Yadda aka gano ƙasurgumin mai fataucin mutane zuwa Turai

Scorpion aka Barzan Majeed
    • Marubuci, Sue Mitchell & Ben Milne
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Mun samu tattaunawa gaba da gaba da ɗaya daga cikin gawurtattun masu safarar mutane a faɗin Turai, a cikin wani kantin cin abinci a ƙasar Iraƙi.

Sunansa Barzan Majeed, kuma yana cikin mutanen da 'yan sanda ke nema ruwa a jallo a ƙasashe da dama ciki har da Birtaniya.

A cikin tattaunawar da muka yi da shi, a kantin da ma a ofishinsa a washe garin ranar - ya faɗa min cewa bai san adadin 'yan ciranin da ya tsallakar da su zuwa Turai ba.

“Wataƙila za su iya kai wa 1,000 ko 10,000. Ban dai sani ba, don ba ƙidayawa nake yi ba''.

Ganawar tamu ta kasance wani abu da ake ganin kamar ba zai yiwu ba 'yan watannin da suka gabata.

Tare da Rob Lawrie, wani tsohon jami'in soja da ya yi aikin kulawa da 'yan gudun-hijira, na samu damar shirya tambayoyi ga mutumin da ake yi wa laƙabi da Scorpion.

Scorpion ya shafe shekaru - tare da taimakon mutanen da ke aiki ƙarƙashinsa - suna aikin safarar mutane zuwa sassa daban-daban na nahiyar Turai ta hanyar amfani da ƙananan jiragen ruwa.

Fiye da 'yan cirani 70 ne suka mutu a ƙoƙarinsu na tsallakawa da jiragen tun 2018, a watan da ya gabata mutum biyar aka kashe a gaɓar tekun Faransa, ciki har da ƙaramar yarinya mai shekara bakwai.

Yan cirani kusan 60 ne ke tsallaka Ingila a watan Maris na 2024.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dubban 'yan cirani ne ke ƙoƙarin tsallaka tekun Ingila a kowace shekara
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tafiya ce mai cike da hatsari, amma ga 'yan fasa ƙaurin sana'a ce mai gwaɓi.

Sukan karɓi fan 6,000 ga kowane mutum da za a tsallakar ta jirgin ruwa, kuma yayin da kusan mutum 30,000 suka yi yunƙurin tsallakawa a shekarar 2023, lallai ribar mai gwaɓi ce.

Sha'awarmu ta hira da Scorpion ta faro ne daga wata ƙaramar yarinya da muka hadu da ita a sansanonin 'yan cirani da ke arewacin Faransa.

Yarinyar ta kusa mutuwa a ƙoƙarinta na tsallaka tekun Ingila - wanda ya raba tsakanin kudancin Ingila da arewacin Faransa a cikin wani ƙaramin jirgin ruwa.

Ƙaramin jirgin ruwa da suka hau ba shi da inganci, wanda ka saya a matsayin tsoho a Belgium - sannan aka maƙare shi da fasinjoji 19 waɗanda ba su da rigunan kariya.

Wane ne zai tura mutane cikin teku irin wannan?

A yayin da wasu ke ajiye lambar da sunan ''Scorpion'', wasu kan sanya hoton 'kunama' domin adana lambar a cikin wayarsu.

A 2006 lokacin da yake ɗan shekara 20, aka yi fataucin Majeed zuwa Birtaniya a cikin wata motar ɗaukar kaya, Inda ya kwashe shekaru a Birtaniya, wasu daga ciki a gidan yari saboda laifukan da suka shafi ƙwaya da bindiga.

A shekarar 2015 ne aka fitar da shi daga Birtaniya zuwa Iraƙi, daga nan ne ake tunanin Majeed ya gaji sana'ar fataucin mutane zuwa Turai daga wajen yayansa wanda ke zaman hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Belgium.

Tsakanin shekarar 2016 zuwa 2021, Scorpion da yaransa ne ke iko da mafi yawan sana'ar safarar mutane tsakanin Turai da Birtaniya.

Barzan Majeed

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Majeed a 2012, lokacin da yake aiki a matsayin bakanike a Nottingham

Farautar da 'yan sanda suka ƙaddamar cikin shekara biyu ta haifar da kama mutum 26 'yan dabar Scorpion, tare da gurfanar da su a kotunan Birtaniya da Faransa da kuma Belgium.

An saurari ƙararsa a Belgium, duk kuwa da bai halarci kotun ba, inda kotun ta same shi da laifuka 121 da suka jiɓanci safarar mutane.

A watan Oktoban 2022 kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari, tare da cin sa tarar fam miliyan 8.25.

Tun daga lokacin aka rasa inda Scorpion ya shiga, wanda kuma hakan na daga cikin abubuwan da muke son ganowa.

Wani abokin Rob ya gabatar da mu ga wani mutumin Iran, wanda ya ce ya yi mu'amala da Scorpion a lokacin da yake ƙoƙarin tsallaka tekun Ingila.

Scorpion ya shaida wa mutumin Iran ɗin cewa a Turkiyya yake zaune, daga can ɗin ne kuma yake gudanar da sana'arsa.

A Beligium, mun nemi ganin yayan Majeed - wanda yanzu aka sake shi daga gidan yarin. Ya gaya mana cewa yana tunanin Scorpion na Turkiyya.

Barzan Majeed
Bayanan hoto, Scorpion (wanda ba a ɓoye fuskarsa ba) tare da 'yan uwansa - Ba a san wuri da lokacin da aka ɗauki hoton ba

Ga mafi yawan 'yan ciranin da ke son shiga Birtaniya, Turkiyya ce mafi muhimmanci a gare su, saboda dokokin ƙasar game da 'yan cirani, abu ne mai sauƙi a samu bizar ƙasar daga kowace ƙasa a Afirka da Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya.

Bincikenmu ya kai mu ga wani shagon shan shayi da masu fataucin mutane ke yawan ziyartarsa, inda a baya-bayan nan aka ga Barzan a ciki.

Da farko haƙarmu ba ta cimma ruwa ba, saboda mun tambayi manajan kantin ya faɗa mana irin sana'ar da kantin nasa ke gudanarwa, amma sai ya ƙi.

Daga nan, sai wani mutum ya miƙe a gabanmu tare da zuge zip ɗin rigarsa, domin nuna mana bindigar da ke jikinsa.

Dabararmu ta gaba ta haifar da sakamako mai kyau. Saboda an gaya mana cewa ba a jima da Majeed ya tura wasu kudi kimanin fam 172,000 a wajen wani mai sana'ar tura kuɗi a kan titin da ke kusa da kantin abincin.

Mun bar wa mutumin lambar wayarmu, domin kiran mu idan an sake ganin sa. Muna kwance cikin wannan sai wayar Rob ta yi ƙara a daren.

Wanda ya yi kiran ya ɓoye lambarsa, da aka ɗauki wayar muryar wani mutum muka ji da yake iƙirarin cewa shi ne Majeed.

Kira ne da ba mu tsammata ba, don haka rob bai samu damar naɗar farkon magangar da suka yi ba, abin da mutumin ya ce shi ne, ''Ina jin ka, na ji an ce kuna nema na'', sai Rob ya ce masa ''e kana ina? Scorpion ne?, sai ya ce ''au haka kake son kira na? to hakan ma ya yi''.

“Wannan ba gaskiya ba ne!” Ya bijire sam! “Kawai ƙaryar kafofin yaɗa labarai ne.”

Daga nan wayar ta tsinke, kuma duk da ƙoƙarin da muke yi ya ƙi gaya mana wurin da yake.

Istanbul

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Santanbul: Turkiyya ta kasance wuri mafi muhimmanci ga 'yan ciranin da ke son shiga Turai

Abokin Rob ya faɗa mana cewa Scorpion na harkar safarar mutane daga Turkiyya zuwa ƙasashen Girka da Italiya.

Abin da muka ji game da shi ya matuƙar razana mu, an ce ya kan loda aƙalla mutum 100, maza da mata da ƙananan yara cikin jirgin da ya kamata ya ɗauki mutum 12.

Masu safarar mutanen ne ke tuƙa jiragen ba tare da ilimin tuƙin jirgin ruwa ba, inda kuma suke bin hanyoyi masu hatsari tsakanin ƙananan tsiburan tekun domin kaucewa masu tsaron teku.

An ce kowanne fasinja na biyan kusan Euro 10,000, domin shiga jirgin. A cikin shekara 10, fiye da fasinjoji 720,000 ne aka yi tunanin sun yi yunƙurin tsallakawa ta tekun Baharrum zuwa Turai, daga ciki kusan mutum 2,500 ne suka mutu sakamakon kifewar jiragen.

Garin Crotone na kasar Italiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Febrairun 2023: Aƙalla 'yan ci-rani 95 ne suka mutu a jirgin ruwa a ƙoƙarinsu na shiga Italiya daga Turkiyya.

Scorpion ya musanta cewa shi mai fataucin mutane ne. To amma ma'anar da ya bai wa kalmar na nufin wanda ke kama mutanen da hannunsa ba wanda yake shirya yadda aikin ke gudana ba.

“Ai mai safarar mutane dole ya kasance a wurin da ake aikin,” in ji shi, “Kuma ko yanzu ba na wurin.”

Majeed ya nuna tausasawa ga 'yan ciranin da suka nutse.

“Da ma tuni Allah ya riga ya ƙaddarawa kowa inda zai mutu, to amma wasu lokutan akwai sakacin mutane, saboda ai Allah bai ce ka shiga jirgin ba.”

 Marmaris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ce Scorpion ya mallaki wata fada a wani wurin shaƙatawa a Turkiyya.

To amma mun samu kira daga wata da tace ta son Majeed na gudanar da sana'ar fataucin mutane, ta ce ta sani cewa damuwarsa ita ce kuɗi, ba halin da 'yan ciranin za su shiga ba.

“Abin baƙin cikin, shi ne ba ya damuwa da halin da za su shiga'',

Ta ce a baya-bayan nan, ba ta gan shi a fadar tasa ba, duk da cewa wani ya faɗa mata cewa yana Iraƙi.

Wani abokin Rob ya tabbatar mata cewa ya ga Scorpion a wurin tura kuɗi a birnin Sulaymaniyah, da ke yankin Kurdistan na Iraƙi.

Daga nan kuma muka tsara tafiya Iraƙi, tare da nufin cewa daga nan in ba mu same shi ba za mu haƙura.

Abokin na Rob ya yi ƙoƙarin magana da shi, da fari ya yi tunanin cewa ƙoƙarin haɗa baki ake yi domin kama shi.

Amma sai ya turo masa saƙon waya yake tambayarsa ''kana ina''?

Mun gaya masa cewa muna kan hanyar zuwa wani kantin sayar da kayyaki.

Daga nan sai ya ce mana mu same shi a sashen shan shayi na kantin da ke hawa na ƙasa.

Daga ƙarshe kuma mun samu nasarar haɗuwa da shi

Barzan Majeed
Bayanan hoto, Direban Sue da Rob ya samu damar naɗar ganawarsu da Scorpion a sirrance.

Barzan Majeed yayi kama da ɗan wasan ƙwallon golf. Ya yi kwalliya da baƙin wandon jeans da rigarsa mai launin ruwan bula tare da falmaran akai.

Akwai wasu mutum uku a zaune kusa da mu da muke kyautata zaton masu tsaronsa ne.

Ya musanta laifin da ake zargin sa da shi na zama babban mai aikata laifi, yana mai cewa wasu mutane ne suka ɓata masa suna.

“Da yawan mutane idan an kama su sai su ce tare muke aiki, saboda ba sa so a yanke musu dogon hukuncin ɗauri.”

Ya ce abin haushin ma shi ne akan bai wa wasu masu safarar mutane bizar Birtaniya domin gudanar da ayyukansu.

“A cikin kwana uku da suka gabata, wani mutum ya aika 'yan cirani 170 ko 180 zuwa Italiya daga Turkiyya, kuma abin mamakin su mutanen na riƙe da fasfon Birtaniya, amma ni ina ma son zuwa wasu ƙasashen don yin kasuwanci amma ba dama tun da ba ni da fasfo.''

Bayan kammala hirar ya kai Rob wani shago a Sulaymaniyah da ya ce a nan yake sana'ar tura kuɗi.

Tsakanin 2016 zuwa 2019, Scorpion yana cikin mutum biyu da ke jagorantar sana'ar tsakanin Belgium da Faransa, inda ya ce ya samu miliyoyin daloli a lokacin.