Me ya sa ƙasar UAE ke faɗaɗa mallakar filayen noma a Afirka?

Asalin hoton, ADQ
Fiye da shekara 10 da suka wuce, ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ƙoƙarin ƙulla alaƙa da Afirka ta hanyar tsare-tsaren tattalin arziki, ciki har da alaƙar kasuwanci da hulɗar tasoshin ruwa da sauran fannonin zuba jari.
Haka kuma ƙasar da ke yankin Gulf ta kuma yi wata dabarar mallakar filaye a yankin na Afirka domin noma, da kiwon namun daji da samar da wuraren shaƙatawa na bakin teku domin masu yawo buɗe idanu.
Sannan kuma ƙasar ta samu manya-manyan dazuka, domin samar da iskar Carbon, wata dabara da masu suka da masu rajin kare dazuka ke kallo a matsayin ƙwace filaye.
To sai dai samun irin waɗannan filaye da ƙasar ta UAE ka iya haifar wa wasu ƙasashen Afirka illoli, ciki har zaizayar ƙasar, da rashin wadataccen abinci a ƙasashen, da tilasta wa al'ummomin yankin ficewa daga ƙasashen, wani abu da ka iya haifar da rigingimu da matsalolin muhallai.
Daga samar da abinci zuwa mallakar filaye

Alƙaluman Bankin Duniya daga 2023 sun nuna cewa kashi 0.7 na ƙasar UAE ne kawai za a iya noma a cikinta.
Abu Dhabi - wadda ke shigar da kashi 85 zuwa 90 cikin 100 na abincinta - ta ƙaddamar ta shirinta na wadata kai da abinci zuwa 2051, da nufin ''kawar yunwa ta hanyar tabbatar da samar da wadataccen abinci mai gina jiki a kowace shekara''
Fiye da shekara 10 da suka gabata, ƙasar ta faɗaɗa harkokin cinikayyarta da ƙasashen Afirka, musamman fannin abinci.
Nan da nan wannan ƙoƙarin ya samo asali daga samun abinci zuwa matsayin cibiyar cinikayyar abinci ta duniya, lamarin da ya share mata fagen samun filaye a Afirka. Sau da yawa ana aiwatar da waɗannan yarjejeniyoyi ta hanyar kamfanoni masu alaƙa da iyalan masarautar ƙasar.
Waɗannan kamfanoni sun zama manyan ginshiƙan noma a ƙasashen Afirka, ciki har da ADQ da Al Dahra da Al Qudra da Elite Agro Projects da Al-Rawabi da Jenan Investments da IHC da kuma ADIA.
Alal misali kamfanin ADIA ya kwashe shekaru yana samun filayen noma a ƙasashen yankin da dama da suka haɗa da Masar da Kenya da Ethiopia da Uganda da Angola da Morocco da Madagascar da Namibia da Saliyo da kuma Sudan.
Shirin samar da abinci a Kenya
Al Dahra ya sanya hannunkan yarjejeniyar samar da abinci da dala miliyann 96.7da ƙasar Kenya a ranar 8 ga watan Agustan 2025 domin noman abinci a katafariyar gonar da ta kai eka 180,000 a ƙasar.
Sakataren shirin, Chris Kiptoo ya ce yarjejeniyar Al Dahra za ta "ƙarfafa samun kudin shiga daga ƙetare".
An fara tunanain samar da shirin a 2013 domin ƙarfafa samar da abinci a ƙasar da ke gabashin Afirka da ta jima tana fama da matsalar fari da ƙarancinn abinci.
Aƙallah ƴan Kenya miliyan 20 ba su da wadatar abinci, a cewar wani rahoto da wani kamfanin mai zaman kansa ya wallafa ranar 12 ga watan Oktoba.
Faɗaɗa cinikayyar abinci a Uganda
A ranar 23 ga watan Satumba, wani shafin gwamnati ya bayar da rahoton cewa Uganda da Kamfanin samar da abinci na UAE na wani aikin hadin gwiwa a fannin harkokin noma.
Shafin ya ce haɗin gwiwar zai ƙarfafa cinikayyar abinci tsakanin ƙasashen biyu da kusan kashi 30 cikin 100.
Abincin da Uganda ke fitar wa zuwa ƙasar UAE ya haura dala miliyan 50.
Noman inibi da dabino a Namibiya
A watan Mayun 2017, wani kamfani a UAE mai suna Socotra Island Investment ya sayi wasu gonakin inibi a namibiya.
Gonakin inibin na kusa da Kogin Orange da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Afriuka ta Kudu.
A 2011 Kamfanin NDC na Namibiya da takwaransa na ADAD na ƙasar UAE suka haɗa hannu wajen samar da wata ƙatuwar gonar noman dabino da inibi da ta kai eka 220 mai nisan kilomita 40 kudu da garin Keetmanshoop a yankin Karas da ke kudanci.
Yawon buɗe-idanu
Baya ga harkar noma kasar UAE na ƙoƙarin samar da wuiraren yawon buɗe idanu a ƙasashen Afirka.
A ƙasar Masar, kamfanin ADQ ya ƙulla yarjejeniyar dala biliyan 35 domin gina birnin gaɓar teku a Ras al Hekma a 2024, da ya kai eka 40,600.
Haka ma akwai rahotonnin da suke ce ƙasar UAE ta sayi wani fili a Tanzaniya ''domin samar da wuraren kiwon namun daji da na yawon shaƙawa'', lamarin da ya haifar da fargabar ficewa daga yankin ga ƴan asalin yankin ƴan ƙabilar maasai kusan 70,000.

Asalin hoton, Emirate Leaks
Sannan a Afirka ta Kudu, wata jarifa mai zaman kanta, ta ruwaito a 2022 cewa wasu mutane kusan 31 yan ƙabilar Maasai sun ji raunuka sakamakon arangama da jami'an tsaro, kan rikicin filin noma da ya kai tsawon kilomiya 1,500.
Haka kuma an fitar da wasu ƴan ƙabilar Mau a Kenya daga wani daji da suka zaune bayan da wani kamfanin UAE ya buƙaci dajin domin samar da isakar carbon.
'Samar da iskar Carbon'
Haka ma kasar ta, Abu Dhabi ta samu miliyoyin eka na filaye daga Afirka domin samar da iskar carbon.
Ƙasar ta wannan shiri a ƙasashen Kenya da Zambiya da Zimbabwa da Tanzania da Liberia da Comoros da kuma Nijar, ta hanyar wani kamfanin ƙasar mai suna Blue Carbon, kamar yadda jaridar Sheikh Ahmed Dalmook Al Maktoum mallakar iyalan masarautar ƙasar.

Asalin hoton, @HAKAINDEHICHILEMA/FACEBOOK
Haka kuma wani shafin intanet mai zaman kansa mai suna 'Standard' ya ruwairo cewa Kenya ta bayar da miliyoyin eka na gonaki ga kamfanin Carbon.
Duk da cewa ba a san adadin gonakin da Kenya ta bai wa kamfanin Blue Carbon, Zimbabwe ta bayar da eka miliya 18 sannan Laberiya ta bayar da miliyan miliyan 2.5 Zambiya miliyan 20 sannan kuma Tanzaniya ta bayar da miliyan 20.











