Abu bakwai game da yaƙin da NDLEA ke yi da shaye-shaye a Najeriya

Asalin hoton, BBC
Najeriya na daga ƙasashen duniya da suka yi ƙaurin-suna wajen sha da safarar miyagun ƙwayoyi, abin da ya sa gwamnatin ƙasar ɗaukar matakai daban-daban ciki har da kafa hukumar NDLEA.
Babban aikin hukumar ta National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) shi ne yaƙi da sha da fataucin haramtattun ƙwayoyi, wanda zuwa yanzu ta ce ta samu nasararori da dama.
Domin jin irin yadda take yaƙin da kuma nasarorin da take iƙirarin samu, Sashen Hausa na BBC ya tattauna da shugaban hukumar, Janar Buba Marwa (mai ritaya) a cikin shirin A Faɗa A Cika.
Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Buba Marwa shugabancin NDLEA a watan Janairun 2021.
Ga wasu muhimman abubuwa bakwai da muka ji daga bakin tsohon janar ɗin.
'Mutum ɗaya cikin bakwai na 'yan Najeriya na shaye-shaye'
Da yake magana kafin fara shirin, tsohon sojan ya bayyana girman matsalar shaye-shayen ƙwayoyi a Najeriya da cewa "babbar matsala" ce.
"Mu a Najeriya muna da matsala babba, saboda cikin mutum bakwai ɗaya yana shaye-shaye," in ji Janar Buba Marwa.
Sai dai ya ce wannan lissafin na Majalisar Ɗinkin Duniya ne da ta yi kusan shekara uku ko huɗu da suka wuce.
'Duk wanda kotu ta ɗaure shi ba zai tarar da komai ba na dukiyarsa'
Wata mai sauraro ta yi ƙorafin cewa wasu da aka ɗaure kan fito da ƙarfinsu fiye da da bayan sun gama zaman gidan-yari.
"Maganar cewa wasu su shiga [gidan-yari] ya fito kuma su tarar da dukiyarsu babu ita yanzu," in ji Janar Marwa. "Mu kaɗai ne doka ta ba mu dama mu shiga gidan duk wanda muke zargi mu kwace shi idan har muna zargin da kudin ƙwaya ya gina shi."
'Mun kama kayan maye kilo miliyan uku da rabi'
Janar Marwa ya bayyana cewa daga cikin aikin hukumarsu akwai hana samun haramtacciyar ƙwayar da za a yi amfani da ita.
"Tun da muka zo wannan aikin kusan shekara ɗaya da rabi mun kama ƙwayoyi [masu nauyin] fiye da kilo miliyan ɗaya da rabi," a cewar tsohon janar ɗin.
Idan aka lissafa kuɗinsu kuma, darajar ƙwayoyin ta kai naira biliyan 130.
'Mun kama mutum 15,000'
Tun bayan da Buba Marwa ya kama aiki a NDLEA, hukumar ta kama mutum 15,000 da ake zargi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, a cewarsa.
Ya ƙara da cewa 2,000 daga cikinsu suna kurkuku yanzu haka, yayin da 8,000 ke tsare a gidajen-yari.
'Mun kama manyan dillalan ƙwaya bakwai'
NDLEA ta ce cikin nasarorin da ta samu a 'yan kwanakin nan shi ne kama manyan dillalan ƙwaya bakwai.
'Akai wanda ake nema tun shekara 10 da suka wuce, amma mun kama shi," a cewar Janar Marwa.
"Akwai wani da muka kama mako biyu da suka wuce da ya shigo da ƙwayar tramadol a 2019, cikin wata ɗaya ya shigo da tramadol ta naira biliyan 22."
'Mun taɓa kama mutum mai asusun banki 103'
Shugaban NDLEA ya ce 'yan makonnin da suka gabata sun kama wani babban dillalin ƙwaya da ke da asusun banki 103.
"Duk sai da muka rufe su kuma muna ci gaba da bincika sauran ma'aikatu da harkokinsa."
Ɓangaren shari'a na ba mu matsala - Buba Marwa
Wata tambaya da wani mai sauraro ya yi wa Buba Marwa ita ce cewa ana yawan sakin waɗanda aka kama da zargin mu'amala da miyagun ƙwayoyi.
Cikin amsar da ya bayar, Marwa ya ce ya san da matsalar har ma ya kai wa alƙalin kotun tarayya ziyara game da hukuncin da ake yi wa masu safarar ƙwayar.
"Akwai wani da aka taɓa yanke masa hukuncin biyan tarar 3,000, wani kuma 4,000.
"Abin da muke yi yanzu shi ne muna yunƙurin cire zaɓin biyan tara daga cikin dokar da ta kafa mu, kuma yanzu haka ana yi wa dokar kwaskwarima a Majalisa."











