Hotunan yadda mahajjata ke gudanar da tsayuwar Arfa

...
Bayanan hoto, Wani ɓangare na alhazai da suka taru a kan Dutsen Arfa wanda aka fi sani da Jabal al-Rahma suna addu'a da neman biyan buƙata yayin aikin Hajji a ranar 5 ga Yuni, 2025.
Lokacin karatu: Minti 2
Arfa
Bayanan hoto, Nan wani alhaji ne a kan dutse Arfa ya ɗaga hannu yana addu'a, domin neman biyan buƙatu.
Arfa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mahajjaciya a gaban dutsen Arfa ta ɗaga hannu tana gudanar da addu'o'i a ranar Arfa sanye da gurumfa domin kariya daga zafin rana.
Mahajjaci daga Najeriya

Asalin hoton, NAHCON

Bayanan hoto, Mahajjaci daga Najeriya, Ahmed Mu'azu na addu'o'i a cikin tanti a filin Arfa.
..
Bayanan hoto, Wani ɓangare na mahajjata a kan Dutse Arfa yayin da wasu suke tsaye kusa da Dutsen.
..
Bayanan hoto, Wasu mahajjata ɗauke da lema suna neman kariya daga tsananin zafin rana.
..
Bayanan hoto, Alhazai a filin Arfa suna adu'o'i da gudanar da sauran ayyuka yayin da fankokin da aka kafa ke ba su iska saboda tsananin zafi.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani alhaji ya ɗaga hannuwa yana adu'o'i da kuka a kan dutsen Arfa
..
Bayanan hoto, Alhazai zaune a filin Arfa suna ɗaga hannu suna adu'o'i, wasu kuma suna tsaye.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani alhaji a kan dutsen Arfa yana addu'a.
..
Bayanan hoto, Kan Dutsen Arfa cike da alhazai cikin tufafin ihram suna ibada da adu'o'i.