Yanayi na aƙuba da ake jefa yaran da ake harbi a Amurka

A daidai lokacin da ake samun yawaitar matasa da ake harba da bindiga a Amurka, asibitocin yara da ke babban birin ƙasar na ƙoƙarin karya lagon irin waɗannan munanan ayyuka.
A wani ɗakin bayar da agajin gaggawa na wata Asibitin Yara da ke birnin Washington DC, gadajen asibitin sun cunkushe wani kwararo yayinda akwatunan talabijin da ke harabar ke famar gabatar da shiraruwan wasan yara.
A wannan ɗakin ne ake kai yaran da suka samu munanan raunuka. Kamar waɗanda haɗurran mota ya rutsada su, amma a 'yan shekarun baya-bayan nan, ana yawan samun karin yaran da ake kai wa bisa dalilan harbin bindiga.
Dakta Mikael Petrosyan wani likitan fiɗa ne wanda galibi ya kan yi wa yara da ba su wuce shekara uku ba aiki, ya ce wannan lamari na faruwa kusan a kullum.
"Lamari ne mai tashin hankali, saboda ban san dalilin hakan ba, abu ne da zai daure maka kai' in ji shi.
A wannan zamani bindiga ce makamin da aka fi amfani da shi wajen hallaka mutanen da ke kasa da shekara 17, inda har ta zarce mace-macen da ake samu sanadiyyar haɗarin mota. Wani bincike da wata mujallar kiyon lafiya mai suna JAMA Network Open ta wallafa ya ce cikin shekara goma ƙaruwar bindigogi a hannuwan jama' ya riɓanya, amma lamarin ya fi muni tun bayan ɓullar annobar korona.
Cibiyar Pew Research ta fitar da wasu alƙalumma da ke nuna cewa cewa tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021 an samu ƙaruwar mutuwar yara 'yan ƙasa da shekara 18 a Amurka da kusan kashi 50 cikin ɗari.
Matasa na neman taimako domin su samu 'yanci wanda ya yuwu karatu ne ko samun sabbin abokan rayuwa ko kuma aikin yi, wanda hakan zai taimaka wajen karya lagon ayyukan ta'addanci.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Mikael Petrosyan, likitan gaggawa na Asibitin Yara ta Ƙasa ya ta'allaƙa illar da bindiga ke yi a matsayin wata cuta da a ganinsa ta zama tamkar annoba da ta yaɗu a sassan birnin Washington.
Wata uwa ta shaida wa BBC cewa, "akwai iyaye da dama da ke shaida muna cewa "babu yarona da ba a harba ba, ko yanzu haka ina da harsashi a jikina, ta ce an kashe mahaifinsa kan hanya ɗaya inda shi ma aka taɓa harbinsa sa".
A bara ma, ta ƙaddamar da wani shirin da kan taimakawa matasa kaucewa shiga aikata muggan laifuka. A maimakon ci gaba da kula da masu raunukan harbin bindiga kawai, shirin kan yi amfani da wannan lokaci maras daɗi wajen wayar da kan matasan domin canza musu tunani da alkibla a rayuwa.
Yvonne Doerre, wata mai yi wa a'lumma hidima ce da ta kwashe shekara 30 a Gundumar ta Columbia, ta ce akwai dalilai da yawa da su ke sa matasa na ɗaukar bindiga. Bindiga na da sauƙin sarrafawa amma kuma akwai tasirin da annobar korona ta bari ita ma a ƙwalƙwarsu.
"Idan muka waiwayi baya lokacin da ake fama da annobar korona, waɗannan yaran ba su fi shekara 10 zuwa 12 ba, wanda lokaci ne na tashin hankali kuma maras tabbas ga mutane", in ji ta.
Haka ma rashin tartibin tsarin halartar makaranta ya sa akasarin yara suka daina ɗaukar darasi ta kafar bidiyo wanda hakan ya haddasa suka kasa zuwa makarantar sakandire a loakcin.
Samun damar tura yara makaranta na cikin muhimman nasarorin shirin, amma ba zuwan su ne makarata ne kawai abinda za a mayarwa hankali kaɗai ba. Akwai kuma buƙatar sa yara su kaucewa wuraren da ake samun fitintinu domin kare su daga cutarwa.

Hasalima dai tawagar ta lura da abubuwan da ke faruwa a zahiri. Ɗaya daga cikin matasan da za su shiga shirin an taɓa harbinsa da bindiga lokacin da ya ke ɗan shekra 13 da haihuwa. Ya shiga ƙungiyar ne bayan an harbe shi karo na biyu, kuma tawagar ta tuntuɓi iyayensa domin jin yadda za a iya shi taimako. Bayan 'yan watanni aka harbe shi karo na uku abinda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
A wani taron kungiyar da ta kan gudanar a duk tsakiyar mako, ta tattauna da wani matashi da ya samu nasarar komawa kan aikinsa bayan wata shawara da suka ba shi. A wurin Dakta Donnely wannan wani matakin nasara ne.
Dakta Donnelly ta tambaya cewa "yara nawa na taimaka na mayar da su makaranta? Yara nawa na samarwa horo har suka yi farin ciki, inda ma suka nuna muna katinsu na cirar kuɗi alamun nasara a rayuwa?."
Jewanna Hardy, wadda ke jagorantar wani shiri da ake kira Guns Down Friday kuma ta ke aiki da wannan tawaga, ta bayyana amincewar ta da wannan magana.
"Kafin soma wannan shiri da zarar an harbi yaro aka yi masa magani, shikenan sai ya koma gida haka", in ji ta.
"Amma yanzu muna ƙoƙarin ganin mun sauya rayuwar waɗannan matasa, da kuma yadda zamu sauya rayuwar iyalansu da ma al'umma baki ɗaya."











