Yadda NDLEA ta bankaɗo gidajen haɗa 'muguwar ƙwaya' a Lagos da Anambra

Muguwar ƙwaya

Asalin hoton, Australian Federal Police

Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta gano manyan ɗakunan haɗa kwayar 'Mkpuru Mmiri' a kudancin ƙasar.

Hukumar ta ce ta gano wuraren haɗa kwayar ce a jihohin Legas da kuma Anambra, inda suke sarrafa sinadarin crystal methamphetamine mai matuƙar haɗari da ake rarrabawa zuwa sassan Najeriya.

"Bayan afkuwar annobar crystal methamphetamine a wata ukun farko na 2021, musamman a kudu maso gabas, hukumar ta baza dukkan ƙarfinta don gano ainahin tushen da ake samar da ita a Najeriya da masu yinta," a cewar shugaban NDLEA Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ranar Talata.

A shekararar da ta gabata ne mazauna yankin kudu maso gabas suka ƙaddamar da yaƙi da Mkpuru Mmiri.

Lokaci guda wani kwamati da mutane gari suka kafa ya fara kai samame sansanoni a ƙauyuka da zimmar kama masu ta'ammali da ita.

Wasu bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda aka dinga yi wa mutanen da ake zargi da ta'ammali da ƙwayar bulala a bainar jama'a.

Buba Marwa ya ce yunƙurinsu na yaƙi da ƙwayar ya sa sun kama ƙasurguman mutanen da ke safararta cikin wata bakwai da suka wuce. Sun sake kama wasu mutum biyu a kwanan nan.

"Shakka babu wannan wani saƙo ne babba ga masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi cewa ko dai su tuba ko kuma su rasa dukkan abin da suka tara na dukiya da kuma 'yancinsu da suke da samu a wannan haramtacciyar harka," in ji shi.

Yadda muka bankaɗo wajen haɗa ƙwayar Mkpuru Mmiri (crystal methamphetamine) - NDLEA

Shugaban na NDLEA ya ce bayan tsawon watanni na tattara bayanan sirri da bin sawu, haƙarsu ta cimma ruwa a ranar Asabar, 30 ga watan Yulin 2022.

"Na farko, mun kama shi ne a Victoria Garden City da ke Lekki a Legas, kuma Chris Emeka Nzewi ne ya kama shi," a cewarsa.

"Shi kuma na biyun a Nise na Ƙaramar Hukumar Awka ta Kudu a Jihar Anambra yake, kuma Paul Ozoemenam ne ya kama shi."

NDLEA ta ce a lokacin ne suka kama masu gidajen haɗa ƙwayar da kuma Sunday Ukah, wani masanin magani ɗan Anambra da ke sarrafa musu ƙwayar.

Su ne suka haɗa masana'antar a Legas a kewayen yara da ke wani gida mai ɗaki huɗu a Legas.

"A nan muka gano kwayar crystal methamphetamine mai nauyin kilogiram 258.74 da sauran sinadarai da suke amfani da su wajen haɗa ƙwayoyin.

"Mun tarar da kayayyakin haɗa magunguna kamar tukunyar gas da takunkumai da safunan hannu da mazauban ajiya da sauransu."

'Dalilin da ya sa Nzewi ya saka rayuwar iyalinsa cikin haɗari'

Buba Marwa ya ce abu ne mai ban mamaki ganin yadda mutumin yake haɗa ƙwayoyin masu rikitarwa a gidan da yake zaune a ciki tare da iyalinsa a Legas.

"A lissafi na tsakatsaki, ɗakin gwajin na samar da kilo 50 na ƙwayar methamphetamine duk sati, inda suke shirin ƙara yawanta zuwa kilogiram 100 a sati.

"Ina ake kai duka waɗannan ƙwayoyi? Daga bincikenmu na farko, mun gano cewa ɗakin na samar da ƙwayoyin ne don amfanin cikin gida da kuma fitarwa ƙasashen waje.

"Idan kuka duba yadda farashin wannan ƙwaya ke tashi sosai har zuwa dala 500 kan kowane kilo a kasuwa, za ku fuskanci dalilin da ya sa Nzewi bai damu ya saka rayuwar iyalinsa cikin haɗari ba.

"Sabaoda haka, bankaɗo waɗannan ɗakunan babbar nasara ce wajen daƙile wannan matsalar."

Mece ce ƙwayar Mkpuru Mmiri (crystal methamphetamine)?

Ƙwayar crystal methamphetamine wadda ake kira Mkpuru Mmiri, wani haɗin sinadari ne da ake kwaikwayar ƙwayoyin magani masu inganci, a cewar cibiyar nazarin tasirantuwa da ƙwayoyi ta Tarayyar Turai (EMCDDA).

An fara ƙera ta ne a Japan a shekarun 1919.

Ba kasafai ake amfani da methamphetamine ba saboda akasari ba a samar da ita a fili, musamman a Amurka da kuma kudancin duniya.

Ƙasashen duniya na sa ido a kanta sosai kuma tana kama da ƙwayar amphetamine.

Shafin WebMD ya ce crystal methamphetamine game-garin suna ne da ake faɗa wa ƙwayar mai ƙarfin gaske wadda kuma take saurin kama mutum.

Yadda za a gane mai shan ƙwayar crystal methamphetamine

Shafin WebMD ya lissafa alamomin da ake iya gane masu shan ƙwayar crystal methamphetamine kamar haka:

  • Mutum ba zai dinga damuwa da yadda mutane ke kallonsa ba
  • Zai dinga yawan soshe-soshen kansa ko jikinsa
  • Ba zai dinga jin yunwa ba kuma zai rame
  • Girman ƙwayar idanu da kuma yawan motsawarsu
  • Yin barci a kowane lokaci na rana - ko kuma shafe kwanaki ba tare da barcin ba
  • Yawan cin bashi, da sayar da kayayyaki, ko sata
  • Yawan hayaniya
  • Mutum zai dinga gane-gane ko jiye-jiyen abubuwa haka kawai