Me ya sa aka ƙi zaɓen ɗan Afirka a matsayin Fafaroma?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Lebo Diseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service global religion correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
A lokacin da al'ummar duniya suke cigaba da tattaunawa game da sabon fafaroma, wata babbar tambaya da ake yi ita ce shin me ya ba a za zaɓi ɗan Afirka ba?
Mutane da dama sun yi tunanin ko cocin ta Vatican za ta zaɓi fafaroma daga nahiyar Afirka, inda ake samun ƙaruwar mabiya ɗariƙar Katolika.
Akwai masu riƙe da muƙamin manyan malaman cocin aƙalla 3 daga nahiyar a baya, fafaroma na ƙarshe Pope Gelasius na ɗaya ya mutu sama da shekara 1,500 da suka gabata, wasu na ganin lokaci ya yi da za a kawo wani.
Fafaroma Francis ya so shugabancin ya yi la'akari da inda cocin ta kai a duniya. 18 daga cikin manyan limaman ɗarikar Katolika wato cardinalds 108 ɗin da ya naɗa daga Afrika suke.
Uku daga cikinsu za su iya gudanar da aikin fafaroma – Akwai Fridolin Ambongo Besungu daga Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da Robert Sarah daga ƙasar Guinea da kuma Peter Turkson daga Ghana. A shekara ta 2013 an duba yiwuwar naɗa Cardinal Turkson amma aka zaɓi fafaroma Francis.

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da aka zaɓi Robert Francis Prevost wanda aka haifa a Amurka, kuma ya ɗauki sunan fafaroma Leo 14. mabiya ɗarikar Katolika a faɗin duniya sun yi farin ciki kodayake wasu na ganin an yi watsi da Afrika.
Majalisar manyan limaman coci wato Cardinalds na zaɓen fafaroma cikin sirri, wannan ce ta sa zai yi wahala a samu ɓillar bututuwan da aka tattauna. Amma akwai yiwuwar a samu wata tambaya ɗaya a zukatan manyan limaman 133, in ji Father Lawrence Njoroge marubucin ɗarikar Katolika kuma farfesa a jami'ar Jomo Kenyatta.
"Za mu zaɓi fafaroman da zai ci gaba da ayyukan da Fafaroma Francis ya bai wa muhimmanci, ko za mu samo wanda zai gabatar da sabbin manufofi?." Ina ganin an samu rabuwar kai anan.
Fafaroma Francis ya kasance mai kawo sauyi - duk da cewar bai sauya tsarin coci ba amma ya kawo sauki a al'amura kamar sakin aure inda ya ba Manyan malamai watau Bishops damar ɗaukar mataki daga ƙasa.
A ƙarshe dai Fr Njoroge ya ce duk da cewar akwai ''Manyan limamai watau cardinals daga Afrika waɗanda kuma suka cancanci zama fafaroma, babbar tambayar ita ce tarihin da fafaroma Francis ya bari".
Akwai yiwuwar samun wasu dalilan da suka taka rawa. Tilas fafaroma ya jagoranci coci a duniya tare da buƙatun kowacce nahiya a duniyar.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Afrika na ƙoƙarin farfaɗowa daga tasirin Turawan mulkin mallaka, a cewar Fr Joseph Nyamunga, shugaban cibiyar ɗarikar Katolika ta St Anne a Nairobi. Nahiyar ba ta gama wartsakewa ba".
"Muna fama da yaƙi ko'ina, a Congo da kuma Sudan.
"Kana buƙatar mai natsuwa lokacin jagorancin babbar Coci. A matsayin fafaroma ba a buƙatar wani abu da zai ɗauke maka hankali daga aiki."
Father Nyamunga ya ja hankalin cocin Katolika a Afrika da su ƙara jajircewa wajen aikin al'umma.
"Tambayar ita ce, me Afrika ke buƙata yanzu? samun matsayin fafaroma ko kuwa nemar wa al'ummar mu mafita?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tabbas, ba a iya nahiyar Afrika ake rikici ba kawai, da irin rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya da kuma Turai. Sabon fafaroma zai tafiyar da cocinsa tare da fuskantar al'amuran da suka shafi shugabanni masu kama-karya da matsalolin kudi.
Dole ne ya iya magance bukatun mabiya a Kudancin Duniya, inda Cocin Katolika ke ƙara samun karɓuwa. Kuma ana sa rai zai taimaka wajen bunƙasa Cocin a Turai - inda fadar Vatican ta ce ɗarikar ba ta yi ƙarfi sosai ba.
Fr Njoroge ya ce manyan limaman cocin na neman ɗan takarar da zai yi wa Cocin duniya hidima yadda ya kamata ba tare da ''la'akari da asalinsa ko ƙabilarsa ba".
Ana kallon fafaroma Leo na 14 a matsayin mai saurare kuma wanda zai ba dukkan ɓangarorin coci dama.
Bugu da ƙari ya na da tasiri a Arewaci da Kudancin duniya.
Fr Njorge ya nuna cewar duk da an haife shi a Amurka, fafaroma Leo na 14 ya shafe shekaru da dama ya na hidimtawa addini a Peru.
"Ya ziyarci duk ƙasashe 50 ɗin da ke ƙarƙashin kulawarsa a Addinance watau Augustinian Order works. A watan Disamban bara ya ziyarci birnin Nairobi inda ya ƙaddamar da ayyukan yaɗa manufofin addinin Kirista a ƙasashen Afrikan da ya ke yiwa aiki."
Kodayake ba ɗan Afrika ba ne, amma ana kallon fafaroma Leo na 14 a matsayin wanda ke da ruwa da tsaki da buƙatun mabiya daga Afrika.











