Getafe na fatan mallakar Greenwood daga Man United

Shugaban kungiyar Getafe, Angel Torres ya ce suna fatan mallakar dan kwallon Manchester United, Mason Greenwood, wanda ke yi musu wasannin aro.

Tsakanin Getafe da United ba wadda take da tabbacin ko ɗan kwallon mai shekara 22 zai koma Old Trafford da taka leda a badi.

''Makomar ɗan kwallon tana ga Greenwood da kungiyarsa, ina jin zai ci gaba da buga wasannin aro zuwa kaka daya,'' kamar yadda Torres ya sanar da Radio Marca.

Greenwood ya ci kwallo 10 a wasa 32 a dukkan karawar da ya yi wa Getafe a bana, wadda take ta 10 a teburin La Liga.

Ya koma Sifaniya da buga wasannin aro cikin Satumba, bayan wani bincike da United ta gudanar kan zargin fyade da aka yi masa daga baya aka soke batun a kotu.

A lokacin aka yanke shawarar Greenwood da ya fita wajen Ingila ya taka leda, har ake cewa ya gama buga wasa a Old Trafford.

Sir Jim Ratclipp ya sanar cewar a cikin watan Fabrairu cewar har yanzu ba su yanke shawara ba kan makomar Greenwood a United.