'Yan matan Sifaniya sun lashe Kofin Duniya

Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Sifaniya ta lashe gasar Kofin Duniya bayan doke Ingila a wasan ƙarshe na gasar ta 2023 da aka buga a Ausraliya.

Carmona ce ta ci ƙwallo ɗaya tilo a minti na 29 bayan ta ɗaɗa ta daga ɓangaren hagu da ƙafarta ta hagu.

Wannan ne karon farko da Sifaniya ta lashe gasar.

Kafin wannan gasar, wasa ɗaya kacal ta taɓa ci a Kofin Duniya.

Yanzu ta zama ƙasa ta biyar da ta ci kofin bayan Amurka (4), da Jamus (2), da Norway (1), da kuma Japan (1).

Rashin nasarar da Ingila ta yi a wannan wasa, shi ne karo na farko cikin wasa 29 da ta buga a dukkan gasa.

Rabon da a ci tawagar tun watan Maris na 2020 a wasa tsakaninta da Sifaniya - ita ɗin dai - a gasar SheBeleives. Ta yi nasara cikin wasa 25, ta yi canjaras 4.