NDLEA ta cafke hodar ibilis da darajarta ta zarce naira biliyan hudu

Jamian hukumar NDLEA
Bayanan hoto, Jamian hukumar NDLEA

Hukumar da ke yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta cafke wasu masu safarar hodar ibilis mai nauyin kilogram 17 da darajarta ta zarce naira biliyan 4.

Ta ce nasarar da ta samu ta biyo bayan sumamen da ta kai a wasu sasan kasar a baya bayanan inda ta kama mutum 10 wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Kakakin hukumar Femi Babafemi ya ce jami'ai sun yi kamen ne a babbar tashar jiragen ruwa ta Apapa da kuma filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

"Ana bincike kan wasu mutane hudu yanzu haka a kan hodar ibilis mai nauyin kilogram 13.65 da aka kwace a cikin wani jirgin ruwa, da ake kira MV Karteria da ya shigo tashar jirgin ruwa ta Apapa daga birnin Santos na kasar Brazil a ranar 7 ga watan Nuwamba, bayan makoni uku da cafke hodar ibilis mai nauyin kilogram 32.9 da aka gano a cikin wani jirgin ruwa da shi ma ya fito daga birnin Santos na Brazil''. In ji shi

Femi Babafemi ya kuma kara da cewa:" An cafke wasu mutane biyar a sassa daban- daban na Legas da Delta wadanda ake zargin suna da hannu a safarar hodar ibilis mai nauyin kilogram 3.200 da aka samu a hannu wani fasinja da ya shigo cikin kasar ranar 5 ga watan Nuwamba''.

Hukumar ta ce jami'anta sun kuma kama wani mutum da ake kira Ude Onyeka a ungwar Mafoluku da ke Oshodi a jihar Lagos.

''Ude Onyeka ya ce yayansa Ikenna Ude da ke zama a kasar Afrika ta Kudu ne ya umarce shi da ya karbi jakar da ke dauke miyagun kwayoyin, ya mika wa wani mutum da zai zo daga jihar Delta",in ji Babafemi.

A samame na biyu da jami'an suka kai sun kama wani mutum da ake kira Abanjo Innocent wanda ya je Lagos daga jihar Delta domin ya karbi jakar a rana 6 ga watan Nuwamba.

Shima Innocent ya bayyana cewa wani Oseki Chinedu wanda yake zaune a kasar Afrika ta Kudu ne ya umarce shi ya yi tafiya zuwa Lagos domin ya karbi jakar.

Hukumar ta kuma ce a ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba jami'anta suka kama Obeluo Emeka daga jihar Anambra tare da hodar ibilis ta Heroine mai nauyin kilogram 600.

Mutumin da ake zargi wanda dillalin kayan gyaran motoci ne a garin Doula na kasar Kamaru ya isa Yenagoa ta jirgin ruwa domin ya miƙa ƙwayar a wani gida da ke Lagos.

Haka kuma an kama mutum 4 tare da hodar ibilis da tabar wiwi da tramadol da kuma Methamphetamine a hannunsu a samamen da suka kai a wasu yankuna na jihar Ribas.

Jami'an hukumar sun kuma kwace miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 18.5 a samamen da suka kai wa wasu ungwani a jihar Bauchi inda suka cafke mutun biyu.