Tsohon saurayin 'yar wasan Olympics ya cinna mata wuta ta mutu

m

Asalin hoton, Alamy

Lokacin karatu: Minti 2

Yar wasan Olympics Rebecca Cheptegei ta mutu, bayan tsohon saurayinta ya watsa mata fetur tare da cinna mata wuta.

'Yar tseren gudun Uganda mai shekara 33, wadda ta halarci gasar Olympics kwanan nan da ta gudana a Paris, ta yi matuƙar ƙonewa sosai bayan harin da ya kai mata ranar Lahadi.

Hukumomin yankin arewa maso yammacin Kenya inda Cheptegei ke zaune kuma take atisaye, sun ce sai da ya daidaici lokacin da take dawo daga coci da ita da 'yaranta mata biyu sannan ya afka mata.

Mahaifinta Joseph Cheptegei ya ce ya yi rashin yarinya mai taimakawa rayuwarsa.

Abokiyar wasanta James Kirwa ta shaida wa BBC yadda take da kirki da kuma yadda take taimakawa ƙanana da manyan 'yan tsere da kuɗi.

Wani rahoto da jami'an cikin gida suka fitar ya yi zargin cewa marigayiyar da tsohon saurayin nata sun yi ta rikici ne kan wani fili. 'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike a kai.

Cheptegei, wadda daga wani yanki ta tsallaka iyakar Uganda, an ce ta sayi filin ne a lardin Trans Nzoia ta kuma gina gida kusa da cibiyar aitisayen tseren gudu ta Kenya.

Hare-haren da ake kai wa kan mata yana ɗaukar hankali a Kenya. A wani bincike da hukumar bincike ta ƙasar ta yi, ya ce a 2022 aƙalla kashi 34 na matan ƙasar sun fuskanci cin zarafi.

"Wannan lamari da ya faru manuniya ce kan yadda ake buƙatar ɗaukar matakin gaggawa game da matsalar banbancin jinsi, wanda a haknali yake ƙaruwa kan masu harkokin wasanni," in ji Ministar wasannin Kenya Kipchumba Murkomen.

v

Asalin hoton, Uganda Atheltics Federation

Da yake tattaunawa da manema labarai a wajen asibitin da ta kwanta, Mista Cheptegei ya nemi gwamnatin Kenya ta tabbatar an yi adalci kan mutuwar 'yarsa.

"Gwarzuwar gidanmu ta rasu," yana cewa tunanin yadda yaranta biyu da ke da shekara 12 da 13 za su ci gaba da karatunsu.

Dr Kimani Mbugua, wani kwararre ne a asibitin Moi da ke Eldoret, ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa, ma'aikatansu sun yi iya ƙoƙarin su ga an ceci 'yar tseren gudun sai dai ta riga ta ƙone yadda wasu sassan jikita ba za su ci gaba da aiki ba, wanda hakan ya kai ga mutuwarta a yau da misalin ƙarfe 5:30 na safe.

Kirwa wadda ta ziyarci Cheptegei a asibiti, ta shaida wa BBC "mutuniyar kirki ce. Tana taimaka mana da kuɗi kuma ta kawo mani takalmin tsere bayan dawowarta daga Olympics. Tamkar yayata ce ita".

s

Asalin hoton, AP