Masu ba da shawara kan harkokin tsaro: Daga kasashen Jamaica • New Zealand • Australia • Canada

Wakilan kasashen Commonwealth da Sarauniya ke jagoranta

Wakilan rundunonin tsaron da Sarauniya ke jagoranta.

Wakilan jiragen ruwan Sarauniya Masarauta; Mataimakin sarkin gida • Mai jan ragamar ma'aikatan masarauta • Wazirin baitul malin masarauta • Masu takewa Saraunuiya baya • Mai kula da fannin ruwa • Masu kula da walwalar Sarauniya

Masu dafawa keken dokin baya:

Wakilan Cavalry

Iyalan Masarauta: Earl na Wessex da Forfar • Duke na York • Gimbiya Anne • Sarki • Peter Phillips • Duke na Sussex • Yariman Wales • Mataimakin Admiral Sir Tim Laurence • Duke na Gloucester • Earl din Snowdon

Mota ta 1: Matar Sarki • Gimbiyar Wales Mota ta 2: Duchess ta Sussex • Matar Countess na Wessex da Forfar Rundunar soji • Masu bai wa masarauta tsaro, ayarin gidan sarki: Sarkin gida • Mai tsaro • Babban sakataren masarauta • Ma'aji

Runduna kasa ta biyu Wakilan farar hula: Sojin ruwa • Sojin ruwa na masarauta • Hukumar masu tsaron teku • Rundunar 'yan sanda • Rundunar 'yan kwana-kwana • Hukumar gidajen yari • Hukumar motocin daukar marasa lafiya • Kungiyar agaji ta Red Cross • Motocin daukar marasa lafiya na St John • Ma'aikatan sa-kai na Masarauta • Matasan sojojin da aka bai wa horo da ke baya: 'Yan sanda masu hawa doki. An samo bayanan nan daga: Fadar Buckingham Palace, da rundunar sojoji

Da zarar tafiyar ta kai Wellington Arch da ke Hyde Park Corner, da misalin karfe 1 na rana agogon Burtaniya, za a maida akwatin gawar cikin wata sabuwar mota, daga nan a yi tafiyar karshe da ita zuwa hubbaren sarakuna da ke cikin Fadar Windsor, inda za a binne Sarauniyar.

Da misalin karfe 3 na rana, ake sa ran motar gawar za ta isa inda ta nufa, sai kuma doguwar tafiyar da za a yi da kafa har zuwa Fadar Windsor. Tafiya ce ta nisan mil uku, da wakilan rundunonin soji za su yi jerin gwano tare da dafewa gawar Sarauniya baya.

Ana sa ran Sarki da manyan 'ya'yan sarauta za su isa Fadar Windsor, don addu'o'in karshe, daga nan kuma sai a binne Sarauniya Elizabeth ta II a bangaren hubbaren St George wanda Sarauniyar ce da kanta ta jagoranci bikin bude shi a shekarar 1962.