Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa kayan abinci ke ci gaba da tsada a Najeriya?
Farashin kayan abinci na ci gaba da hawa da sauka a Najeriya duk da matakan da ake ɗauka na magance tsadar rayuwa a ƙasar.
A cikin rahotonta na baya bayan nan da ta fitar, hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayan abinci a kasar ta kai kashi 37.52 a watan Agusta inda aka samu ƙarin kashi 8.18 idan aka kwatanta da Agustan bara.
Sai dai alƙalumman sun ce hauhawar ta kai kashi 2.37 a Agusta idan aka kwatanta da watan Yuli inda aka samu raguwar kashi 0.10.
Rahoton ya nuna an samu ƙaruwar farashin ƙwai a Agusta da kashi 5.48 idan aka kwatanta da watan Yuli.
Rahoton ya kuma ce an samu ƙaruwar farashin wake a Agustan 2024 inda ake sayar da kilogram daya kan N2,574.63 inda aka samu ƙaruwar kashi 271.55 idan aka kwatanta da Agustan bara, sannan an samu ƙari da kashi 5.31 daga Agusta idan aka kwatanta da Yuli a ma’aunin wata wata
Tun janye tallafin man fetur, ake ci gaba da fuskantar tsadar kayan masarufi a Najeriya.
Rahoton hukumar NBS ya kuma ce tsadar sufuri ta yi tasiri ga tsadar kayan abincin.
Duk da wasu kayan abincin sun sauka yayin da aka fara samun amfanin gona amma kuma har yanzu wasu kayan abincin na ci gaba da tsada.
Wane yanki kayan abinci suka fi tsada?
Rahoton ya nuna cewa tashin farashin kayan abinci ya shafi kayan abinci irin su burodi da shinkafa da hatsi da dankalin turawa da doya da rogo.
Duk da cewa alkalumman hukuma sun sha bamban da zahirin farashin kayan abincin a kasuwa, amma rahoton hukumar hukumar ƙididdiga sun ce a ma'aunin watan Agustan 2024 ya nuna farashin kayayyakin sun bambanta tsakanin yankunan Najeriya.
Alkalumman sun nuna shinkafa ƴar gida da ake nomawa a ƙasar ta fi tsada a yankin kudu maso yammaci inda ake sayar da kilogram ɗaya kusan rabin mudu kan naira 1,960.87, yayin da shinkafar kuma ta fi sauƙi a yankin arewa maso yammaci inda ake sayar kilogram ɗaya kan naira 1,591.21.
Alƙalumman sun nuna cewa burodi ya fi tsada a yankin kudu maso kudu inda ake sayar da leda daya kan naira 1,785.56 wato gram 500. Sai dai farashin ya fi sauƙi na burodi a yankin arewa maso gabas inda ake sayar da ledar 500 gram kan naira 1,163.78.
A ɓangaren nama, yankin kudu maso yammaci ne ya fi tsada inda ake sayar da kilogram kan N6,135.87. kilon nama ya fi sauki a yankin arewa maso yammaci inda ake sayarwa kan N4,869.25
Hukumar ta ce ta tattara alƙalumman ne daga ƙananan hukumomi 774 na sassan jihohin Najeriya haɗi da Abuja.
Me ke haifar da tsadar kayan abincin?
Matsalar tsaro ta yi tasiri sosai ga haifar da tsadar kayan abinci a Najeriya musamman a yankin arewa maso yammaci da aka fi yin noma kuma inda matsalar tsaron ta fi yin ƙamari.
Sannan ana alaƙanta hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar naira a Najeriya, ƙasar da tattalin arzikinta ke dogaro da man fetur.
Janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi har yanzu yana ci gaba da yin tasiri ga tsadar kayayyaki, da kuma barin kasuwar kuɗin ƙasashen waje ta daidaita farashin.
Duk da masana sun yi hasashen za a iya samun sauƙi a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta amma kayan abinci sun fara cirawa sama.
Masana irinsu Dr Muhammad Shamsudden, malamin tattalin arziki a Jami’ar Bayero Kano, na ganin a zahiri hauhawar farashin kayayyakin ta zarta alƙalumman hukumomi.
A cewar masanin, duk lokacin da canjin kudi na kasashen waje ya sauya dole kayan da ake shigo da su daga waje farashinsu dole ya tashi, haka ma na gida saboda yadda buƙatarsu za ta ƙaru.
Dr Muhammad Shamsudden, ya ce wani daliin da ke sa farashin kaya ya rinka hawa shi ne kara kudaden haraji da ake yawan yi dama kirkiro sabbin haraji da kuma ƙarin kuɗin makamashi.
Amma masana na ganin sai gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa.