Ko Trump ya cika alƙawuran da ya ɗauka zai aiwatar a kwanakin farkon mulkinsa?

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 5

Donald Trump ya yi alƙawura da dama a lokacin da yake gudanar da yaƙin neman zaɓen zama shugaban ƙasar. Ya yi alƙawarin rage haraji da rage farashin kayayyaki, da hana kwarorowar baƙin haure ba bisa ƙa'ida ba, da kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da ƙarfafa masana'antun Amurka.

Wasu daga cikin tsare-tsaren tawagarsa ce ta feɗe su dalla-dalla wasu kuma Trump ne da kansa ya gabatar da su, a cikin bidiyo na "Agenda 47" wanda ya wallafa a shafin intanet na yaƙin neman zaɓensa. Wasu kuma an bayyana su ne kamar kara zube cikin irin salon da aka san trump da shi na furta duk wani abin da ya ke tunani ba tare da ya tauna ba da kuma salonsa na ɗaukar shawarwarin wadanda ke kusa da shi.

A cikin jawabinsa na nasara a ranar 6 ga Nuwamba, ya bayyana a fili cewa yana da niyyar cika alƙawuran da suka yi sandiyyar komawarsa fadar White House: "Zan yi mulki da wani take mai sauƙi: alƙawuran da aka yi, su ne alkawuran da za'a cika."

Hakan dai ya zama tamkar taken gwamnatinsa a cikin watansa na farko, wanda a ciki aka yi fama da hada-hada da kuma gagarumin ci gaba wajen cimma wasu manufofinsa.

A fannoni irin su shige da fice da manufofin ƙasashen ƙetare, Trump yana da iko cikakkaen ikon yanke hukunci ba tare da wata tuntuɓa ba - kuma ya yi hakan. A wasu ɓangarorin kuma, ya fuskanci ƙalubalen shari'a da cikas na siyasa. Wasu daga cikin yawancin alƙawuran da ya ɗauka za su buƙaci a amincewar Majalisa, inda jam'iyyar Republican ke da rinjaye.

Anan ga wasu manyan alƙawuran "ranar farko" da Trump ya ɗauka da kuma ƙoƙarin da ya yi na tabbatar da su.

Rage farashin kayayyaki

Abin da ya ce:

"Ina cin zaɓe, nan da nan zan rage farashin kayayyaki, farawa daga ranar farko." Agusta 2024

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abin da ya yi:

Wannan wataƙila shi ne babban ƙalubalensa da kuma babban alƙawarin yaƙin neman zaɓe da ya rage bai cika. A cikin jawabinsa na farko, Trump ya yi alƙawarin "tattaro ikon " majalisar ministocinsa don rage farashi cikin gaggawa, amma ba a san wace hanya zai bi ya yi hakan ba. Wata hanya, in ji shi, ita ce ta hanyar haɓaka hakowa don rage farashin makamashi.

Tashin farashin da aka samu a watan Janairu, shi ne mafi girma a kowane wata cikin watanni 16 da suka gabata, ya kawo wa Tump cikas a cikin tsarinsa. Ya zargi Joe Biden, wanda ya bar ofis a ranar 20 ga Janairu, da kuma abin da ya kira kashe kashen jam'iyyar Democrats. "Ba ni da hannu ciki wannan lamari," in ji Trump.

A wasu lokuta, duk da haka, ya yarda cewa yana da wuya shugabannin Amurka su iya yin tasiri kan farashin kayayyaki. Sai dai masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa wasu daga cikin manufofinsa za su iya haifar da hauhawar farashin kayayyaki kuma ƙuri'un jin ra'ayin jama'a na nuna cewa masu kaɗa ƙuri'a na son ganin ya ƙara ƙaimi wurin yin wani abu kan batun da galibi ke ci musu tuwa a ƙwarya.

Tasa ƙeyar baƙin haure

Abin da ya ce:

"A rana ta farko, zan ƙaddamar da shirin korar baƙin haure mafi girma a tarihin Amurka domin sallamar masu aikata laifuka." Nuwamba 2024.

Abin da ya yi

Shige da fice ya kasance babban abin da Trump ya fi mayar da hankali a kai tun bayan hawansa mulki, tare da ba da umarnin zartarwa fiye da guda 12 da nufin yin garambawul ga tsarin. Da alama shirinsa na korar ƴan ƙasashen waje da ke zaune a ƙasar ba bisa ka'ida ba, inda zai soam daga waɗanda aka samu da aikata laifuka, kuma da alama yana samun goyon bayan jama'a.

Sai dai babu tabbas ko zai cika alƙawarinsa na korar ƴan ƙasashen waje da dama. An kai wasu hare-hare amma adadin mutanen da ake kora ba su taka kara sun karya ba kamar yadda alƙalumman yau da kullun suka nuna.

A cikin watan farko da ya hau kan karagar mulki, Amurka ta kori mutane 37,660 - kasa da matsakaitan korar mutane 57,000 na kowane wata a cikin cikar shekarar da ta gabata ta gwamnatin Joe Biden, in ji bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu.

Wani mai magana da yawun hukumar tsaro ta DHS ya shaidawa kamfanin cewa yawan korar da Biden ya yi, ya fi yawa saboda shige da fice ba bisa ka'ida ba ya fi yawa a wannan lokacin. Artabun da ake yi a lan iyakokin ƙasar sun ragu da kashi 66% a watan Janairu idan aka kwatanta da 2024, a cewar fadar White House.

Yafewa ƴan shida ga watan Janairu

Abin da ya ce:

"Zan duba batun J6 da wuri, wataƙila cikin minti tara na farko." Dec 2024

Abin da ya yi:

Kamar yadda ya faɗa, sa'o'i kaɗan bayan an rantsar da shugaban ƙasar, Trump ya yi afuwa da rangwame wanda ya share fagen sakin mutane sama da 1,500 da aka samu da laifi ko kuma aka tuhume su da hannu a rikicin da ya ɓarke a ginin majalisar dokokin Amurka. Wani ɗan sandan da aka cusawa naushi a ranar ya shaida wa BBC cewa afuwar da aka yi tamkar cin fuska ce gare su.

Kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Abin da ya ce:

"Suna mutuwa, ƴan Rasha da Ukraine. Ina so su daina mutuwa. Kuma zan tabbatar da hakan - zan yi hakan a cikin sa'o'i 24." Mayu 2023.

Abin da ya yi:

Trump dai ya fara tattaunawa ta farko tsakanin Amurka da Rasha tun bayan fara yaƙin, amma Ukraine ta sha alwashin yin watsi da duk wata yarjejeniya da aka ƙulla ba tare da ita ba, kuma an yi ta musayar kalamai tsakanin shugabannin. Shugaba Volodymyr Zelensky na fargabar shugaban na Amurka ya cika alkawarinsa na kawo ƙarshen yaƙin amma bisa sharuɗɗan Moscow ba tare da wani tabbacin tsaron ƙasarsa ba. Har ila yau akwai fargaba a manyan biranen Turai na cewa an mayar da su gefe guda, kuma wataƙila Trump ya wargaza wasu takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha a matsayin ladabtarwa kan mamayar da ta yi.

Kawo ƙarshen haƙƙin zama ƴan ƙasa kan waɗanda aka haifa a ƙasar

Abin da ya ce:

Trump ya shaida wa NBC a watan Disamba cewa "da gaske" yana shirin kawo ƙarshen zama ɗan ƙasa a rana ta farko: "Idan wani ya sanya ƙafa ɗaya kawai… a ƙasarmu, sai a taya shi murna. Yanzu kai ɗan ƙasar Amurka ne. Eh, za mu kawo ƙarshen hakan."

Abin da ya yi:

A ɗaya daga cikin ayyukan farko na shugabancinsa na biyu, Trump ya ba da umarnin kawo ƙarshen wani haƙƙi na kai tsaye da ke bayar da daman zama ɗan ƙasar Amurka ga kusan duk wanda aka haifa a ƙasar. Zama ɗan kƙasa bayan haihuwa ba al'ada ce a duniya ba, ko da yake haka ya ke a Mexico da Canada, kuma matakin na Trump ya shafi waɗanda ke Amurka ba bisa ƙa'ida ba ko kuma masu biza na wucin gadi.

An kafa wannan dama ta hanyar gyara ga Kundin Tsarin Mulkin Amurka kusan shekaru 160 da suka gabata, kuma yawancin malaman shari'a sun ce shugaban ba shi da ikon canza shi ba tare da izini ba. Batun na iya zuwa kotun kolin Amurka bayan da wata kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan Trump, inda ta tabbatar da kawo cikas a shirin na sa.

Ƙaƙaba haraji kan Canada da Mexico

Abin da ya ce:

"A ranar 20 ga Janairu, ɗaya daga cikin dokokin zataswa na farko, zan sanya hannu kan duk takardun da suka wajaba don ɗaurawa Mexico da Canada harajin kashi 25% akan duk kayayykin da su ke shigoa da su Amurka, ta buɗaɗɗun iyakokinta." Nuwamba 2024

Abin da ya yi:

Trump ya bayar da sanarwar a ranar 21 ga Janairu cewa zai sanya harajin bai-ɗaya kan makwabtansa a ranar 1 ga Fabrairu, tare da danganta su da kwararar miyagun ƙwayoyi da baƙin haure zuwa Amurka. Shugaban ya daɗe yana ganin haraji kan kayayakin da ake shigowa da su , a matsayin wata hanya ta kare masana'antun cikin gida da kuma haɓaka kuɗaɗen shiga. Ƙasashen Canada da Mexico sun ce za su sanya harajin ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke shigowa da su. Sai dai Trump ya jinkirta fara harajin na tsawon wata guda, bayan alƙawurran da ƙasashen biyu suka yi na ƙara tabbatar da tsaro a kan iyakokin ƙasar. Haka kuma an yi ta samun sauye-sauye a kasuwanni inda masana tattalin arziki ke gargaɗn cewa waɗannan matakai na iya haddasa tashin farashin kayayyaki.